An kama ƴan Mexico biyar a Najeriya bisa zargin sarrafa ƙwayar meth ta dala miliyan 227
An kama wasu ƴan ƙasar Mexico biyar da kuma wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya bayan da hukumomi suka gano wani babban ɗakin sarrafa ƙwayar methamphetamine (meth) a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin ƙasar.
Hukumar Yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce ta ƙwace fiye da tan 1.5 na wannan ƙwaya. Ƙwayoyin da aka ƙwace sun haɗa da waɗanda aka riga aka sarrafa da kuma waɗanda har yanzu ake sarrafawa a cikin ɗakin.
NDLEA ta ƙiyasta darajar miyagun ƙwayoyin da aka kama ta kai kusan dala miliyan 227 (£173m).
Wannan shi ne karo na huɗu cikin watannin baya-bayan nan da aka gano irin wannan babban ɗakin sarrafa meth da ake zargin yana da alaƙa da ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi na Mexico a Najeriya.