Rahoto na musamman kan hako man fetur
An wallafa
Cikin watan jiya ne gwamnatin Najeriya ta kaddamar da ayyukan bunkasa hako man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.
Yayin bikin kaddamarwar shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa kamfanin man kasar NNPCL umarnin fadada aikinsa don jan yo masu zuba jari da nufin bunkasa haƙo man fetur din a karon farko a arewacin kasar.
Kamfanin samar da man fetur na Najeriya NNPCL ya ce tun shekara biyu da ta wuce ne aka tabbatar da gano tarin arzikin man fetur mai yawan da za a iya sayarwa a yankin.
Ga rahoto na musamman da Zahraddeen Lawan ya hada mana.