Hotuna: Wuraren da za'a yi wasannin Olympic a Landan

An wallafa

Hotunan wuraren da za'a yi wasannin Olympic da birnin Landan zai karbi bankonci a badi.

A kowanne shekaru hudu ne ake gasar Olympics, kuma bayan wanda akayi a Beijing na kasar China a shekara ta 2008, sauran shekara guda cif a fara wata sabuwar gasar ta Olympics da birnin London zai dauki bakunci a badi.
Bayanan hoto, A kowanne shekaru hudu ne ake gasar Olympics, kuma bayan wanda akayi a Beijing na kasar China a shekara ta 2008, sauran shekara guda cif a fara wata sabuwar gasar ta Olympics da birnin London zai dauki bakunci a badi.
A lokacin gasar dai, 'yan wasa 10,500 ne zasu fafata daga kasashe 200.
Bayanan hoto, A lokacin gasar dai, 'yan wasa 10,500 ne zasu fafata daga kasashe 200.
Zasu samu rakiyar jami'ai da masu horaddasu kusan kimanin 5000.
Bayanan hoto, Zasu samu rakiyar jami'ai da masu horaddasu kusan kimanin 5000.

Ana sa ran halartar manema labarai har su 20,000 da dubbban 'yan kallo daga kasashe daban daban na duniya.
Bayanan hoto, Ana sa ran halartar manema labarai har su 20,000 da dubbban 'yan kallo daga kasashe daban daban na duniya.

Za a shafe kwanaki 17 ne ana fafatawa a wasanni 26 a yayinda za a bada kyautuka guda 300.
Bayanan hoto, Za a shafe kwanaki 17 ne ana fafatawa a wasanni 26 a yayinda za a bada kyautuka guda 300.
A matakin soma bikin, an soma kidayan kwanakin da suka rage wato count down na fara wasannin a dandalin Trafalgar a Ladan.
Bayanan hoto, A matakin soma bikin, an soma kidayan kwanakin da suka rage wato count down na fara wasannin a dandalin Trafalgar a Ladan.
Wadanda ke shirya bukin sunce komai na tafiya dai dai kamar yadda aka tsara.
Bayanan hoto, Wadanda ke shirya bukin sunce komai na tafiya dai dai kamar yadda aka tsara.
Paul Deighton Shugaban kwamitin shirya gasar yace haryanzu da sauran aiki, amma kuma yana alfahari da yadda abubuwa ke tafiya.
Bayanan hoto, Paul Deighton Shugaban kwamitin shirya gasar yace haryanzu da sauran aiki, amma kuma yana alfahari da yadda abubuwa ke tafiya.
Shugaban kwamitin ya shaidawa BBC cewa baza'a samu matsala ba wajen samarwa jama'a tikitin shiga kallon wassanin.
Bayanan hoto, Shugaban kwamitin ya shaidawa BBC cewa baza'a samu matsala ba wajen samarwa jama'a tikitin shiga kallon wassanin.
Paul Deighton ya ce; "akwai tikiti masu yawa kuma mutane na son suyi ta tanadinsu, sai mukayi tunanin cewa ayi kuri'a, don haka ne hanya mafi a'a la da zamu samarwa mutane tikiti."
Bayanan hoto, Paul Deighton ya ce; "akwai tikiti masu yawa kuma mutane na son suyi ta tanadinsu, sai mukayi tunanin cewa ayi kuri'a, don haka ne hanya mafi a'a la da zamu samarwa mutane tikiti."
Sai dai wasu na ganin cewa abun na 'yan boko ne kawai kuma akwai almubazzaranci a ciki.
Bayanan hoto, Sai dai wasu na ganin cewa abun na 'yan boko ne kawai kuma akwai almubazzaranci a ciki.

An kashe dala biliyan 15, akan shirye-shiryen, abunda ya zarta kasafin da akayi tun farko.
Bayanan hoto, An kashe dala biliyan 15, akan shirye-shiryen, abunda ya zarta kasafin da akayi tun farko.