An ci tarar gidajen talabijin na Channels, AIT, Arise kan zanga-zangar EndSARS

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a yau Litinin 26 ga watan Oktoban 2020.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    Masu bibiyarmu nan muka zo ƙarshen rahotannin kai-tsaye a wannan shafi.

    Kuna iya dubawa ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa a yau Litinin kafin mu sake haɗuwa gobe idan Allah Ya kai mu.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. An kashe mutane da dama a harin da Rasha ta kai Syria

    Syria

    Mayaƙan da ke samun goyon bayan Turkiyya da dama aka kashe sanadin wani hari ta sama da Rasha ta kai kan sansaninsu a Lardin Idlib da ke hannun 'yan tawaye.

    Ƙungiyar Faylaq al-Sham na ɗaya daga cikin ɓangare mafi karfi da Turkiyya ke goyon baya a Syria kuma tana daga cikin kungiyar ƙawance ta National Front for Liberation.

    A martanin da ta mayar, mayakan sa kai na ƙungiyar NFL sun kai hari kan sansanonin sojojin Shugaba Assad.

    Rasha ta shiga tsakani tare da sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Idlib amma ana ci gaba da samun rikici tsakanin Turkiyya da Syria.

    Hakan ya biyo bayan tsoma bakin da Turkiyya ta yi kan rikicin yankin Nagorno Karabakh, wanda rahotanni ke cewa ta tura mayaka daga Syria.

  3. Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin bunƙasa rayuwar matasa

    Osinbajo

    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa wani kwamitin gwamnoni da zai saurara tare da biyan buƙatun matasan ƙasar biyo bayan zanga-zangar da aka shafe makonni ana yi.

    Matakin nasu ya biyo bayan taron da Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa ta yi ne a yau Litinin, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

    Mambobin kwamitin sun ƙunshi gwamnoni shida da aka zaɓo daga shiyya shida na ƙasar, ƙarƙashin shugabancin Osinbajo.

    Kwamitin zai fara aiki nan take, a cewar fadar shugaban ƙasa, kuma zai lalubo hanyoyin kyautata rayuwar matasa tare da ƙara kyautata tsaron ƙasa ta hanyar yin aiki da gwamnatocin jihohi da kuma ƙungiyoyin farar hula.

    Mambobin kwamitin:

    • Gwamnan Jihar Sokoto - Arewa maso Yamma
    • Gwamnan Jihar Borno - Arewa maso Gabas
    • Gwamnan Jihar Neja - Arewa ta Tsakiya
    • Gwamnan Jihar Ondo - Kudu maso Yamma
    • Gwamnan Jihar Ebonyi - Kudu maso Gabas
    • Gwamnan Jihar Delta - Kudu maso Kudu
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Kaduna: An sassauta dokar hana fita amma ban da Kaduna ta Kudu da Chikun

    Kaduna

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da aka saka domin daƙile yunƙurin masu wawashe kayan abinci a ƙaramar hukuma 21 na jihar.

    Sai dai dokar na nan daram ta awa 24 a ƙananan hukumomin Kaduna ta Kudu da kuma Chikun.

    Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya faɗa cikin wata sanarwa a yau Litinin cewa, dokar za ta fara aiki ne gobe Talata daga 4:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.

    Aruwan ya ce sun ɗauki matakin ne biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaron jihar suka bai wa gwamnati.

    Sai dai ya ce an ƙi sassauta dokar a Kaduna ta Kudu da Chikun saboda har yanzu masu satar kayan abincin ba su daina ba, saboda haka ne ya shawarci mazauna yankunan da su zauna a gida.

    "Dukkanin wuraren kasuwanci da wuraren cin abinci da otel-otel za su kasance a rufe a waɗannan yankunan. Taron jama'a shi ma haramun ne har sai baba ta gani," in ji sanarwar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Mata na zanga-zanga kan kisan yara a Kamaru

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama ku saurari rahoton Mahamman Babalala daga Kamarun

    Mata sun fito a birnin Yawundi suna zanga-zanga kan adawa da ci gaba da kisan yara a yankin renon ingilishi na Kamaru.

    Zanga-zangar na zuwa bayan kisan yara bakwai a wata makaranta mai zaman kanta a Kumba a yankin na kudu maso yammaci.

    Matan sun fito sanye da bakin tufafi da kwalayen da ke dauke bayanin nuna fushinsu kan kashe-kashen.

    Gwamnati da ƴan awaren kamaru na zargin juna kan harin.

    An shafe kwanaki shekara hudu ƴan aware na rikicin neman ɓallewa daga Kamaru, kusan

    3,000 aka kashe tare da tursasa dubbai barin gidajensu.

  6. An ci tarar gidajen talabijin na Channels, AIT, Arise kan zanga-zangar EndSARS

    NBC

    Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta NBC a Najeriya ta ci tarar gidajen talabijin na Channels da AIT da Arise game yadda suka yi rahotanni kan zanga-zangar EndSars.

    Muƙaddashin daraktan hukumar Farfesa Armstrong Idachaba, shi ne ya bayar da sanarwar tarar a yau Litinin a Abuja, inda ya ce za su biya tarar naira miliyan uku kowannensu.

    An yaɗa hotuna da bidiyo na boge a tsakanin mako biyu da aka shafe ana zanga-zangar nuna ɓacin rai game da ayyukan rundunar 'yan sanda a Najeriya, wadda aka yi wa laƙabi da EndSars - wato a rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami.

    BBC ta bincika tare da bankaɗo gaskiya da ƙaryar wasu daga cikinsu a wannan labarin.

    An ci tarar gidajen talabijin ɗin uku ne saboda "yaɗa hotunan da ba a tantance ba na harbe-harben da ake zargin an yi".

    Tun a baya, NBC ta gargaɗi kafofin yaɗa labarai da su yi taka-tsantsan wurin yaɗa hotunan da suka samu daga shafukan sada zumunta, tana mai cewa rashin tantance sahihancinsu ka iya jawo hatsaniya a ƙasa baki ɗaya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Pogba zai kai jaridar Sun kotu kan rahoton cewar zai bar buga wa Faransa wasa

    Pogba

    Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba ya ce zai dauki matakin shari'a, bayan "tsagwaron karya" da wani rahoto cewar ya bar buga wa tawagar Faransa tamaula.

    An bayar da rahoton cewar Pogba mai shekara 27, zai bar buga wa tawagar kwallon kafa ta Faransa tamaula saboda wasu kalamai da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi kan Musulunci.

    Dan wasan da ke da ya lashe Kofin Duniya wanda kuma Musulmi ne, ya ci wa tawagar Faransa kwallo 10 a wasa 72 da ya buga mata.

  8. Abin da kuke son sani game da wasan Juventus vs Barcelona

    Ronaldo da Messi

    Barcelona za ta buga wasa na biyu a cikin rukuni na bakwai, inda za ta ziyarci Juventus a gasar Champions League ranar Laraba.

    Ana sa ran za a fafata tsakanin Cristiano Ronaldo da Messi ranar Laraba, amma babu tabbas game da yiwuwar hakan bayan Ronaldo ya killace kansa sakamakon kamuwa da cutar korona.

    Juventus tana da kofin Champions League biyu, inda Barcelona ta lashe shi sau biyar a tarihi.

    Kungiyoyin biyu sun fafata a tsakaninsu sau 13, inda Barcelona ta ci wasa hudu, Juventus ta yi nasara sau biyar da canjaras hudu.

  9. Ba ɓoye kayan tallafin korona muka yi ba - Gwamnonin Najeriya

    Gwamnonin Najeriya

    Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ta musanta zargin da ake yi musu cewa ɓoye kayan tallafin annobar korona suka yi, waɗanda aka tanada domin agaza wa mabuƙata.

    Maganar tasu na zuwa ne bayan dubban matasa sun ɓalle rumbun kayan abinci a jihohi daban-danban suna yashe dukkanin abin da suka tarar - ciki har da magunguna da injinan lantarki da kekunan ɗinki.

    Cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin ƙungiyar na intanet a yau Litinin, gwamnonin sun ce batun cewa ɓoye kayan suka yi "ba gaskiya ba ne".

    "Abin da ake yaɗawa cewa waɗannan kayan tallafi ɓoye su muka yi ba wai ƙarya ba ce kawai, kuskure ne babba kuma bi ta da ƙulli ne," in ji gwamnonin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa wasu gwamnonin sun ajiye kayan ne cikin shirin ko za a shiga karo na biyu na ɓarkewar cutar ta korona a Najeriya.

    Har zuwa 'yan makonnin da suka gabata, ana bai wa wasu jihohin kayan tallafin daga Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma'aikatar Agaji, Cigaban Al'umma da Kiyaye Afkuwar Bala'i.

  10. Cutar korona na ci gaba da barazana ga nahiyar Turai

    BBC

    An sa sabbin dokokin kulle da tuni suka fara aiki a kasashen Turai sakamakon karuwar masu fama da cutar korona a akasarin yankunan nahiyar.

    An sa dokar hana fita a fadin Spaniya.

    A Italiya kuma, an rufe wuraren motsa jiki da gidajen silima sannan za a rufe wuraren cin abinci da wuraren shan barasa amma ban da tsarin sayi ka tafi ko na kai wa mutum abinci har gida.

    A Belgium ma an rufe wuraren motsa jiki sannan dole ne shaguna su rufe karfe takwas na dare.

    A yanzu sa takunkumi a Belgium din ya zama dole a wuraren taron jama'a kamar yadda yake a Croatia inda hukumomi suka sa dokar haramta zuwa kallon wasanni na tswon mako biyu.

  11. Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi kira a daina sayan kayan kasar Faransa

    getty

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira kan jama'ar kasar su kauracewa kayayyakin Faransa.

    Ya kuma yi kira ga Tarayyar Turai ta kawo karshen abin da ya kira wata manufar Faransa ta kyamar musulunci.

    Alama ce ta tsamin dangantaka inda Shugaba Macron wanda ya kare kasarsa tun bayan da wani mai kishin addinin musulunci ya fille kan wani malamin makaranta a watan da ya gabata saboda nunawa dalibansa zanen Annabi Muhd SAW.

    A makon da ya gabata, Erdogan ya bukaci Macron ya yi gwajin kwakwalwa saboda yadda yake kallon addinin musulunci. Tuni dai Faransa ta janye jakadanta daga Turkiyya.

  12. An kashe mayaƙan Taliban a Afghanistan

    BBC

    Sojojin Amurka a Afghanistan sun ce sun ƙaddamar da wani hari kan 'yan Taliban a tsakiyar Lardin Wardak da yammacin jiya Lahadi.

    Mai Magana da yawun sojin ya ce harin ya halaka mayaƙan Taliban biyar.

    Dakarun Amurka a Afghanistan sun daina kai hare-hare kan wuraren Taliban sakamakon wata yarjejeniya da aka cimma da mayaƙan cikin watan Fabrairun bana.

    Amma sojin sun ce an dauki matakin domin kare sojojin Afghanistan.

    A farkon watan nan ne ƙungiyar Taliban din ta zargi Amurka da saɓa yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare kan mayakanta da ke Lardin Helmand – zargin da Amurkan ta musanta.

  13. Mata na zanga-zanga kan kisan yara a Kamaru

    Mata sun fito a birnin Yawundi suna zanga-zanga kan adawa da ci gaba da kisan yara a yankin renon ingilishi na Kamaru.

    Zanga-zangar na zuwa bayan kisan yara bakwai a wata makaranta mai zaman kanta a Kumba a yankin na kudu maso yammaci.

    Matan sun fito sanye da bakin tufafi da kwalayen da ke dauke bayanin nuna fushinsu kan kashe-kashen.

    Gwamnati da ƴan awaren kamaru na zargin juna kan harin.

    An shafe kwanaki shekara hudu ƴan aware na rikicin neman ɓallewa daga Kamaru, kusan

    3,000 aka kashe tare da tursasa dubbai barin gidajensu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Yajin aikin gama gari a Belarus na ƙara tada ƙura

    Getty

    Kiran da ‘yan hamayya suka yi na a shiga yajin aikin gama gari a Belarus ya janyo ma'aikata yi wa masana'antun gwamnati kawanya da kuma dalibai da suka yi zaman dirshan a jami’o’in kasar, a kokarin ganin an hambarar da gwamnatin Alexander Lukashenko.

    Ma'aikatan da ke yajin aiki sun yi ta rera wakoki a wajen masana'anta sai dai ba a samu fitowar jama'a sosai ba.

    Gwamnatin Belarus din ta dage cewa komai yana tafiya dai-dai a dukkanin masana'antunta.

    Jami'an tsaro kuma na ta tsare masu yajin aikin da kuma mutanen da suke zanga-zanga.

    Wata kungiyar kare hakkin bil adama ta ce sama da mutane dari da ashirin aka kama, yayin da jagorar 'yan hamayya a kasar Svetlana Tikhanovskaya ta yi kira ga masu kananan sana'oi su shiga yajin aikin.

    epa
  15. An fasa rumbun ajiyar abinci da ke Gwagwalada a Abuja

    Others

    An fasa rumbun ɗakin ajiyar abinci na gwamnati da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin Najeriya.

    Cikin wadanda aka ga hotunansu suna kwasar kayan da akwai tsofaffin mutane da kuma matasa maza da mata da ke ikirarin kayan hakkokiinsu ne.

    Mutane hudu ne suka faɗi yayin turmutsutsu kamar yadda rahotanni suka ruwaito, kuma masu kwasar kayan sun yi tsa tsallakawa ne ta shingen ginin da aka kafa domin kwaso ganima.

    Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun ruwaito cewa cikin kayan da aka wawashe akwai taliya da indomi da gishiri da shinkafa da sikari wandanda aka ce mallakar hukumomin birnin tarayyar ne.

    Tuni dai sojoji suka dira wurin da ake sace-sacen sai dai masu kwasar kayan ba su bar aikin da suke yi ba.

  16. 'Yan sanda sun fara bincike kan rikicin siyasar Ghana

    Getty

    Jami'an 'yan snda a Ghana sun fara bincike kan wani rikici da ya ɓarke tsakanin magoya bayan jam'iyya mai mulki ta NPP da kuma babbar jam'iyyar adawa ta NDC.

    Mutane da dama sun jikkata yayin wannan rikici tare da tayar da hankalin jami'an tsaro gabanin zaben ƙasar a Disamba.

    An tsara haɗuwar bangarorin biyu ne da nufin tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu a Accra sai kuma ta rikiɗe ta koma rigima.

    Babu dai wani takamaiman abin da ya janyo wannan rikici, sa dai hoton bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ɓangarorin ke ta jifan juna da duwatsu da kwalabe da sauran abubuwa.

    Wasu da suka ga faruwar lamarin sun ce an ta jin ƙarar harbin bindiga.

    'Yan sanda sun ce an samu kwanciyar hankali a yankin da rikicin ya faru kuma suna ci gaba da neman mutanen da suka assasa rikicin.

  17. Ahmed Musa ya bar ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya

    g

    Dan wasan Najeriya Ahmad Musa ya bar ƙungiyar Najd Knight bayan kwashe shekara biyu da kulob din da ya lashe gasar Saudiyya sau takwas.

    Kungiyar ta bayyana tafiyar dan wasan ne a shafinta Twitter.

    Musa mai shekara 28 yanzu ba shi da wata ƙungiya sai dai rahotanni na cewa yana son koma wa Turai ne da taka leda bayan barin ƙungiyar cikin ruwan sanyi.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa, ƙungiyar ta haɗa wani hoton bidiyo tun daga farkon zuwansa har da ƙwallayen da ya jefa, tare da yi masa fatan alheri a rayuwar ƙwallonsa a nan gaba.

    Cikin wasa 58 da ya bugawa ƙungiyar, ya samu nasarar jefa ƙwallo 11 da kuma bayar da 14 aka ci, ya kuma taimaka wa ƙungiyar ta ɗauki kofin gasar ƙasar da kuma Super Cup ɗinta.

    Yanzu dai ana sanya ido domin jin inda ɗan wasan zai nufa a rayuwarsa ta gaba a ƙwallon kafa.

  18. Sojoji na bincike gida-gida don neman kayan da aka sace a Calabar

    BBC

    Sojoji na bincike gida-gida domin neman kayan da aka sace a Calabar, bayan mazauna jihar sun wawashe kayan gwamnati da na daidaikun 'yan kasuwa a karshen sati.

    Rahotanni na cewa yayin wannann rikicin, gwamnan jihar Ben Ayade ya fice daga jihar zuwa Abuja domin naiman taimakon gwamnatin tarayya.

    An lalata dukiya mai matukar yawa, " wanda zai lakume akalla naira biliyan takwas domin gyara Yankin Tinapa da aka kirkira domin kasuwanci," in ji gwamna Ayade.

    Shugaban harkokin yaɗa labaran gwamnan ya shaida wa BBC cewa al'amura sun koma yadda suke a jihar, yana mai cewa ba a samu rahoton wanda ya rasa ransa ba a yayin sace-sace.

    Tun ranar Juma'a 23 ga watan Oktoba gwamnan ya sanar da dokar kulle a fadin jihar, domin tabbar da komi ya koma daidai, tare da kare dukiyoyin jama'a.

  19. An amince da sauya kundin tsarin mulkin Chile

    Reuters

    Rahotanni daga Chile na cewa sakamakon kuri'ar raba gardama da a ka jefa kan bukatar sauya kundin tsarin mulki ya nuna amincewar 'yan kasar kan haka.

    Kawo yanzu kashi 78 na kuri'un sun nuna amincewa da sabon daftarin.

    Shugaba Sebastian Pinera ya jinjinawa 'yan kasar kan yin zaben cikin lumana.

    Ya kuma ce sabon kundin tsarin mulkin zai kunshi muradun dimokradiyya da yan kasar ke fata. 'Yan Chile na neman sauyi a harkar ilimi da lafiya da fansho da kuma abin da ya shafi mallakar gidaje.

  20. An kama ɗaruruwan mutane a zanga-zangar da ake yi a Angola

    Getty

    Aƙalla mutum 100 ne aka kama a zanga-zangar kin jinin gwamnati da ake yi a Luanda babban birnin Angola.

    Masu zanga-zangar na neman a fitar da sabon kwanan watan zaɓen ƙananan hukumomin kasar wanda aka tsarayi a wannan shekarar a baya, amma aka samu jinkiri gudanarwa sakamakon annobar korona, da kuma buƙatar samar da ayyukan yi da rayuwa mai kyau.

    Ministan cikin gidn kasar Salvador Rodrigues ya shaida wa gidan talabijin na ƙasar cewa ana tsare da mutum 103.

    Ya kuma ce akwai shugabannin jam'iyyun siyasa cikin wadanda aka kaman.

    Hukumomin ƙasar sun ce masu zang-zangar na jefe-jefe da duwatsu, da kona tayoyi da kuma ɓata abubuwan amfani.

    Getty

    Masu zanga-zangar sun yi shinge ta hanyar sanya wuta tsakaninsu da jami'an tsaro.

    getty
    Getty

    A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, babbar jam'iyyar adawa ta Unita, ta zargi 'yan sanda da amfani da ƙarfin da yawuce iyaka tare da neman a saki duka mutanen da aka kama ba tare da wani sharadi ba.