Gwamnatin Kaduna ta rushe otel ɗin da aka so yin dabdalar nuna tsiraici

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau.

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa a wannan shafin tun daga safiyar yau.

  2. Guinea ta fara gwajin allurar riga-kafin korona kan ministan tsaro na ƙasar

    Hukumomi a ƙasar Guinea, sun fara yin allurar riga-kafin korona ga mutanen ƙasar inda aka fara amfani da wadda ƙasar Rasha ta samar.

    Ministan tsaro na ƙasar, Mohamed Diane ne mutum na farko da aka fara yi wa riga-kafin Sputnik V ta ƙasar Rasha.

    Allurar mutum 60 kaɗai ƙasar ta samu a halin yanzu, inda a karon farko ake bayar da su ga jami'an gwamnati da wasu da suke aikin sa kai da suka haura shekara 60.

    Har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta yi ƙarin bayani ba kan ko za ta tsawaita wa'adinta na ci gaba da yin riga-kafin bayan gwajin

  3. An tasa ƙeyar waɗanda suka shirya da tallata dabdalar nuna tsiraici a Kaduna

    ..

    Ƴan sanda a Kaduna sun tasa ƙeyar waɗanda suka shirya gudanar da dabdalar nuna tsiraici a Kaduna da kuma waɗanda suka tallata dabdalar a shafukan sada zumunta.

    Gwamnatin Kaduna ta shaida wa BBC cewa za a gurfanar da waɗannan matasa a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

    .

    Ɗazu ne dai gwamnatin jihar ta je ta rushe har otel ɗin da aka yi niyyar gudanar da wannan dabdalar, inda gwamnatin ta zargin otel ɗin da saɓa dokokin korona

  4. Mahamadou Issoufou zai sauka cikin girma da mutunci ‒ Buhari

    ...

    Shugaban Najeriya Muhammaduj Buhari, ya jinjina wa Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou da al'ummar ƙasar kan gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da na ƴan majalisa cikin kwanciyar hankali.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan watsa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce "na ji daɗi matuƙa dangane da abin da nake ji da gani. Zan kira shi domin na yi masa murna. Issoufou zai sauka cikin girma da mutunci", in ji shugaban.

    Shugaban ya kuma bayyana haka ne yayin wata ziyara da tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Namadi Sambo ya kai masa a fadar shugaban da ke Abuja.

    .

    Namadi Sambo ne ya jagoranci tawagar Ƙungiyar ECOWAS zuwa Nijar domin sa ido kan zaɓen ƙasar.

  5. China ta amince da riga-kafin kamfanin Sinopharm

    ..

    Hukumomi a ƙasar China, sun amince da amfani da allurrar rigakafin cutar korona da kamfanin haɗa magugunan na ƙasar, Sinopharm ya kirkiro, ga jama’ar kasar.

    Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da kamfanin ya ce bincike ya nuna cewa allurar rigakafin na da ingancin kashi 76 bisa 100 a gwajin da aka yi kashi na uku, ba tare bayar cikakkun bayanai ba.

    Tuni aka fara amfani da alluran rigakafi da dama da aka sarrafa aka kuma yi gwaji a ƙasar China, bayan da aka amince da yi musu lasisin izini da gaggawa.

    Annobar ta ɓulla ne a tsakiyar birnin Wuhan na ƙasar ta China a cikin watan Disambar shekara ta 2019.

    Tuni da riga ta bazu a ƙasashen duniya, amma China ta yi kokarin rage kaifin yaduwarta ta hanyar ɗaukar matakai masu tsauri.

  6. Buhari zai yi wa ƴan Najeriya jawabin sabuwar shekara gobe Juma'a

    ...

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wa ƙasar jawabin sabuwar shekara a gobe ɗaya ga watan Janairun 2021.

    Mai taimaka wa shugaban kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce shugaban zai yi jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe.

    Malam Garba Shehu, ya buƙaci kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da su jona da gidan talabijin na ƙasar wato NTA da kuma gidan rediyo na tarayya FRCN domin su ma su yaɗa jawabin na shugaban kasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. An umarci jami'an ƴan sanda a Legas su tabbatar an bi dokokin korona a jihar

    ,,..

    Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya umarci duka kwamandojin yanki na faɗin jihar da su tabbatar da an bi dokokin da gwamnatin Najeriya da ta jihar Legas suka shimfiɗa na daƙile yaɗuwar annobar cutar korona.

    A cikin sanarwar, kwamishin ‘yan sandan ya bayyana dokokin da suka hada da amfani da takunkumin rufe fuska a wuraren taruwar jama’a, yin nesa da juna, da rufe daukacin gidajen dabdala, da gidajen shan barasa, har da wuraren shakatawa da wuraren bukukuwa da taruka.

    Sauran abubuwan sun haɗa da haramta bukukuwan kan titi, da tabbatar da amfani da na’urar gwajin zafin jiki, da amfani da sinadarin goge hannu, har da kafa dokar hana fita waje daga ƙarfe 12 na dare zuwa karfe huɗu na asuba.

    Kwamishinan ya kuma umarci kwamandojiin yankunan su tabbatar da cewa jami’ansu sun bi wannan doka, domin cutar korona gaskiya ce.

    Ya kuma gargaɗi jami’an da su tabbatar cewa ba su aikata abubuwan da za su zubar da kimar aikin ɗan sanda ba, kamar shaye-shaye, kuskuren harbi da kuma amfani da ƙarfin tuwo.

  8. Real Madrid ta fuskananci kalubale a hannun kananan kungiyoyi a 2020

    .

    Ranar Laraba Real Madrid ta buga wasanta na karshe a shekarar 2020, kuma karawar mako na 16 a gasar cin kofin La Liga ta Spaniya.

    Real din ta ziyarci Elche a karawar da suka tashi kunnen doki 1-1, wasan ya kara nuna kasa tabuka abin kirki da Real ke yi a duk lokacin da ta fuskanci karamar kungiya 2020.

    Karawar da Real ta tashi 1-1 da Elche ya kawo karshen wasa shida da Madrid ta ci a jere, kuma ta ci gaba da zama ta biyu a teburin La Liga biye da Atletico Madrid wadda take ta daya.

    Ga cikakken labarin a nan:

  9. Gwamnatin Kaduna ta rushe otel ɗin da aka so yin dabdalar nuna tsiraici

    .

    Gwamnatin jihar Kaduna ta rushe otel ɗin da aka yi niyyar gudanar da dabdalar nuna tsiraici a jihar.

    Mai taimaka wa gwamnan jihar Kaduna kan kafofin watsa labarai Abdallah Yunus Abdallah ya tabbatar wa BBC da faruwar rushe otel ɗin, inda ya ce an rushe Asher otel ne bayan bincike ya nuna cewa a wurin aka yi niyyar gudanar da dabdalar nuna tsiraici.

    .

    Ya kuma bayyana cewa otel ɗin wanda ke a Unguwar Barnawa, ya rinƙa saɓa dokokin da gwamnnatin jihar ta shimfiɗa na hana yaɗuwar korona, inda ko a kwanakin baya sai da gwamnan ya yi barazana mai ƙarfi ga wuraren da suka yi kunnen ƙashi.

    A makon nan ne dai an ƴan sanda a jihar suka damƙe matasan da suka yi niyyar gudanar da wannan dabdalar a jihar, inda a jikin goron gayyatar aka buƙaci mahalarta bikin su je wurin tsirara

    ..
  10. Mun ƙaddamar da hare-hare 50 a Syria cikin wannan shekara - Isra'ila

    Benjamin Netanyahu

    A wasu kalaman da ba ta cika yinsu ba, game da farmakin da take kaiwa a Syria, rundunar sojin Israila tace ta kaddamar da hare-hare guda 50 a Syria a cikin shekara guda da ta wuce.

    Gwamnatin Syria ta kan zargi Israila akai-akai da kai hare-haren sama a kan yankinta, amma yawanci Israilawan ba sa cewa komai game da rahotannin kai hare-haren.

    A yawancin lokuta sukan kai hari ne ga wuraren da ke da alaka da sojojin Iran, wadanda suke goyan bayan Shugaba Bashar al-Assad a yakin basasar Syriar.

    Israilawa dai na daukar kasancewar sojojin Israila a Syria a matsayin wata gagarumar barazana

  11. Yadda aka dama da matasa a zaben Jamhuriyyar Nijar

    Daya daga cikin abun da aka yi la'akari da shi bana a zaɓen jumhuriyar Nijar wannan karo shi ne fitowar matasa a fillin daga domin yin gogayya da waɗnda shekarunsu suka tura.

    Mahamane Nourou Harouna wanni matashi ne da ya shafe shekaru ya na turin motar siyasa amma a bana ya tsaya takarar kasila a jihar Maradi karakshin wata sabuwar jaim'iya da aka kira SDR Sabuwa.

    Ga kuma abun da ya shidawa Abdou Halilou.

    Bayanan sautiMahamane Nourou Harouna
  12. Paparoma na fama da rashin lafiya

    Paparoma Francis

    Fadar Vatican ta ce Paparoma Francis ba zai sami damar jagorantar addu'oin da aka saba yi jajiberin sabuwar shekara da kuma ranar farko ta sabuwar shekara ba, saboda rashin lafiya

    Wannnan shine karon farko a cikin shekaru da halin rashin lafiya zai tilasatawa Paparoma mai shekaru 80 rashin iya halartar Taron addu'oin.

    Fadar Vatican tace larurar da yake fama da ita na janyo masa matsanancin ciwo a kafarsa daya, a wasu lokutan ana ganin kuma wannan larura na shafar tafiyar Paparoma.

  13. Jami'an MDD za su fara shirin ficewa daga yankin Darfur

    UN

    A yau aikin kiyaye zaman lafiya na haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin Darfur na Sudan ke ƙarewa, bayan kimanin shekaru goma sha uku.

    Dama an tura dakarun ne domin kare farar hula da kuma taimaka wa wajen raba kayakin agaji, bayan da al'umomi da galibinsu ba Larabawa ba ne suka yi wa gwamnatin Sudan tawaye. '

    Wakiliyar BBC ta ce yanzu rundunar kiyaye zaman lafiya mai dakaru kusan dubu huɗu, tana da wa'adin watanni shida ta tattare ya nata-ya nata.

    A baya dai lokacin yaƙin an zargi dakarun gwamnati da abokan aikinsu galibi Larabawa da ake kira Janjaweed da aikata kisan ƙare dangi da kuma laifukan yaƙi a Darfur.

    An kashe mutane fiye da mutane dubu ɗari uku a yakin.

    Galibin ƙungiyoyin ƴan tawaye a yankin dai sun ƙulla yarjejeniyar sulhu da gwamnati a watan Oktoba.

  14. Iyayen yaran da aka sace a Kano sun yi zanga-zanga

    Iyayen yaran da aka sace
    Bayanan hoto, Iyayen yaran da aka sace

    Iyayen wasu yara fiye da 100 da suka nemi ƴaƴansu sama ko ƙasa suka rasa a jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zanga a safiyar yau Alhamis da zummar zaburar da hukumomi don ceto musu su.

    Sun riƙa daga hotunan ƴaƴan nasu, suna bayyana damuwa kan yadda suka ce gwamnatin jihar na nuna halin ko in kula game da aniyar ceto yaran bayan shafe tsawon lokaci ana nemansu ruwa a jallo.

    Su dai waɗannan iyaye na zargin cewa an sace yaran ne an yi kudancin kasar da su.

    A kwanakin baya ne hukumomi a jihar Kano suka bankaɗo yadda ake satar yara ƙanana ana kai su kudancin Najeriya tare da sauya musu addini da yare.

    Ga hotunan yadda zanga-zangar ta kasance

    Iyayen yaran da aka sace
    Bayanan hoto, Iyayen yaran da aka sace
    Hotunan yaran da aka sace
    Bayanan hoto, Hotunan yaran da aka sace
  15. Labarai da dumi-dumi, Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2021

    Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2021.

    Hakan na nufin kasafin wanda ya kai Naira Triliyan 13 ya zama doka, kuma za a fara aiwatar da shi a hukumance.

    Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai na ƙasa Femi Gbajabiamila ne suka gabatarwa shugaban kasafin kuɗin bayan amincewa da shi da majalisar dokoki ta yi.

    Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osibanjo da ministar kudi Zainab Shamsuna, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun halarci sanya hannun, kamar yadda yake kunshe cikin wani hoto da mai taimakawa shugaban ƙasar na musamman kan kafafen sadarwar zamani.Bashir Ahmad ya wallafa a tuwita.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Buhari ne Ummul-haba'isin matsalolin Najeriya - PRP

    PRP

    Jam’iyyar PRP ta yi kira ga‘ yan Nijeriya da su ɗora alhakin dukkanin matsalolin da suka addabi Najeriya kan shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC.

    Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Falalu Bello, wanda ya bayyana hakan a sakonsa na sabuwar shekara ga ƴan Najeriya, ya ce gwamnatin APC ta kasa magance kalubalen tsaro, da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar da kuma yadda ake ci gaba samun ƙaruwar matsalar garkuwa da mutane.

    A cewarsa, yayin da suke fatan samun sauki a shekarar 2021, ƴan Najeriya ba za su iya mantawa da tafiyar hawainiya da wahala da nadamar da gwamnatin Shugaba Buhari da jam'iyyarsa ta APC suka jawowa ƴan Najeriya ba.

    “Abin takaici ne matuƙa cewa maimakon magance ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta da kuma tsara hanyoyin ci gaba, gwamnatin APC na ta yin wasan zargi'', kamar yadda Daily Trust ta rawaito shi yana fada.

  17. Yau Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2021

    Buhari

    Nan gaba a yau Alhamis ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai rattaba hannu kan dokar kasafin kudi ta shekarar 2021 da Majalisar Dokoki ta amince da shi.

    Mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan ga Daily Trust.

    Wasu daga cikin waɗanda ake sa ran za su albarkaci sanya hannun sun haɗar da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da wasu manyan yan majalisa.

    Sannan akwai wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta kasar (FEC) da ake sa ran za su halarci bikin sanya hannun, da suka hadar da Ministar Kudi Hajiya Zainab Ahmed, Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Clement Agba, da Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN) wato Godwin Emefiele, da Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi Ben Akabueze da sauransu.

  18. Likitan da aka yi wa rigakafin korona ya kamu da cutar

    Likita

    Wani ma'aikacin jinya a jihar Carlifonia dake Amurka ya kamu da cutar korona fiye da mako guda bayan karɓar rigakafin Pfizer.

    Wannan lamari ya sa tuni kamfanin da ya samar da rigakafin ya ce "zai yi bitar duk bayanan da ake da su a kan lamari kawo yanzu''.

    Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce "Mutane na iya kamuwa da cutar kafin ko bayan rigakafin musamman wanaki 10 na farko bayan yi musu, wanda a wannan lokaci ne rigakafin ke ginuwa a jikin mutum".

    Matthew W., mai shekaru 45, wani ma'aikacin jinya ne da ke aiki a wasu kananan asbitoci biyu, kuma ya fada a wani sakon da ya wallafa a Facebook a ranar 18 ga watan Disamba cewa ya karbi allurar rigakafin ta Pfizer, amma hannunsa ya dan masa ciwo na wuni guda, bayan hakan ba ta da wata illa.

  19. Ƴan hamayya a Afrika ta tsakiya na neman a soke zaɓukan ƙasar

    CAR

    Ƴan hamayya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun yi tir da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisu da aka yi a ranar 27 ga Disamba tare da yin kira da a soke su, ci gaban da ake ganin zai kara tayar da jijiyoyin wuya a ƙasar.

    Haɗin gwiwar ƴan adawar da ke kiran kansu da (COD-2020) sun ce babu adalci cikin zaben, saboda yadda aka hana jama'a da dama shiga jefa ƙuri'a.

    A farkon wannan makon, Ministan cikin gida na ƙasar Augustin Yangana-Yahote ya ce ba a yi zaɓen a cikin 29 daga cikin ƙananan hukumomin ƙasar ba, saboda matsalar tsaro.

    Daga baya hukumar zaɓen ta ce ba a buɗe kimanin rumfunan zaɓe 800 daga cikin 5,408 da ake da su a ƙasar ba, saboda dalilan tsaro.

    Ƙawancen ya haɗa manyan ƴan siyasar adawa ciki har da ƴan takarar shugaban ƙasa biyar da tsohon shugaban ƙasar Francois Bozize wanda aka hana shi tsayawa takara.

    Gwamnatin Shugaba Faustin Archange Touadera ta zargi Bozize da aiki tare da ƴan tawaye da ke iko da wasu sassan ƙasar don kifar da gwamnati.

  20. Korona ta kashe fiye da Amurkawa 4000 a rana guda

    Korona

    Amurka ta kafa sabon tarihi game da adadin waɗanda suka mutu sanadiyyar cutar Korona a rana guda, inda mutane fiye da dubu uku da dari tara suka mutu.

    Jami'ar Johns Hopkins wadda ke tattara alƙaluman annobar na Amurka, ita ce ta bayar da adadin mace-macen na sa'o'i ashirin da hudu da suka gabata.

    Jihar Carlifornia ta zama jiha ta biyu da ta tabbatar da ɓullar sabon nau'in cutar mai saurin yaduwa, wanda aka fara ganowa a Birtaniya.