A shirye muke don zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasa - Shugaban INEC

Wannan shafi na kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bibiyar BBC Hausa, nan za mu dakata da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Tsohon wakilin Italiya a EU ya cimma masaya da masu gabatar da ƙara

    Babban mutumin da ake zargi da laifin rashawa kan tuhume-tuhumen da ake yi wa kungiyar tarayyar Turai EU, ya cimma matsaya da masu gabatar da kara na kasar Belgium.

    Tsohon wakilin kasar Italiya a majalisar EU, Pier Antonio Panzeri, zai samu sassauci a hukunci zaman gidan yari da aka yanke masa, saboda yin musayar wasu bayanai.

    Sannan zai biya tara, kuma zai fuskanci hukuncin kwace wasu kaddarorinsa na kusan dala miliyan guda.

    Mr Panzeri, yana daga cikin mutane hudun da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da zambar kudi, bayan wasu zarge-zargen da suka bayyana cewar, kasashen Qatar da Morocco sun baiwa jami'an cin hanci, da nufin jan ra'ayin majalisar wakilan kungiyar ta EU.

    Koda yake kasashen biyu sun musanata zargin da ake musu na aikata ba daidai ba.

  3. Dakarun Najeriya sun kashe 'yan fashin daji tare da lalata sansaninsu a Kaduna

    sojoji

    Rundunar sojin Najeriya da ke yaƙi da 'yan bindiga ta 'Operation Forest Sanity' ta kashe 'yan fashin daji biyu tare da lalata sansaninsu a yankin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

    A wata sanarwa da kwamishinan al'amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar ya ce dakarun sojin ƙasar sun samu nasarar kakkaɓe sansanonin 'yan bindigar a wani samame da suka kai dajin Kaboresha zuwa Rijana, a yankin Kachia.

    Mista Aruwan ya ce dakarun sojin sun shirya kwantan ɓauna a kan hanyar Gwanto zuwa Kwasau, daga nan kuma suka buɗe wuta kan 'yan fashin da ke fuskantar yankin a kan babaru.

    Lokacin gumurzun, sojojin sun kashe 'yan fashin daji biyu tare da kwato babura uku.

    Haka kuma ya ce sojojin sun kai samame sansanonin 'yan fashin dajin da ke yankin Kuturu-Rijana, inda 'yan fashin dadjin suka gudu bayan da suka hangi jami'an tsaron, wadan su kuma suka wargaza sansanonin.

    Sauran kayayyakin da sojojin suka ƙwato sun haɗar da tufafin soji, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

  4. Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama tufafin sojoji da ƙwayoyi masu yawa

    kwastam

    Hukumar kostom mai yaƙi da fasa ƙwauri da ke a filin jirgin sama na Murtala Muhammad a birnin Legas, ta kama tufafi da sauran kayayyakin sojoji da na ‘yan sanda waɗanda take zargin an shigo da su daga Afirka ta kudu, ba bisa ka’ida ba.

    Babban jami'in hukumar mai lura da tashar jirgin saman na Legas Bello Kaniyal Dangaladima, ya shaida wa BBC cewa daga cikin kayyakin da aka kama har da Riguna da hulunan kwano na sojoji, da kayayakin 'yan sanda

    Ya kuma ce akwai kuma nau’in ƙwayoyin Tramadol da ake kira (aji garau)da kuɗinsu ya haura naira biliyan talatin da bakwai da aka shigo da su daga ƙasashen Indiya da kuma Pakistan.

    Wannan kame dai na zuwa a daidai lokacin da Naijeriya take shirin gudanar da babban zabe na shugaban kasa a watan Gobe.

  5. A shirye muke don zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasa - Shugaban INEC

    Mahmood

    Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman ƙanta a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa a shirye take game da zuwa zaɓen zagaye na biyu na shugaban ƙasar idan har ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko ba.

    Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar na tunkarar babban zaɓen ƙasar da ke tafe a Chatham House da ke birnin Landan a Birtaniya.

    Ya ƙara da cewa a INEC ta yi shirin yiyuwar zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, kamar yadda take yi a zaɓuka uku da suka gabata.

    Shugaban hukumar zaɓe ya kuma ce zaɓen ƙasar da za gudanar cikin wannan shekara zaɓe ne na matasan ƙasar.

    Farfesa Yakubu ya kuma ce rajistar masu kaɗa ƙuri'a ta nuna cewa matasa ne suka mamaye adadi mafi yawa na masu rajistar zaɓen.

    Shugaban Hukumar ya ce ya ji daɗin yadda mutane suka fito domin karɓar katinan zaɓensu, yana mai cewa fiye da mutum 600,000 sun karɓi katinansu a jihar Legas kaɗai cikin watan da ya gabata.

    Ya ƙara da cewa a yanzu adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya sun kai miliyan 93.4, kuma daga ciki miliyan 37 wato kashi 39 na rajistar zaɓen matasa ne 'yan tsakanin shekara 19 zuwa 34.

    Ya kuma tunasar da maharta taron cewa hukumar za ta tsayar da rabar da katin zaɓen daga ranar 29 ga watan Janairun da muke ciki.

  6. Gwamnatin Najeriya ta kammala yi wa sabuwar ƙungiyar malaman jami'a ta CONUA rajista

    Ngige

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kammala yi wa sabuwar ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasar mai suna 'Congress of University Academics' (CONUA).

    Ministan ƙwadago na ƙasar Dakta Chris Ngige, ne ya bayyana haka ga manema labarai jim ƙadan bayan tattaunawar sirri da shugabannin sabuwar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugabanta Niyi sunmonu.

    Ministan ya kuma gargaɗi sabuwar ƙungiyar da cewa kada ta ɗauki hanyar da takwararta ta 'Academic Staff Union of Universities' (ASUU). ta bi

    Ya umarci ƙungiyar da ta yi aiki a duka jami'o'in ƙasar ba tare da fargabar kowa ba, yana mai cewa gwamnati ta ɗauki matakin kawar da 'katutun' da ASUU ta yi tare da lalata tsarin jami'o'in ƙasar.

    A shekarar da ta gabata ne dai aka ƙirƙiri sabuwar ƙungiyar lokacin da kan malaman jami'o'in ƙasar ya rabu kan yajin aikin da ƙungiyar ASUU ta share kusan wata takwas tana gudanarwa a faɗin ƙasar

  7. Sri Lanka na shirin jinkirta biyan albashin ma'aikata

    Majalisar gudanarwar ƙasar Sri Lanka za ta jinkirta biyan albashin wasu daga cikin ma'aikatu da hukumomin ƙasar har zuwa nan da wasu makonni.

    A makon da ya gabata, gwamnatin ƙasar ta ayyana cewa tattalin arzikin kasar zai yi matukar durkushewa fiye da yadda ake tsammani.

    Gwamnatin Colombo ta umarci dukkan ma'aikatun kasar da su zaftare kashi biyar bisa dari na kudaden da suke kashewa.

    Asusun bada lamini na IMF ya amince zai yafewa kasar kusan dala biliyan uku domin saukaka mata yadda zata warware dunbun bashin da ake binta.

  8. Firaministan Pakistan zai tattauna da takwaransa na Indiya

    Shehbaz/Modi

    Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya mika bukatar tattaunawa da takwaransa na Indiya Narendra Modi, domin dinke baraka kan bangarorin da kasashen biyu ke takaddama kansu, ciki har da batun rikici kan yankin Kashmir.

    A tattaunawarsa da kafar yada labarai ta Al Arabiya, Sharif yace yana bukatar gudanar da muhimmiyar tattaunawa ta gaskiya tare da takwaran nasa.

    Yace babu abinda yaki ya haifar ga kasashen biyu sai takaici da talauci da rashin aikin yi.

    Kasashen Indiya da Pakistan sun sha gwabza yaki tun bayan samun 'yancin kai daga Birtaniya a 1947.

  9. Shugaban ƙasar Vietnam ya yi murabus

    Vietnam

    Shugaban kasar Vietnam, Nguyen Xuan Phuc, ya sauka daga muƙaminsa, jim kadan bayan murabus din mataimakan firaministan biyu.

    Dukkan jami'an gwamnatin sun rasa ayyukansu ne sakamakon tsattsauran shirin yaki da rashawa, wanda babban sakataren jam'iyyar kwaminisanci na kasar Nguyen Phu Trong ya kaddamar.

    A bara ne yayi nasarar lashe wa'adin mulki na uku, wanda hakan bai taba faruwa ba a tarihin kasar.

    Wakilin BBC a shiyyar ya rawaitro cewa, shugaban yayi kokarin karfafa ikonsa a yayin da yake rike da madafun iko.

    Sama da mambobin jam'iyyar 500 ne aka gurfanar ko kuma aka ladaftar da su bisa zarginsu da laifukan rashawa da aikata ba daidai ba a shekarar 2022.

    Kawo yanzu dai, babu tabbacin ko wanene zai iya kasancewa sabon shugaban kasar.

  10. 'Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu shida a Katsina

    Bandits

    Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu shida har da wata mata mai ciki a ƙauyen Jajar Kanwa da ke karamar hukumar Jibia na jihar Katsina.

    Wasu mutum uku kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa mazauna ƙauyen sun ce mutum biyu daga ciki sun mutu nan take yayin da matar kuma ta rasu a wani asibiti a Katsina wajen da aka kai ta domin bata kulawar lafiya.

    An kuma ruwaito cewa 'yan bindigar sun tafi da awaki da tumaki da ba a san adadinsu ba bayan sun sanya wa mazauna garin biyan harajin 20,000 kowanne.

  11. Wolves ta cimma yarjejeniyar ɗauko Sarabia kan yuro miliyan 4.4 daga PSG

    Sarabia

    Kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton Wanderers ta amince ta biya yuro miiyan 4.4 domin ɗauko ɗan wasan Paris St-Germain, Pablo Sarabia.

    Ɗan wasan mai shekara 30 ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da rabi, inda za a gwada lafiyarsa a ranar Talata. Shi ne ɗan wasa na uku da kungiyar ta ɗauka a bana.

    Ya koma PSG ne daga Sevilla a 2019 inda ya zura kwallo 11 a wasa 35 da ya buga a gasar Ligue 1.

    Sarabia ya shafe kakar 2021-22 a matsayin ɗan aro a Sporting Lisbon, inda ya buga wa Spain wasa ɗaya a gasar cin kofin duniya da aka kammala.

    Tun lokacin da ya fara buga wa Sifaniya wasanni a shekarar 2019 ,ya samu nasara a wasa 26, inda ya zura kwallaye tara.

    Ɗan wasan sananne ne a wajen kocin Wolves Julen Lopetegui saboda ya horar da shi lokacin da yake kocin Sevilla.

    Sai dai Sarabia bai taba buga wasa ba a karkashin Lopetegui lokacin da yake kocin Sevilla kafin ya koma PSG.

  12. Masar ta saki mutum 31 da aka zarga da ƴaɗa labaran ƙarya

    Ƙasar Masar ta saki mutum 31 da aka tsare kan zargin ƴaɗa labaran ƙarya.

    Wannan ne karo na biyu tun shiga wannan shekara da aka saki irin waɗannan mutane a wani afuwa na shugaban ƙasa.

    Wani ɗan gwagwarmaya Hassan Mustafa da wani mai zane-zane Amir Abdel-Ghani na cikin mutanen da aka sake bayan tsare su na shekaru da dama.

    Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce Masar ta tsananta takunkumin da ta yi wa 'yancin fadin albarkacin baki a ƙarkashin Shugaba Abdul Fattah al-Sisi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Mutum 18 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Sokoto-Kebbi

    Accident

    Akalla 'yan kasuwa 18 ne suka rasu a hatsarin mota kan hanyar su ta kai shanu zuwa Legas daga Sokoto a yammacin ranar Litinin.

    A cewar rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, ta ce an kai fasinjoji 42 da suka samu raunuka a hatsarin zuwa asibiti a yankin Gwandu da ke jihar.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa shanu 16 sun rasu a hatsarin.

    Kakakin 'yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban wata babbar mota ɗauke da fasinjoji da shanu daga yankin Illela na jihar Sokoto ya kauce hanya a mahaɗar Malisa, inda nan take motar ta faɗi kasa.

    Ya ce hakan ne ya janyo rasuwar fasinjoji 18 yayin da 42 kuma suka samu raunuka daban-daban.

    SP Nafiu Abubakar ya kara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kebbi, Ahmed Magaji Kontagora, ya tura jami'an 'yan sanda zuwa wajen domin ɗaukar waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don yi musu magani.

    Kwamishinan 'yan sandan ya miƙa ta'azziya zuwa ga iyalan waɗanda suka rasu, inda kuma ya buƙaci kungiyoyin NURTW da NARTO da sauran masu amfani da hanya da su rika lura da abubuwan rage gudu da kaucewa ɗaukar kaya fiye da ƙima da kuma mayar da hankali yayin tuki.

  14. Shakhtar Donetsk za ta tallafa wa ƴakin Ukraine da kuɗin da ta sayar da Mudryk

    Shakhtar Donetsk

    Shugaban kungiyar Shakhtar Donetsk Rinat Akhmetov, ya yi alkawarin tallafa wa ƴakin Ukraine da £22m bayan sayar da Mykhailo Mudryk zuwa Chelsea.

    Chelsea ta sayi ɗan wasan ne a ranar Lahadi kan kuɗi £89m, wadda shi ne irinsa na farko da aka sayi ɗan wasa daga Ukraine.

    Akhmetov ya ce kuɗin zai taimaka wa wani shiri na koƙarin mazauna Mariupol da kuma iyalan sojoji da aka kashe.

    "Ina son na gode wa dukkan mutane a faɗin duniya da suka taimaka wa Ukraine," a cewar Akhmetov.

    "Muna iya magana a kan kwallon kafa a Ukraine a yau saboda taimakon sojojin ƙasar da mutanenta da kuma goyon bayan illahirin duniya." in ji Akhmetov.

    Rasha ta mamaye Ukraine ne a watan Febrairun 2022.

  15. An samu fashewar wani abu a sansanin sojin Somaliya

    Somalia

    An jiyo ƙarar bindiga da abubuwan fashewa a safiyar Talata a sansanin sojin Somaliya a garin Hawadley da ke kusa da yankin Shabelle na ƙasar.

    Hukumomi sun ce suna zargin mambobin kungiyar masu iƙirarin jihadi ta al-Shabab da kai harin.

    Abin fashewar ya janyo rasuwar wani babban jami'in soja, sai dai ba a san iya adadin mutanen da abin ya rutsa da su ba.

    Harin na zuwa ne kwana guda bayan da sojojin ƙasar suka kwace iko da birnin Haradhere mai muhimmanci, wanda ke hannun al-Shabab sama da shekara 15.

    Al-Shabab ta rasa yankuna da dama tun watan Agustan bara, lokacin da sojojin gwamnati da taimakon wasu mayaka suka kaddamar da hare-hare a yankin kudanci da kuma tsakiyar Somaliya.

    Sai dai kungiyar ta ci gaba da kai hare-hare a kan gine-ginen gwamnati da kuma dakarun kungiyar haɗin kan Afirka.

    A mako da ya gabata, al-Shabab din ta kai hare-haren bama-bamai a garin Hiran da ke tsakiyar ƙasar.

  16. 'Yan Najeriya miliyan 25 na cikin barazanar faɗawa halin yunwa - Rahoto

    Food Risk

    Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa 'yan Najeriya miliyan 25 na cikin barazanar faɗawa halin yunwa tsakanin watan Yuni da kuma Agustan 2023 muddin ba a dauki matakin gaggawa ba.

    Rahoton wanda kungiyar Cadre Harmonisé ta fitar, wadda kungiya ce ta Majalisar Dinkin Duniya da ke taimakawa wajen samar da abinci mai gina jiki, ya nuna cewa ƙasar na ci gaba da fama da rikice-rikice da sauyin yanayi da kuma hauhawar farashin kayan abinci.

    A cewar wata sanarwa ta haɗin gwiwa da hukumar noma da samar da abinci da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya da hukumar bayar da agaji suka fitar, ta ce hakan ya nuna ƙaruwa a cikin mutane miliyan 17 da ke fama da matsalar ƙarancin abinci a yanzu.

    Sanarwar ta kuma lura cewa ayyukan 'yan ta-da-ƙayar-baya ya shafi aikin samar da abinci a yankin arewa maso gabas a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe da kuma matsalar ayyukan 'yan bindiga da garkuwa da mutane a Katsina da Sokoto da Kaduna da Benue da kuma Neja.

    Sanarwar ta ce Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta ruwaito cewa matsalar ambaliyar ruwa da aka samu a shekarar 2022, ya lalata kadada 676,000 na gonaki wanda kuma ya kawo raguwa a abin da mutane suka girba da janyo ƙaruwar barazanar matsalar ƙarancin abinci ga iyalai a faɗin Najeriya.

  17. 'Yan kasuwa a Afirka ta Kudu sun yi barazanar shigar da ƙarar gwamnati kan ƙarancin wutar lantarki

    SA

    Kungiyoyin 'yan kasuwa a Afirka ta Kudu sun yi barazanar shigar da ƙarar gwamnatin ƙasar saboda matsalar wutar lantarki da ake fuskanta a faɗin ƙasar.

    Sun bai wa gwamnati daga nan zuwa ranar Juma'a domin daidaita harkokin samar da wutar lantarki ko ta fuskanci hukuncin kotu.

    Kungiyoyin sun rubuta wata wasika zuwa ga ministan masana'antu Pravin Gordhan, inda suka ce hakkin gwamnati ne na samar da wutar lantarki ga jama'a.

    Mutane sun yi ta fuskantar ƙarancin wutar lantarki sama da shekaru goma saboda rashin iya gudanarwa da cin hanci da rashawa.

    A baya-bayan nan ma, ƙasar ta yi ta fama da ɗaukewar wutar lantarki na sama da sa'a goma a kowace rana.

    Matsalar ta sanya shugaban ƙasar katse ziyarar da yaso yi a birnin Davos don tattaunawa da 'yan kasuwa da kuma shugabannin kungiyoyin kwadago.

  18. Tattalin arzikin China ya samu tagomashi a shekarar bara

    Alkaluma daga hukumomi a China na nuna cewa tattalin arzikin kasar ya samu tagomashi a bara.

    Jumullar abin da China take samarwa GDP ya karu da kashi uku cikin 100 a 2022, kusan fiye da rabin abin da gwamnati ta so samarwa na sama da kashi biyar cikin 100.

    Masu sharhi sun ce kididdigar na nuna yadda tsauraran dokokin korona da kasar ta kakaba suka shafi harkokin kasuwanci. A watan da ya gabata ne kuma mahukuntan kasar suka janye dokokin.

  19. An sake buɗe makarantu a Malawi bayan ɓullar kwalera

    ..

    Daliban sakandare da firamare a Malawi za su koma makaranta a manyan biranen kasar biyu bayan da barkewar cutar kwalara ta kashe daruruwan mutane.

    Makarantu a Lilongwe, babban birnin kasar da kuma cibiyar kasuwanci, birnin Blantryre sun kasance a rufe na tsawon makonni biyu bayan hutun Kirstimeti.

    An fara samu barkewar annobar a karon farko a watan Maris cikin shekarar da ta gabata, kuma zuwa yanzu ta kasha fiye da mutum 750.

    Har yanzu akwai mutane da dama wadanda ke fama da cutar a biranen Lilongwe da Blantryre.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai-tsaye barkanmu da hantsin Talata.

    Ku kasance domin samun laraban abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya tare da Ahmad Tijjani Bawage

    Idan kun shirya ja mu je!