Mu kwana lafiya
Nan muka kawo ƙarshen labarai rahotonni a wannan shafi na ranar Laraba.
Za mu zo da wani shafin a gobe Alhamis.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/09/2024
Daga Aisha Babangida da Abdullahi Bello Dingiza
Nan muka kawo ƙarshen labarai rahotonni a wannan shafi na ranar Laraba.
Za mu zo da wani shafin a gobe Alhamis.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Kwamatin ba da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na duniya wato Ballon d’Or ya fitar da jerin 'yan wasa 30 da za a zaɓa ba tare da Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo ba a cikinsu.
Wannan ne karon farko da aka yi hakan cikin shekara 21 - tun shekarar 2003.
Duk da cewa Messi ya lashe Copa America da Argentina, ba shi ne ɗan wasan da ya fi ƙoƙari ba a gasar.
Kazalika, Ronaldo ya ci ƙwallo sama da 50 a shekarar wasan da ta ƙare, amma kuma bai je ko'ina ba a gasar Euro 2024, inda aka cire Portugal a zagayen kwata fayinal kuma bai ci ƙwallo ko ɗaya ba.
Messi ya lashe kyautar sau takwas a tarihi, yayin da Ronaldo ya ci biyar.
Ga jerin sunayen 'yan wasan da za a rairayo uku daga ciki kuma daga ƙarshe a zaɓi mutum ɗaya:

Asalin hoton, RT
Gwamnatin Amurka ta sanar da ƙaƙaba takunkumai kan wasu shugabannin kafar yada labaran kasar Rasha ta RT da wasu mutane da dama.
Amurkar ta zarge su da yunƙurin yin katsalandan a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Nuwamba.
Baitulmalin Amurka ta zargi wasu mutum 10 - ciki har da babbar editan RT Margarita Simonovna, da mataimakiyarta Elizaveta Yuryevna Brodskaia -- da wasu kungiyoyi biyu da yunkurin shirya tafka maguɗi a zaɓen na watan Nuwamba mai zuwa.
Mataimakin babban mai shigar da ƙara na Amurka, Matthew Olsen, ya yi magana ne a wani taro na Kwamitin duba barazana ga zabe na Ma'aikatar Shari'a.
Ya ce: "Tuhume-tuhumen da aka yi yau sun zama abin tunatarwa cewa ma'aikatar shari'a ta ci gaba da yin tsayin daka wajen kare dimokuradiyyarmu daga katsalandan ɗin ƙasashen waje da kuma kare haƙƙin Amurkawa da ke cikin tsarin mulki."

Asalin hoton, Nema
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kwaso 'yan ƙasarta 167 da suka maƙale a ƙasar Libya.
Sanarwar da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa, Nema, ta fitar a yau Laraba ta ce mutanen sun isa filin jirgin sama na Legas da misalin ƙarfe 3:51 na ranar Talata.
Nema ta ce an yi aikin kwaso su ne bisa taimakon ƙungiyar 'yan cirani ta duniya wato International Organisation for Migration (IOM).
Mutanen sun ƙunshi maza 77, da mata 69, da yara 10, da kuma jarirai 11.

Asalin hoton, Nema
Aƙalla mutum 31 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon ambaliyar ruwa da ta auka wa ƙananan hukumomin jihar Kano 21, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.
Babban sakatare na hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa reshen Kano, Isyaku Kubarachi, ya ce ambaliyar ta kuma rusa gidaje 5,280 a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.
"Mutum 31,818 lamarin ya shafa da kuma rusa gidaje 5,280," in ji shi. "Bala'in ya kuma lalata gonaki 2,518 da suka kai faɗin hekta 976."
Ya ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ne ya jawo ambaliyar, kuma akasarin gidajen da lamarin ya shafa na ƙasa ne.

Asalin hoton, Garba Shehu
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da mutanen da 'yanbindiga suka kashe a jihar Yobe a farkon makon nan.
Wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawunsa, ya wallafa a shafukan zumunta ta ce harin na baya-bayan nan "mummunar tunatarwa ce ga mazauna yankuna cewa akwai babban aiki a gabansu da za su yi wajen taimakawa a daƙile matsalar 'yanta'adda".
Rahotonni daga jihar ta Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa an yi jana'izar mutum 30 da maharan masu iƙirarin jihadi suka kashe.
Cikin saƙon da ya aika wa Gwamna Mai Mala Buni da kuma majalisar sarakunan Yobe, tsohon shugaban ya yi addu'ar Allah ya ji ƙan su, in ji sanarwar.
"Ya kuma nemi a ɗauki mummunan mataki kan waɗanda suka aikata wannan aikin rashin imanin."
Shugaban Ukraine ya sake yin kira ga kawayen kasarsa su samar da karin na'urorin tsaron sama bayan da aka kashe mutum bakwai a wani sabon harin bama-bamai da Rasha ta kai a birnin Lviv da tsakar dare.
Harin ya biyo bayan wani ƙazami da aka kai a jiya Talata a birnin Poltava.
Magajin garin Lviv, Andrii Sadovyi, ya yi bayani kan munin harin: “Barnar ta yi yawa, sama da gine-gine masu dinbin tarihi 70 a cikin birnin sun ruguje.
"Ana kan aikin kwashe baraguzan, kuma gobara ta tashi a yankin ma'aikatar titin jirgin kasa wanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ke kokarin shawo kanta. wannan ba karamin hari ba ne."
A yau Laraba Moscow ta ce Ukraine za ta fuskanci martani mai zafi idan har ta kai hari cikin yankunan Rasha.

Asalin hoton, Bala Mohammed/X
Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP ta buƙaci jami'an tsaron Najeriya su ɗauki mataki kan 'barazanar' da suka ce Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi musu.
A ƙarshen makon a ya gabata ne dai tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi barazanar haifar da rikicin siyasa a jihohin gwamnonin jam'iyyar, matsawar suka ci gaba da sa baki kan rikicin siyasar jihar Rivers.
''Na ji wasu gwamnoni da suka ce za su ƙwace jam'iyyarmu don miƙa wa wani, Ina tausaya wa waɗannan gwamnoni, saboda zan kunno musu wutar da ba za su iya kashe ta ba a jihohinsu'', in ji Mista Wike.
To sai dai cikin sanarwar da daraktan ƙungiyar gwamnonin PDPn, Emmanuel Agbo, ya fitar ƙungiyar ta ce babu wanda ya fi ƙarfin doka sannan ta buƙaci jami'an tsaro su ɗauki mataki kan kalaman ministan, kamar yadda gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.
“Ƙungiyarmu na kira da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasar nan su ɗauki mataki kan kalaman ministan da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ƙoƙarin haifar da fiitina a jihohin, saboda babu wanda ya fi ƙarfin doka'', in ji sanarwar.
Gwamnonin na PDP sun kuma ce kalaman na mista Wike ba abu ne da za a lamunta ba saboda yadda suke barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, ya sanar da matakin ƙarin farashin man fetur, ƴan ƙasar da dama ke ci gaba da bayyana fargabarsu kan ƙaruwar farashin kayyan masarufi a ƙasar.
Dama dai ƴan Najeriya na cikin halin matsin rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi, lamarin da masana da dama suka alaƙanta da cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a ranar farko da ta karɓi mulki a watan Mayun 2023.
Tashin farashin kaya da matsin tattalin arziƙi ya kai ga cewa wasu al'ummar ƙasar suka gudanar da zanga-zanga a farkon watan Agusta.
Ci gaban labarin - https://www.bbc.com/hausa/articles/ckgw5xl6d0do

‘Yan Najeriya dai na fuskantar ƙalubale biyu da suka haɗa da na matsanancin ƙarancin man fetur da kuma tsadar kayayyaki, sakamakon ƙarin kuɗin mai da NNPCL ya yi.
Kamfanin mai na NNPCL da ke shigo da man fetur da kuma rarraba shi, ya bayyana basussuka da hauhawar farashin man a kasuwannin duniya, a matsayin dalilan ƙara farashin man fetur ɗin
Lamarin dai ya janyo dogayen layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar, inda mutane da dama suka maƙale.
Masu zirga'zirga a Legas sun shaida wa BBC kokensu kan wahalar da suke sha wajen nema da samun motocin bas ɗin hawa da kuma ƙarin kuɗin mota lamarin da ya tilasta wa mutane da yawa takawa a ƙafa don yin tafiya mai nisa.
A ranar Talata ne kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin farashin man fetur daga naira 617 zuwa naira 897 a kan kowacce lita.
Yayin da gidajen mai na NNPCL ke bayar da farashi mafi karanci, yawancin farashin - gidajen mai masu zaman kansu - ya yi tashin gwauron zabi, inda wasu a Jihohi kamar Oyo da Kano da Kaduna ke sayar da man a kan Naira 1,200 kan kowace lita.
BBC ta ruwaito cewa yawancin tasoshin mai sun rufe a jihar Kano ko dai saboda rashin man fetur ko kuma don daidaita farashin su, lamarin da ya sa direbobi ke jira a dogon layi domin sayen man.
Cire tallafin man fetur da shugaba Bola Tinubu ya yi ya ƙara ta’azzara taɓarɓarewar tattalin arziki, wanda ya haifar da zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa a watan Agusta.

Asalin hoton, Getty Images
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo za ta fara karɓar alluran rigakafin cutar ƙyandar biri a ranar Alhamis, 5 ga Satumba.
Kason farko na rigakafin zai haɗa da allura 99,100, sannan kuma a kashi na biyu allura 100,900 a ranar Asabar wanda za a karɓa a ranar 7 ga watan Satumba.
Kamfanin Bavarian Nordic na Denmark ne ya samar da riga-kafin wanda Afirka CDC ta sayo kuma Amurka ta ba da gudummawarsu.
Dokta Cris Kacita, manajan kula da cutar mpox na DR Congo, ya bayyana cewa, za a adana alluran a Kinkole Hub, wurin ajiyar alluran riga-kafi a babban birnin ƙasar, Kinshasa, kafin a raba su.
Akalla mutane 10 ne suka mutu, wasu 20 kuma suka jikkata a rikicin kabilanci da ya ɓarke a yankin Galgudud da ke tsakiyar ƙasar Somaliya a jiya, a cewar wani rahoto da gidan talabijin na Universal Somali mai zaman kansa ya bayar.
Rikicin ya ɓarke ne a yankin Bali-Senyoone na jihar Galmudug, wanda ya haɗa da ‘yan banga da suka fito daga garuruwan Abudwaq da Cadaado.
Ba a fayyace musabbabin rikicin ba, amma irin waɗannan rigingimun da ake fama da su a yankin na faruwa ne sakamakon ƙabilanci da kisar ramuwar gayya, da filayen kiwo da dai sauransu.
A baya dai gwamnatin tarayyar Somaliya ta zargi ƙungiyar ta'adda ta al-Shabab da yin amfani da waɗannan rikice-rikice na ƙabilanci domin ƙara dagula zaman lafiya a yankin.
A farkon watan Yuni, sama da mutum 50 ne suka mutu, wasu 60 kuma suka jikkata, a fadan da aka gwabza tsakanin wasu kabilun garin Abudwaq da Herale a yankin Galmudug.

Asalin hoton, SAUL LOEB
Hamshaƙin attajirin nan na Amurka, Bill Gates ya ce ba a karɓar haraji yadda ya kamata a Najeriya.
Yayain da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan abinci mai gina jiki da wata ƙungiyar matasan Afirka ta shirya a Abuja, shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, ya ce nan da wani lokaci mai zuwa, Najeriya na iya zama babbar ƙasar da ke fitar da abinci zuwa kasuwannin duniya .
“A fannin noma, a yau Najeriya na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke sayo abinci daga ƙetare, amma duba da yawan jama'ar ƙasar idan ƙasar ta yi amfani da shawarwarin da ake bai wa manoman ƙasar, to akwai yiwuwar ƙasar za ta samu bunƙasa a fannin samar da abinci, ta yadda ma za ta zama babbar mai fitar a abinci a duniya'', in ji shi.
Hamshaƙain attajirin ya kuma ce ya kamata manoman ƙasar su rungumi hanyoyin noma na zamani tare da amfani da irin shuka mai inganci domin samun bunƙasar noman abinci a ƙasar.
Haka kuma ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta bunƙasa fannin lafiyarta.
“Ya kamata a bai wa fannin lafiya fifiko. Gwamnatin ƙasar ta jima tana yin shirin ɗaukar nauyin fannin lafiyar fiye da yadda yake a yanzu. To sai dai a haƙiƙanin gaskiya a Najeriya ba a biyan haraji yadda ya kamata''.
Bill Gates ya ce duk 'yan ƙasar da ke son ilimi da lafiyarsu do ya wajaba a kansu su riƙa sauke haƙƙokin da ke kansu.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta tuhumi shugaban Hamas, Yahya Sinwar da wasu ƙusoshin ƙungiyar kan zargin hannu a ƙazamin harin da ƙungiyar ta kai Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Ma'aikatar shari'ar Amurka ta tuhumi 'yan Hamas shida bisa zarge-zarge bakwai, ciki har da kisan Amurkawa da haɗin baki wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci, da kuma amfani da makaman da ke haddasa mummunar ɓarna.
Laifin da ake tuhumarsu da shi ya kuma haɗa da hare-haren da ake zargin Hamas da ƙaddamarwa na tsawon gomman shekaru, da kuma mummunan harin da ta kai kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban bara.
Wannan dai shi ne mataki na farko da jami'an Amurka suka ɗauka na hukunta waɗanda suka kai harin, duk da cewa uku daga cikin wɗanda ake tuhumar sun mutu, yayain da ake kyautata zaton Sinwar na ɓoye a cikin ramuka a Gaza.

Asalin hoton, Other
Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta sanar da cewa sabuwar matatar mai ta Dangote za ta fara samar da lita miliyan 25 na man fetur a kowace rana ga kasuwannin Najeriya a cikin watan Satumbar da muke ciki.
Ana sa ran adadin man zai ƙaru zuwa lita miliyan 30 a kowace rana daga watan Oktoba.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin sada zumuntarta na X ta bayyana cewa, a wani taro da suka yi a Abuja ranar Talata, NMDPRA da Kamfanin NNPCL sun amince da fara sayar da ɗanyen mai ga matatar Dangote da kuɗin ƙasar wato Naira.
Bayan shafe sama da shekara guda da taƙaddamar da aikinta a watan Mayun 2023, matatar Dangote, a ranar Talata, ta fara fitar da man fetur ɗin.
A jiya ne dai kamfanin NNPCL ta ƙara farashin man fetur daga naira 617 zuwa naira 897.
Aliko Dangote ya ce da zarar kamfaninsa ya kammala shirye-shirye da NNPCL, man fetur na kamfanin zai shiga kasuwa.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da sammacin kama ɗan ƙasar Birtaniya, Andrew Wynne tare da wasu ‘yan Najeriya bisa zargin cin amanar ƙasa da ta’addanci a lokacin zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da sammacin bayan ƙarar da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya shigar gaban kotun.
Sufeton 'yansandan ya zargi zargi Wynne da wasu ƴan zanga-zangar 10 da aka tsare da laifin haɗin baki do nufin hamɓarar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da cin amanar ƙasa da tayar da zaune tsaye, da kuma ta’addanci, wanda ya saɓa wa sassa da dama na dokar ƙasa.
Waɗanda ake tuhuman, ana kuma zarginsu da hannu wajen shirya kai hare-hare da suka haɗa da ƙona harabar babbar kotu da ofishin NCC, da kuma gidan buga takardu a Kano.
A farkon wannan makon ne dai rundunar 'yansandan Najeriya ta ayyana neman mista Wynne ruwa a jallo, bisa waɗannan zarge.
To sai a cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels Mista Wynne, ya musanta zarge-zargen tare da cewa zai amsa gayyatar 'yansanda ta manhajar Zoom ko whatsapp.

Asalin hoton, Akinwumi Akinkunmi
Iyalan Taiwo Michael Akinkunmi, mutumin da ya zana tutar Najeriya, sun ce sun gaji da jiran jana'izar karramawar gwamnatin Najeriya ta yi musu alƙawari, shekara guda bayan rasuwarsa.
A shekarar da ta gabata ne marigayin ya mutu yana da shekaru 87 a duniya.
A maimokon jiran jana'izar da aka yi musu alƙwari, iyalan sun ce za su binne Akinkunmi, wanda aka fi sani da "Mr. Flag" a wannan makon a jihar Oyo, inda ya ke zauna.
Duk da fatan jana'izar ƙarramawar, ɗan Akinkunmi, Akinwumi Akinkunmi, ya bayyana cewa iyalan sun zaɓi su binne shi, tare da tallafin da gwamnatin jihar Oyo ta bayar.
"Dole ne mu yi masa jana'izar da ta dace," kamar yadda ɗan nasa ya shaida wa BBC.
Taiwo Akinkunmi, ya zana tutar Najeriya kafin ƙasar ta samu 'yancin kai a 1960.
An haife shi ne a Ibadan da ke jihar Oyo, ya uma yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnati a ma’aikatar noma har zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekarar 1994.
Duk da irin gudunmawar da Akinkunmi ya bayar, har zuwa lokacin da Nijeriya ta cika shekara 50 da samun ‘yancin kai, ba a sanya shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan Nijeriya 50 ba.
Bayan rasuwarsa ne wani sanata ya nemi ayi masa jana’izar karramawa a jihar wanda har yanzu, bayan shekara guda kenan, babu wani abu da ya gudana. lamarin da ya sa danginsa suka yanke shawarar binne sa da tallafin da gwamnatin jihar Oyo ta samar.

Asalin hoton, REUTERS/Roman Baluk
Magarin garin Lviv na ƙasar Ukraine, Andriy Sadovy ya ce mutum bakwai ne suka mutu ciki har da ƙananan yara uku a wani sabon harin da Rasha ta kai Ukraine, a cewar magajin garin.
An kai harin ne da sanyin safiyar Laraba, inda Rasha ta tura jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami, in ji Sadovy.
Harin na Lviv na zuwa ne a dai dai lokacin da Ukraine ke ci gaba da kokawa kan wani mummunan harin da aka kai a wata cibiyar soji da ke Poltava, wanda ya yi sadaniyyar mutuwar aƙalla mutum 50 a ranar Talata.
An kuma bayar da rahoton fashe-fashe a Kyiv babban birnin ƙasar.
A Kryvyy Rih, mutume biyar sun jikkata lokacin da aka kai hari a wani otel, wanda ya lalata gine-ginen da ke kusa da wurin.
Duk da ɓarnar da aka samu, magajin garin, Oleksandr Vilkul ya bayyana jin daɗinsa da cewa ba a samu asarar rai ba, yana mai cewa.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Sudan sun aike da dakarun soji zuwa Gallabat, wani gari da ke kusa da kan iyakar ƙasar Habasha, domin mayar da martani ga ƙazamin faɗa tsakanin 'yan kabilar Fano da sojojin Habasha.
Jaridar Sudan Tribune ta ruwaito cewa kwamitin tsaro na jihar Gedaref na gabashin Sudan ya ba da shawarar a ci gaba da rufe iyakokin da kuma ƙara yawan sojojin da za su tabbatar da tsaro a yankin.
Wani sabon rikici tsakanin sojojin Habasha da 'yan tawayen Fano ya ɓarke a yankin Kokit na yankin Amhara na ƙasar Habasha mai tazarar kilomita 15 daga Gallabat, lamarin da ya sa ɗaruruwan mutane tserewa zuwa Sudan.
Tun da farko dai Sudan ta rufe mashigar Gallabat a ranar 2 ga watan Satumba bayan mayaƙan Fano sun ƙwace garin Metema na Habasha.
Hukumomin ƙasar Habasha ba su ce uffan ba game da ƙwace garin Metema da ke zaman mafakar dubban 'yan gudun hijirar da ke tserewa rikici a Sudan.
Masu bibiyar mu, barka da warhaka. Da fatan muna lafiya a wannan rana.
A yau ma, kamar kodayaushe, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashe maƙwabta.
Za kuma ku iya leƙawa shafukan sada zumuntarmu domin kallon hotuna da bidiyo.
Sai ku kasance tare da mu.