Mu kwana lafiya
Jama'a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa. Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau.
Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Buhari Muhammad Fagge and Ahmad Tijjani Bawage
Jama'a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa. Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau.
Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Shugaba Bola Tinubu ya isa Legas don gudanar da bikin karamar sallah.
Shugaban ya bar Abuja, babban birnin Najeriya a yau Lahadi domin zuwa mahaifarsa.

Asalin hoton, Dada Olusegun/X

Asalin hoton, Dada Olusegun/X

Asalin hoton, Dada Olusegun/X

Asalin hoton, Fadar Sarkin Musulmi
Kwamitin ganin wata na Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar Musulmin ƙasar su fara duban watan Shawwal a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da kwamitin ya fitar yau Lahadi a Sokoto.
"Duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi," in ji sanarwar.
Fadar Sarkin Musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar.

Asalin hoton, Reuters
Harin ranar 7 ga watan Oktoba ya kaɗa Isra'ila sama da duk yadda ake tsammani. Hakan ya tilasta mata fitowa da dakarunta don yin duk abun da za ta iya wajen rushe Hamas.
Yanzu wata shida kenan, amma ana ayyana yaƙin a matsayin mafi muni da salwantar rayuka da duniya ta shaida a tarihin bayan nan.
Isra'ila ta ce wai tana harin mutanen da ke ɗauke da bindiga ne kawai da suka kai mata hari. Sai dai abin da duniya ke ganin shi ne yadda ake durƙusar da Gaza kan gwiwowinta.
Za a iya cewa an yi wa Hamas illa amma dai ba a ci galaba a kanta ba.
Manyan ƙawayen Isra'ila na kusa da suka haɗa da Amurka da Burtaniya, yanzu suna amfani da kakkausan yare wajen kiran tsagaita wuta cikin gaggawa domin kare fararen hula ciki har da masu aikin agaji da Isra'ila da take da dama.
Watakila wannan rikicin na Isra'ila da Gaza mafi dadewa ya zo ƙarshe a kusa. Amma mutanen Gaza da yunwa ta yi wa katutu ba sa ganin hakan zai faru a kusa.
A gafe guda kuma ci gaba da riƙe Isra'ilawan da Hamas ke yi na ƙara rura wutar zanga-zanga kan Firaiminista Netanyahu.

Asalin hoton, NDLEA/X
Jami'an Hukumar da ke Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke wani fasinja a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke jihar Legas ɗauke da kullin hodar iblis guda 80.
An kama Ogbonna ne a ranar Lahadi, 31 ga Maris, 2024, a lokacin da yake yunkurin hawa jirgin Qatar Airways zuwa birnin Delhi na ƙasar Indiya, ɗauke da fasfo ɗin ƙasar Laberiya.
NDLEA ta bayyana kama mutumin ne a wata sanarwa da kakakinta Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi.
Babafemi ya ce an yi wa wanda ake zargin gwaje-gwaje, inda aka gano cewa yana tu'amalli da miyagun kwayoyi.
“Mun yi mamaki da muka gano yawan kwayoyi da a haɗiye a cikinsa, nan da nan ya fara yin amai na kullin hodar iblis da ya haɗiye," in ji Babafemi.
NDLEA ta ce mutumin da ake zargi ya yi iƙirarin cewa wani dan uwansa ne ya ɗauke shi aiki don ya rika safarar kwayoyi.
An kuma samu ɗaurin hodar iblis guda 80 mai nauyin kilogram 889 a wajensa wanda ya amayar cikin kwanaki huɗu.
“Abin da ya kusa janyo ya rasa rayuwarsa shi ne, Ogbonna ya ce an ba shi kwayoyi domin ya hadiye a wani otel a Ikeja, tare da yi masa alkawarin tukuicin Naira 300,000 idan ya yi nasarar kai hodar iblis din zuwa Indiya,” in ji sanarwar NDLEA.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da cewa an kara kashe jami’anta guda huɗu a Gaza.
Ta ce wasu mayakan Hamas ne suka yi musu kwantan ɓauna a birnin Khan Younis, da ke kudancin Zirin Gaza.
Gwamnatin Isra’ila ta ce sojojin ƙasar 604 ne aka kashe tun fara yaƙi a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba.
Firaminsta Benjamin Netanyahu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasa ransu a wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasar.

Asalin hoton, Ndume Facebook
Babban mai tsawatarwar Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce ba wannan ne lokacin da ya dace a yi ƙarin kuɗin wutar lantarki ba ga 'yan ƙasar.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Sanata Ndume ya ce wutar da babu ita ta yaya za a yi ƙarin kuɗi a kanta, ya shawarci gwamnati da ta fara samar da ita gabanin yin ƙarin kudinta.
"Babbar maganar ita ce kamfanonin da aka raba musu tashoshin bayar da wutar nan ba su biya kudaden ba ma tukunna har yau. Na biyu babu wutar, tun da aka ba su ba su habbaka yayyukansu ba.
"Gwamnati ta cefananr da wutar da zimmar ko za ta habbaka, amma kullum ƙara taɓarɓarewa take yi," in ji Sanatan.
Ya ce da zarar majalisarsu ta koma hutu a ranar 16 ga watan Afrilu, shi da wasu abokan aikinsa za su jagoranci gabatar da ƙuduri kan janye wannan ƙarin.
Za kuma su bayyana cewa ya kamata duk abin da za a yi da ya shafi rayuwar talakawa ya ji ra'ayoyinsu gabanin aiwatar da shi, za kuma a iya cimma haka ne ta sauraren ra'ayinsu 'yan majalisa a matsayin wakilan al'umma.
"Kamata ya yi idan za a ƙara kuɗin wuta a samar da ita, a ƙara albashin ma'aikata sannan a tabbatar da hauhawar farashin kayayyaki ya yi ƙasa".
Ya kuma ce abin kunya ne raba wutar lantarki mataki daban-daban, akwai ta masu kuɗi akwai ta talakawa.

Asalin hoton, Getty Images
Kafofin watsa labaran Isra'ila sun ce ƴan sanda a Tel Aviv sun tarwatsa dubun dubatar masu zanga-zangar ƙin jinin gwamanti da ke neman a sako ƴan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.
Rikici ya ɓarke tsakanin ƴan sandar da masu zanga-zangar, lamarin da janyo aka kama mutum huɗu sakamakon toshe babban titi da masu zanga-zangar suka yi.
A ranar Asabar gwamnatin Isra'ila ta ce ta gano gawar ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a gabashin Gaza, sai dai yar uwarsa ta ce sakacin gwamnatin Isra'ila ne ya kashe mata shi.

New Zealand ta sanar da ƙara tsaurara dokokin karbar 'yan ci-rani domin rage yawan kwarar da su ke yi cikin ƙasar, wanda ta ce adadinsu a bara ya kai inda ba a taɓa gani ba.
Mutum 173,000 ne suka shiga ƙasar, adadin da gwamnati ta ce ba za ta iya ci gaba da gudanarwa ba.
Ƙasar New Zealand na da yawan mutanen da ba su fi miliyan biyar ba.
Wata sabuwar doka ta ce daga yanzu za a riƙa yi wa 'yan ci-rani jarrabawar yaren turanci mai tsauri ga ma'aikatan da ba su da kwarewa sosai, kuma za a rage tsayin lokacin da wasu mutanen da za su riƙa kwashewa a ƙasar.
Itama Australia kwanan nan ta gabatar da wasu tsauraran dokoki domin rage kwararar 'yan ci-rani.

Athelic Bilbao ta kawo ƙarshen jiran da ta kwashe shekara 40 tana yi domin ta lashe kofin Copa del Rey, bayan nasarar da ta yi kan Mallorca a bugun fenareti a ƙarshen wasan.
Athletic Bilbao ta lashe kofin karo na 24 kuma na farko tun 1984 - lokacin Alex Berenguer da ta yi nasara a bugun fenareti da ci 4-2 a Seville.

An riƙa ihu da tafi bayan nasarar saboda ciwon da ƙungiyar ta ji a baya na zuwa wasan ƙarshe a gasar sau biyu a 2021 kuma tana rashin nasara.
A minti na 21 ne Dani Rodriguez ya ci wa Mallorca kwallo, wato gabanin tafiya hutun rabin lokaci.
A minti na 50 Oihan Sancet ya farkewa Athletic Bilbao.

Asalin hoton, La Liga

Asalin hoton, de
Gwamnatin Ecuador ta ce jami'an tsaro sun kutsa ofishin jakadancin Mexico domin kamo tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ke ƙoƙarin tserewa daga hannun jami'an tsaro.
An kai Jorge Glas a gidan yarin ƙasar mafi tsaro ne bayan da aka kamo shi saboda zargin cin hanci da rashawa.
Ministar harkokin ƙasashen wajen ƙasar Gabriela Sommerfeld ta ce sun dakatar da duk wata huldar diplomasiyya tsakanin su da Mexico.

Asalin hoton, X
Jam'iyar Republican ta ce an tara sama da dala miliyan hamsin a wajen taron hadawa Donald Trump kudin tallafin tsayawa takara a Florida.
Daruruwan mutane ne suka halarci taron wanda attajirin nan John Poulson ya jagoranta.
Tikiti mafi tsada shi ne na zama kusa da Trump din wanda aka sayar sama da dalar Amurka dubu dari takwas.
Sai dai tsohon shugaban Amurkar ya kasa samun kwatankwacin kudaden da abokin karawarsa Joe Biden ya tara.

Asalin hoton, Reuters
Alƙaluman da aka tattara cikin watanni shidan da aka kwashe a na rikin Gaza na ƙara zama masu tayar da hankali.
Sama da mutanen Gaza 33,000 mafi yawansu fararen hula aka kashe, kamar yadda alƙaluman hukumar lafiya ta Falasdinu suka bayyana.
Alƙaluman da ma'aikatar ta saki a ranar 5 ga watan Afrilun nan sun nuna sama da kashi 70 na waɗanda aka kashe mata ne da ƙananan yara.
A cewar kungiyar Save the Children an ƙashe ƙananan yara a Gaza 13,800 an kuma raunata sama da 12,009.
Asusun tallafawa ƙananan yara na duniya ya ce an yankewa yara sama da 1,000 kafa daya ko kuma biyu a Gaza daga fara rikicin.
An tilastawa sama da mutum miliyan 1.7 barin muhallansu a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Asalin hoton, PO
A Najeriya, jam'iyun adawa sun soki matakin gwamnatin ƙasar na ƙara kudin wutar lantarki ga masu amfani da layin Band A da ake samun wuta tsawon sa'o'i 20.
Jam'iyar PDP da Labour sun ce matakin zai ƙara haifar da matsi ne ga ƴan ƙasar, babu wani abu bayan wannan.
Tun bayan sanar da matakin ƙarin kuɗin wutar da gwamnatin Najeriya ta yi, take fuskantar suka daga ɗaiɗaikun mutane ƙungiyoyi da kuma jam’iyyun siyasa na ‘yan adawa.
Sai dai gwamnatin Shugaba Tinubu ta ce da gwamnatin Najeriyar tana daukan dumar magaji da nishi ne..kasancewar dawainiyar ta fi karfinta…ga shi `yan kasa ba sa amfana daga tallafin naira sama da tiriliyan 3 da bangaren wutar ke lashewa a kowacce shekara. Amma da wannan za ta iya riƙa tsira da naira tiriliyan daya kowacce shekara da za ta iya karkatarwa zuwa ga ayyukan raya ƙasa.
A yammacin ranar Juma’a tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasar a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa a shafukansa na sa da zumunta cewa, "kamar yadda aka saba gwamnati ta ƙara yi wa talaka shaƙar mutuwa, ba tare da sanarwa ko ba da wa’adi ba, a kuma hakan matsi zai ƙara ga tattalin arziki".
Irin dai wannan ra’ayi ne da jam’iyyar adawa ta Labour kamar yadda kakakinta Dr Yunusa Tanko ya yi ƙarin bayani.
"In gwamnati ba za ta iya ba ta kauce ta ba da wuri, amma abin babu tausayawa a ciki, dame za mu ji, arin kuɗin mai ko hauhawar farashin kayayyaki?"
Abdul’aziz Abdul’aziz na cikin masu taimakawa shugaban Najeriya kan harkokin yaɗa labarai, ya ce gwamnati ta tsinci kanta ne cikin tsaka mai wuya na kudaden tallafin da take biya a bangaren wutar lantarki.
"Abu ne da za ka iya cewa ya zama babu yanda za a yi, kuɗin da ake kashewa kan tallafin wuta kuɗaɗe ne masu yawa, kuma kamfanin da yake tafiyar da harkar yace babu kudinma a kasafin kudi na bana.
"A yanzu haka kamfanonin da suke rarraba wutar suna bin gwamnati makudan kudade na tallafin da ake biya. To ai babu ma'ana a ce ko da yaushe sai an kabo bashi za a biya wannan tallafi, kuma da za a karkatar da kudaden wani wuri da sun yi amfani." in ji shi.
Abdul’aziz ya ƙara da cewa da sannu talakawan Najeriya za su yi farin ciki da wannan tsari a gaba.
Yau ake bikin ranar lafiya ta duniya, wadda Majalisar ɗinkin Duniya ta ware ranar 7 ga watan Afrilun ko wacce shekara domin faɗakar da al'umma muhimmancin ranar. Take bikin na bana shi ne "Lafiyata 'yanci na"..
Sai dai bikin na bana na zuwa ne lokacin 'yancin lafiyar miliyoyin mutane a faɗin duniya ke fuskantar barazana.
Cutuka da annoba sun janyo mutuwar mutane da dama tare da nakasta wasu.
Rikice-rikice sun tarwatsa rayuwar miliyoyin mutane a fadin duniya, wasu sun mutu dalilin hakan, wasu kuma suna fama da yunwa ga matsanaciyar damuwa.
Hayaƙi mai gurɓata muhalli ya riƙa janyo rikicin sauyin yanayi kuma hakan ya riƙa tauyewa mutane haƙƙinsu na shaƙar tsaftatacciyar iska, a cikin gidaje ko a wuraren aiki gurbatar muhalli na kashe mutum guda duk sakan biyar.
Mutum biliyan hudu da rabi 4.5 sama da rabin yawan mutanen duniya ne aka yi ƙiyasin ba su samu kulawar lafiya kamar yadda ya kamata a 2021.
Umayma Sani Abdulmumini ta tambayi Dr Nasiru Sani Gwarzo likita mai kula da lafiyar al'umma a Najeriya kan muhimmancin ranar, sai dai ya fara ne da bayani kan taken ranar.

Asalin hoton, Reuters
Jirgin ruwan sojin Birtaniya ya bi ta gabashin tekun Bahrun domin kai kayan agaji a Zirin Gaza.
Birtaniya ta ce hanyar za ta taimaka wajen samar da sabuwar hanyar kai kayan agaji daga yankin Cyprus.
Amurka da ƙawayenta sun samar da tashar jirgin ruwan wucin gadi a Gaza da za a riƙa sauke kayan agajin.
A Isra'ila kuwa ana ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da Netanyahu.

Asalin hoton, AS
A yau Lahadi ne Rwanda ta fara alhinin cika shekara talatin da kisan kiyashin kan ƙabilar Tutsi da masu sassaucin ra'ayi ƴan hutu.
Za a gudanar da taruka a dukkan sassan ƙasar da duniya baki daya domin tunawa da wadanda aka kashe.
Shugaban ƙasar Paul Kagame ne zai jagoranci wanda za a yi a babban birnin kasar Kigali.
Za kuma a dakatar da kunna kade-kade da wasanni da fina-finai a gidajen radiyo da talabijin yayin makoki na mako guda da za a yi ƙasar.
Masu bin wannan shafi namu da fatan an wayi gari lafiya.
Buhari Muhammad Fagge ke fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Ku kasance da mu.