Wannan shirin ya yi tsokaci ne kan darussan yakin Biafra
An wallafa
A wannan makon ne Najeriya ta cika shekara hamsin da kawo karshen yakin basasar da aka yi a kasar, wanda ya yi sanadin asarar miliyoyin rayukan jama'a da dukiya. Fiye da shekara uku aka shafe ana yakin wanda na daga cikin yake mafiya muni da aka yi a nahiyar Afrika a karni 20. Wadanne abubuwa ne suka haddasa yakin basasar? Me wadanda aka yi abin kan idonsu ke iya tunawa game da shi? Kuma wadanne irin darussan ne al'ummar kasar ta koya daga yakin? Wadannan su ne abubuwan da muka tattauna a filin na Ra'ayi Riga na wannan makon!