Daruruwan nakasassu suka gudanar da zanga-zanga a birni Kano don nuna adawa da dokar hana bara a jihar.
Bayanan hoto, Kungiyoyin nakasassu da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a Kano ciki hadda guragu don nuna adawa a kan dokar hana bara a cikin jihar.
Bayanan hoto, Mambobin kungiyar kutare ma sun shiga cikin zanga-zangar don neman gwamnati ta sauya matsayinta.
Bayanan hoto, Nakasassu sun yi dandazo a gaban ofishin majalisar dokokin jihar Kano don a sauya dokar.
Bayanan hoto, Guragu mata ma sun fito don karawa zanga-zangar armashi, saboda watakila gwamnati ta sake duba lamarin.
Bayanan hoto, Jami'an tsaro a majalisar dokokin jihar Kano sun kafa shingen da nakasassu ba zasu wuce ba lokacin zanga-zangar.
Bayanan hoto, An kiyasta cewar akwai mabarata kusan miliyan daya da rabi a jihar Kano.
Bayanan hoto, An rufe kofar shiga Majalisar Dokokin Jihar Kano don kada masu zanga-zangar su kai cikin zauren majalisar.
Bayanan hoto, Shugaban kungiyar nakasassu ta jihar Kano, Aminu Ahmed Tudun Wada ya bayyanawa manema labarai abinda suke son su cimma wajen zanga-zangar.