Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 22/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 22/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. An sake dage taron yakin neman zaben Atiku Abubakar na Kaduna

    Jam'iyyar ADC ta sanar da dage taron yakin neman zaben dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba a jihar Kaduna.

    A cikin wata sanarwa da Sanata Adamu Usman ya fitar, ya ce an yanke shawarar dage taron ne bayan nazari mai zurfi da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsakin jam'iyyar a jihar.

    Sanata Adamu Usman ya ce za a sanar da sabuwar ranar gudanar da taron cikin kankanin lokaci.

    Ya kuma bayyana godiyarsa ga mambobin jam'iyyar, magoya bayanta da sauran masu fatan alheri bisa hakuri, fahimta da ci gaba da goyon bayan da suke bai wa jam'iyyar a jihar Kaduna da ma wajenta.

    Sanarwar ta kara da cewa jam'iyyar na godiya ga daukacin magoya bayanta bisa fahimtar wannan mataki.

  2. Aƙalla mutum ɗaya ya mutu sakamakon harin Rasha a Ukraine

    Aƙalla mutum guda ne ya mutu bayan wani harin da Rasha ta kai kan wani ginin gidaje da ke arewacin birnin Kyiv, babban birnin Ukraine, inda har yanzu ana ci gaba da neman wasu mazauna yankin da suka bace.

    An kai harin ne kan wani ginin bene mai hawa biyar a garin Dymer, lamarin da ya sa wani bangare na ginin ya ruguje, a yayin hare-haren dare da aka kai a wurare da dama.

    Tun da farko, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce akwai yiwuwar mutane goma sha huɗu har yanzu suna makale a ƙarƙashin baraguzan ginin.

    Jami’an Ukraine sun kuma ce Rasha ta kai hari kan wata tashar rarraba wutar lantarki a yankin Dnipropetrovsk.

    A birnin tashar ruwa na Odesa da ke kudancin kasar, hukumomi sun sanar da cewa makarantu za su koma koyarwa ta yanar gizo, bayan hare-haren Rasha sun lalata hanyoyin samar da makamashi, lamarin da ya haddasa matsaloli masu tsanani ga samar da dumama gidaje, wutar lantarki da kuma ruwan sha.

  3. Muna da makamai masu linzami masu cin zango fiye da kilomita 2,000 - Iran

    Qasem Qureshi, mataimakin shugaban dakarun Basij, ya bayyana a gefen wani biki da aka gudanar a Tehran cewa makaman Iran masu linzami suna iya cin zango da ya wuce kilomita 2,000.

    Malam Qureshi ya ce: "Ba zan iya bayyana ainihin zangon waɗannan makamai masu linzami ba. Amma abin da Jagora ya faɗa dangane da nisan da karfin makamai da kayan aikinmu ya tabbata kuma an aiwatar da shi."

    Ya kuma shaida wa kamfanin dillancin labarai na Fars cewa Iran tana da wani shiri na kauce wa duk wani killacewa ko takunkumin ruwa da za a ƙaƙaba mata. Sai dai bai yi ƙarin haske kan cikakkun bayanan wannan shirin ba.

  4. An kai hare-haren jirage marasa matuƙa a wuraren zama a Khartoum

    Jiragen yaƙi marasa matuƙa sun kai hare-hare kan unguwannin zama a birnin Khartoum, babban birnin Sudan.

    Shaidun gani da ido sun ce hare-haren sun lalata gidaje, yayin da mutane ke ƙoƙarin ceto ƴanuwansu da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da suka ruguje.

    Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ayyukan jin ƙai a Sudan ya ce wasu gine-ginen Majalisar Ɗinkin Duniya sun samu matsala sakamakon hare-haren, duk da cewa ma’aikata na ciki a lokacin da lamarin ya faru.

    A cikin wata sanarwa, MDD ta ce ginin yana cikin yankin fararen hula, tare da jaddada cewa bai kamata a kai farmaki kan fararen hula ba a lokacin yaƙi.

    Birnin Khartoum na ƙarƙashin ikon rundunar sojin Sudan, wadda ke faɗa da dakarun Rapid Support Forces (RSF) tun daga watan Afrilun shekara ta 2023.

    MDD ta sha yin suka ga ɓangarorin biyu kan amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa, waɗanda suka yi sanadin mutuwar fiye da mutum dubu ɗaya a watanni shida na farkon wannan shekara.

  5. Amnesty ta bukaci a yi bincike kan bidiyon zargin ‘cin zarafi’ da ya shafi Sarkin Daura

    Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin cin zarafin wata mata 'yar kasar waje da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, mai shekaru 92.

    Sanarwar Amnesty ta nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Nuwamba, lokacin da matar ke rangadin ziyara a fadar Sarkin Daura da ke jihar Katsina.

    Amnesty ta ce faifan bidiyo da matar ta wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda sarkin ya yi ta kokarin cin zarafinta, duk da yadda take nuna rashin amincewarta.

    Kungiyar ta ce matar ta zargi sarkin da taba jikinta ta hanyoyi daban-daban da ba su dace ba.

    Amnesty International ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi, tare da bukatar gwamnatin jihar Katsina da rundunar 'yan sandan Najeriya su gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya domin tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifi.

    Kungiyar ta ce wannan lamari wata dama ce ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa babu wanda ya fi karfin doka a kasar, komai matsayinsa a cikin al'umma.

  6. NAFDAC ta lalata jabu da haramtattun kayayyaki na naira biliyan 100

    Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta lalata magunguna da kayayyakin jabu, waɗanda suka hada da haramtattu, waɗanda wa’adinsu ya kare da kuma marasa rajista, da darajarsu ta kai kimanin naira biliyan 100 a jihar Ogun.

    An gudanar da aikin lalata kayayyakin ne a wurin zubar da shara na Ogwama da ke Ogere Remo, a wani mataki na hana irin waɗannan kayayyaki masu hadari komawa kasuwannin Najeriya, kamar yadda shafin intanet na Chanels ya ruwaito.

    Babbar Daraktar-Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce kayayyakin da aka lalata sun haɗa da magungunan da aka haramta ko ba a yi musu rajista ba, giya na leda da ƙananan kwalabe, allurar Analgin da aka haramta, magungunan tari masu ɗauke da codeine da wa’adinsu ya ƙare, allurar Oxytocin, kayan kwalliya na jabu da kuma wasu kayan abinci marasa inganci.

    Ta bayyana cewa an ƙwato kayayyakin ne a yayin samame da sintiri da jami’an NAFDAC suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar, tare da wasu da kamfanoni suka miƙa da kansu da kuma waɗanda Hukumar Kwastam ta Najeriya ta damƙa wa NAFDAC.

    Adeyeye ta kuma ce jami’an hukumar sun gano wasu wuraren da ake samar da kayan kwalliya da magunguna ba bisa ƙa’ida ba a Legas, da kuma wuraren da ake haɗa giya na bogi.

  7. Myanmar ta kama masu damfara da sunan tilasta shiga aikin soja

    Gwamnatin Myanmar ta ce ta ɗauki matakin shari’a kan mutane da dama da ake zargi da karɓar kuɗaɗe ta hanyar damfara da kuma tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba, musamman maza da ke ƙoƙarin gujewa shiga aikin soja na dole.

    Wannan na daga cikin ƙalilan da hukumomin ƙasar suka amince a fili da samun cin hanci da rashawa da kuma anfani da tsarin ɗaukar sojoji ta hanyar da ba ta dace ba.

    Ma’aikatar Tsaron Myanmar ta ce an dauki matakin shari’a kan fiye da mutane dari guda a kan abin da ta kira laifukan karbar kudade ta hanyar damfara, sannan kusan mutum dari guda kuma na fuskantar zargin tilasta daukar mutane aikin soja ba tare da izini ba.

    Hukumomin yankuna ma sun kasance suna karbar kudade domin samar da masu maye gurbin wadanda ke kokarin kauce wa aikin soja.

    Sojojin Myanmar na ci gaba da yaki da kungiyoyin masu goyon bayan dimokuradiyya da kuma wasu kungiyoyin kabilu masu dauke da makamai tun bayan juyin mulkin soji da ya faru a shekarar 2021, wanda ya jefa kasar cikin yakin basasa mai tsanani.

  8. Ko ya kamata Musulmi ya dogara da AI wajen neman fatawa ta addini?

    "Ka ji tsoron Allah. Idan ka bi fatawar da ba daidai ba da wani malami ya bayar, ba ka da laifi. Amma idan ka bi ƙirƙirarriyar basira, to kai ne ke da laifi - kuma Allah zai yi maka hisabi."

    Wani rikicin ya ɓarke a kafafen sada zumunta a kan AI ya riƙa zartar da hukunci kan mas'alolin addini, inda miliyoyin mutane suka riga suka kalli wani bidiyo na ƙaddamar Qaf, wani ƙirƙirarren basira na musulunci, "wanda aka tsara don taimaka wa Musulmi wajen samun ilimi, da nazari a kan rayuwarsu, da kuma yin tambayoyi" game da Musulunci.

  9. Ƴanbindiga sun kashe mutum 11 ciki har da Dagaci da ƙananan yara a Neja

    Wasu ƴanbindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari wani ƙauye a tsakiyar Najeriya da sanyin safiyar Asabar, inda suka kashe mutum 11 ciki har da ƙananan yara. Harin ya janyo ramuwar gayya mai muni a kan wani matsugunin makiyaya Fulani da ke kusa.

    Rahoton tsaro da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani ya ce wasu ƴanbindiga masu ɗauke da makamai sun kutsa cikin ƙauyen Luman Ba'are da ke ƙaramar hukumar Borgu da misalin ƙarfe 6:00 na safe, a daidai lokacin da mazauna garin ke shirin tafiya sallar asuba.

    Rahoton ya ce an kashe mutum 11, ciki har da yara ƴan ƙasa da shekara biyar da kuma dagacin ƙauyen. Wasu daga cikin waɗanda aka kashe sun rasu ne a cikin masallacin ƙauyen, wanda mazaunan ƙabilar Kambari ke zaune a cikinsa.

    Rahoton ya kuma ce an yi garkuwa da wasu mazauna ƙauyen da dama tare da tafiya da su zuwa wuraren da ba a sani ba, sannan an kwashe shanu tare da ƙona gidaje, shaguna da babura da dama.

    Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Usman ya shaida wa AFP cewa, "An jefa gawar dagacin ƙauyen cikin wutar da ake ƙona gidaje."

    Ƴansanda sun tabbatar da aukuwar harin, sai dai sun ce mutum biyar ne suka mutu.

    Bayan harin, wasu jami'an tsaron sa-kai daga Ƙauyen sun kai hare-haren ramuwar gayya kan matsugunan Fulani da ke maƘwabtaka da su a Wawa da Gadi Oli, a cewar wani ma'aikacin agaji da ya yi magana da AFP.

    "Lokacin da sojoji daga sansanin da ke kusa suka isa wurin, tuni lamarin ya yi muni," in ji ma'aikacin agajin.

    Jami'an tsaron sa-kan sun zargi mazauna Fulani da sanin waƊanda suka kai harin amma suka gaza taimakawa wajen daƙile shi.

  10. Abinci uku da ke ƙara ƙarfin ƙashi a jikin mutum

    Ƙarfin ƙashin jikin mutum na fara raguwa tun kafin lokacin da ake tsammani. Sai dai cin abincin da ke ɗauke da muhimman sinadarai na taimakawa wajen kiyaye lafiyar ƙashi da ƙarfafa shi.

    Shan madara na taimakawa wajen samun ƙashi mai ƙarfi. Wannan na daga cikin shawarwarin lafiya na farko da ake bai wa mutane da dama tun suna ƙanana.

    A lokacin ƙuruciya, ana ƙarfafa yara su riƙa shan madararsu, musamman a lokacin hutun makaranta, bisa bayanin cewa sinadarin calcium da ke cikinta zai taimaka wajen samar musu da ƙashi mai ƙarfi da lafiya.

  11. Iran ta ce ta harbo jirgin Amurka mara matuƙi a mashigar Hormuz

    Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin yaƙi maras matuƙi na Amurka ƙirar MQ-1 a gabashin mashigar Hormuz.

    A cewar rundunar, "wannan shi ne jirgin leƙen asiri da na yaƙi maras matuƙi na huɗu mallakin sojojin Amurka da aka harbo cikin sa'o'i 24 da suka gabata."

    A kwanakin baya-bayan nan, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci da kuma sojojin Iran sun sha bayyana cewa sun yi nasarar harbo jiragen marasa matuƙi na sojojin Amurka.

    Sai dai har yanzu Babban Hedikwatar Sojojin Amurka ta Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ba ta tabbatar ko ta musanta waɗannan ikirari ba.

  12. Amurka ta buƙaci sojojinta su taƙaita mu'amala da sojojin Canada

    Ma'aikatar Tsaron Amurka ta umarci sojojin ƙasar da su taƙaita mu'amalar zamantakewa da takwarorinsu na Canada.

    Sanata Mike Rounds na jam'iyyar Republican, wanda ke halartar taron soji na shekara-shekara a Canada, ya ce takunkumin zai ci gaba da kasancewa har sai ƙasashen biyu sun cimma yarjejeniya kan cinikin makamai.

    Wakiliyar BBC ta ce "Canada na duba yiwuwar sayen jiragen yaƙi ƙirar F-35 da dama daga Amurka ko Turai, yayin da take ƙoƙarin ƙara kashe kuɗi a fannin tsaro."

    Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta yi tsami a lokacin mulkin Shugaba Trump, inda ƙasashen biyu suka ƙaƙaba wa juna harajin kasuwanci..

  13. Ana fargabar fuskantar ambaliya mai tsanani a San Francisco

    Magajin Garin San Francisco ya yi gargaɗi game da wani yanayi mai matuƙar tsanani, yayin da ake fuskantar ƙaruwar yawan ruwan teku da ba a taɓa ganini irinsa ba a tarihi.

    Daniel Lurie ya bayyana cewa, mamakon ruwan sama da iska mai karfi, tare da karuwar ruwan tekun, na iya haifar da ambaliyar ruwa mai zurfin da ya wuce rabin mita.

    Ya ce "wannan gargaɗi ne da na ke son kowa ya dauka da muhimmanci, muna son ku taƙaita tafiye-tafiyen da ba su da muhimmanci, musamman a wannna lokacin da ake samu ƙaruwar yawan ruwan teku.

    Hukumar Kula da Yanayi ta Amurka ta kuma yi gargaɗin ambaliyar ruwa da iska mai ƙarfi a wasu sassan jihar Florida, waɗanda ke da alaƙa da lamarin sauyin yanayi na El Nino.

  14. Ministan ilimin Koriya ta Kudu ya yi murabus saboda maguɗin jarabawa

    Ministan ilimi na Koriya ta Kudu ya yi murabus saboda badaƙalar magudin jarrabawa. Choi Kyo-jin ya ce ya ɗauki cikakken alhakin ruɗanin da aka samu sakamakon sabbin matakan daƙile magudi ta hanyar amfani da fasahar AI da aka ɗauka a jarrabawar shiga jami'a.

    Mako guda da ya gabata, wanda ya fi kowa samun maki a jarrabawar akawun haraji na Koriya ta Kudu ya amince da amfani da wata ƙaramar kyamara da wayar salula.

    Wannan ikirarin ya sa hukumomi suka sanar da matakan gano na'urori da aka boye, da suka hada da aika sanarwar gaggawa zuwa wayoyin hannu.

    Jarabawar shiga jami'a ta shekara-shekara a Koriya ta Kudu baban lamari da ke shafar miliyoyin dalibai a kasar.

  15. Falasɗinawa biyu sun mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Gaza

    Majiyoyin kiwon lafiya a Gaza sun tabbatar da mutuwar Falasɗinawa biyu da suka jikkata sakamakon wani hari na Isra'ila a kudancin Gaza.

    A cewar Asibitin Nasser Medical Complex, mutum biyu sun samu raunuka ne a wani hari da Isra'ila ta kai yankin Al-Mawasi da ke birnin Khan Yunis a safiyar ranar Lahadi.

    Bayan an kai su asibiti domin jinya, daga bisani suka rasu sakamakon munanan raunukan da suka samu.

  16. Buɗewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC.

    Za ku iya leƙwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta sauran labaranmu da kallon bidiyo, tare da tafka muhawara.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.