FA ba za ta hukunta Aguero kan fada da dan kallo ba

'Yan kallo sun mamaye fili bayan wasan Wigan da Man City
Bayanan hoto, Sergio Aguero ya ce mutumin da ya yi sa-in-sa da shi ya tofar masa yawu ne kuma ya zage shi
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta ce ba za ta hukunta dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero ba, a kan sa-in-sa da ya yi da wani dan kallo bayan an tashi daga wasan da Wigan ta fitar da su da ci 1-0, a gasar cin kofin FA ranar Litinin.

A wani hoton talabijin an ga Aguero yana ture wani dan kallo wanda kuma daga baya ya ce mutumin ne ya tofar masa yawu da kuma zaginsa.

Hukumar ta FA ta tuhumi dukkanin kungiyoyin biyu da laifin kasa tsawatar wa 'yan wasansu bayan da alkalin wasa ya kori Fabian Delph na Manchester City.

Jan katin da alkalin wasan ya ba wa Delph a kashin farko na wasan ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin kociyan City Pep Guardiola da takwaransa na Wigan Paul Cook a lokacin da suka kama hanya ta zuwa hutun rabin lokaci, amma hukumar ta FA ta ce ba wani abu na saba doka da ya faru a tsakaninsu.

Kungiyoyin suna da wa'adin zuwa karfe bakwai na yamma agogon Najeriya da Nijar ranar Juma'a su bayar da bahasi.

Sannan kuma an bukaci Wigan da Man City din su gabatar wa hukumar abin da suka sani game da kutsen da 'yan kallo suka yi zuwa cikin fili bayan an tashi daga wasan.