Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wayne Rooney ne zai yi wa Ingila kyaftin a wasansa na karshe
Tsohon dan wasan Manchester United Wayne Rooney ne zai yi wa Ingila kyaftin kuma zai sanya riga mai lamba 10 a wasansa na karshe.
Rooney mai shekara 33, ya yi ritaya daga yi wa kasarsa wasa ne a shekarar 2017, sai dai zai kara taka wa kasarsa leda a wasan da za ta yi da kasar Amurka a filin wasa na Wembley ranar Alhamis.
Fabian Delph ne zai fara jagorantar kungiyar Ingila a matsayin kyaftin, kafin Rooney ya karbe shi bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Rooney, wanda yanzu yake wasa a kungiyar DC United da ke Amurka, ya yi ritaya ne bayan ya yi wa kasarsa wasanni 199, inda ya zura kwallaye 53.
Sai dai hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta bukaci dan kwallon ya dawo ya taka wa kasarsa leda a wasan saboda a martaba shi don bajintar da ya nuna lokacin da yake wakiltar kasarsa a wasan kwallon kafa.
Wasan ne kuma zai zama wasan da zai yi wa Ingila na karshe, abin da zai sa ba zai buga wasan da kasar za ta yi da Kuroshiya ba a gasar Nations League a ranar Lahadi mai zuwa.