An soke jan katin da aka bai wa Yoro a wasan Liverpool, Premier League
An soke dakatarwar wasa ɗaya da aka yi wa Leny Yoro, bayan jan katin da aka nuna masa a wasan da Manchester United ta sha kashi 4-0 a hannun Liverpool.
An kori mai tsaron bayan ɗan ƙasar Faransa ne bayan laifin da ya yi wa ɗan wasan Liverpool, Alexander Isak, yayin da yake kan hanyar zura ƙwallo a raga, inda alkalin wasa Sam Barrott ya yanke cewa Yoro ya hana damar cin ƙwallo.
Tun a ranar Litinin Manchester United ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan korar ɗan wasan, kuma yanzu Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) ta tabbatar da cewa an soke dakatarwar.
FA ta ce za ta fitar da cikakken bayanin dalilan da suka sa aka ɗage dakatarwar a nan gaba.