Gane Mani Hanya: Tsarin bankin Musulunci
An wallafa
A kwanan baya ne aka yi wani babban taro a nan London, a kan hada-hadar kudade bisa tsarin shari'ar musulunci.
A cewar Praministan Birtaniya, David Cameron, an yi taron ne a London da zummar ganin birnin na London ya zama cibiyar hada-hadar tattalin arziki bisa tsarin musulunci.
Masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arziki daga kasashe dabam-dabam ne suka halarci taron.
To sai dai a Najeriya, kokarin bullo da tsarin banki irin na musulunci ya haddasa cece-kuce.
Malam Sanusi Lamido Sanusi, shi ne gwamnan babban bankin Najeriyar CBN, kuma ya halarci taron na London.
Daga bisani ya zo nan BBC, kuma Isa Sanusi ya tattauna da shi inda ya fara da tambayarsa muhimmancin taron: