Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kamaru ta tsallake zuwa gasar cin kofi duniya ta mata
Kungiyar kwallon kafar mata ta kamaru Indomitable Lionesses ta samu damar zuwa ga gasar cin kofin duniya ta Mata bayan ta samu nasara akan mali da ci 4-2 a wasan neman na uku a gasar cin kofin kwallon kafa na matan Afrika da ake gudanarwa a Ghana.
Wannan shi ne karo na biyu da Kamaru za ta buga gasar cin kofin kwallon kafar mata na duniya, wanda za a yi Faransa a 2019, bayan ta samu mataki na uku a gasar cin kofin Afrika.
Kamaru ta bi sahun Afrika ta kudu da Najeriya wadanda za su kece raini a ranar Asabar a wasan karshe na gasar cin kofin Afrika na mata da za a kammala a Ghana.
Wannan shi ne karo na biyu da kungiyoyin za su kara a wannan a gasar, inda a zagayen farko wasannin rukuni, Afrika ta kudu ta ci Najeriya ci 1-0.
Masu sharhi na ganin Najeriya za ta fito da neman ramuwar gayya ne, sai dai ita ma Afrika ta kudu za ta dage, lamarin da ake ganin wasa ne da ba a san maci tuwo ba.