Man United ta fi cin Arsenal a tarihin karawa

An wallafa

Manchester United za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na 15 a gasar cin kofin Premier a ranar Laraba a Old Trafford.

Wannan karawa ce ta 53 a tsakaninsu inda United ta ci 24, Arsenal ta yi nasara a 13 da canjaras 15.

A ranar Asabar United ta buga 2-2 a gidan Southampton, ita kuwa Arsenal doke Tottenham 4-2 ta yi a ranar Lahadi a Emirates a wasan hamayya kuma karawa 19 a jere ba a doke ta ba.

Cikin wasa 19 da Arsenal din ta yi a jere ba a yi nasara a kanta ba har da 12 a gasar Premier da biyu a Caraboa da biyar a Europa League.

Ita kuwa United ta yi rashin nasara a hannun makwabciyarta Manchester City, sannan ta tashi babu ci da Crystal Palace da kuma 2-2 da ta yi a Southampton.

Arsenal tana ta hudu a kan teburin Premier da maki 30, ita kuwa Manchester United tana ta bakwai da maki 22.