Trump ya bayar da umarnin ƙaddamar da hari kan ISIS a Somaliya

Asalin hoton, US Africa Command
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin ƙaddamar da hare-hare ta sama kan ƙungiyar ISIS a Somaliya.
Mista Trump ya ce an kashe da dama daga mayaƙan ƙungiyar a harin, wanda ya kuma lalata wuraren da suka ɓoye.
Ya ƙara da cewa hare-haren sun nuna aniyar Amurka na gano tare da kashe duk wanda ke yi wa Amurkawa barazana.
Ƙungiyar ISIS na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da suka ɓulla a 2010, amma a yanzu ƙungiyar ta taƙaita ne kawai musamman a wasu yankunan Afirka.
Amurka ta sha ƙaddamar da hare-hare a Somaliya, musamman a shekarar da ta gabata da nufin kakkaɓe masu ikirrarin jihadi.
















