Sai da safe
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Litinin.
Za mu kawo wasu rahotonnin gobe da safe a wani shafin daban.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/03/2025
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Aliyu Jaafar, da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Litinin.
Za mu kawo wasu rahotonnin gobe da safe a wani shafin daban.

Asalin hoton, Dangote Group
Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPC ya ce yana tattaunawa da matatar mai ta Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira.
Sanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko.
Wata sanarwa da kamfanin ya fitar a yau Litinin ta ce ba haka lamarin yake, yana mai cewa sai a ƙarshen watan nan na Maris yarjejeniyar za ta ƙare.
"A sani, yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a naira ta wata shida ce, kuma da sharaɗin akwai man, wadda za ta ƙare a ƙarshen watan Maris na 2025," a cewar sanarwar da Olufemi Soneye ya fitar.
"Ana ci gaba da tattaunawa domin ƙulla sabuwar yarjejeniya," in ji shi.
Masana na cewa idan NNPC ya daina sayar wa matatar Dangote mai a naira hakan zai iya haddasa hauhawar farashin man, maimakon sauƙin da ake tunanin hakan ya jawo a baya-bayan nan.

Asalin hoton, State House
Wata kotu a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ta ɗaure mutum uku wata shida a gidan yari saboda laifin wulaƙanta takardun kuɗi na naira.
Mai Shari'a Uche Agomoh ya kama Amos Remilekun Ilesanmi, da Olanrewaju Samuel Ilesanmi, da Ugbeh Emmanuel Ukali da laifin yin liƙi da kuɗi naira N391,400.00 a ƙarar da hukumar EFCC ta shigar.
"Bayan karanto musu laifinsu, duka mutanen waɗanda aka taɓa ɗaurewa saboda laifin zamba ta intanet da kuma sojan-gona sun amsa laifin," a cewar wata sanarwa da EFCC ta fitar a yau Litinin.
Bayan lauyansu ya nemi a sassauta musu, sai alƙalin ya yanke musu hukuncin zama a gidan yari na wata shida ba tare da zaɓin biyan tara ba tare da ƙwace adadin kuɗin da suka liƙa ɗin.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama mutanen tun a watan Yunin 2024, lokacin da aka zarge su da liƙa kuɗin a wani gidan rawa da ke Ibadan babban birnin jihar ta Oyo.

Asalin hoton, Social Media
Mutumin da ya yi wa jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya taya tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai murnar komawa jam'iyyar tasu.
Adewole Adebayo ya ce lokaci ya yi da za su haɗa kai da El-Rufai "domin yaƙi da talauci da kuma matsalar tsaro".
A yau Litinin ne Nasir El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga APC - bayan shafe shekara takwas a matsayin gwamnan jihar da ke arewaci - mai mulkin Najeriya tare da komawa SDP mai adawa.
Sanarwar ficewar tasa na ci gaba da jan hankalin 'yan Najeriya musamman a shafukan zumunta, saboda kasancewarsa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar kafin babban zaɓen 2015.
"A madadin mambobin SDP...ina yi wa ɗan'uwana El-Rufai maraba zuwa cikin jam'iyyarmu," in ji Adewole cikin wani saƙo a shafinsa na dandalin X.

Asalin hoton, PA Media
Ana wani gagarumin aikin ceto a gabas da gaɓar tekun gabashin Ingila bayan tankar mai mallakin Amurka ta yi taho-mu-gama da wani jirgin ruwa na dakon kaya na Portugal a tekun North Sea.
Wakilin BBC ya ce wata sanarwa ta ce ana shirya kai ɗaukin gaggawa bayan samun rahoton tankar mai da jirgin ruwan dakon kaya sun yi karo.
Jirgin ruwan da kuma tankar sun kama da wuta yayin da wani bakin hayaki ke tashi a sama.
Jirage masu saukar ungulu da jiragen ruwa na kashe gobara duk sun kewaye wurin lamarin ya auku.

Asalin hoton, EPA
Rasha ta kori wani jami'in diflomasiyya na Birtaniya da matar wani jami'in daban, a cewar hukumar tsaro ta cikin gida a ƙasar.
Hukumar tsaro ta Federal Security Service (FSB) na zargin mutanen ne da "leƙen asiri da kuma zagon ƙasa", inda ta ce an umarce su da su bar Rasha cikin mako biyu.
Ofishin Harkokin Wajen Birtaniya ya ce: "Ba wannan ne karo na farko da Rasha ta yi zargi maras tushe ba a kan ma'aikatanmu."
A watan da ya gabata Birtaniya ta kori wani jami'in diflomasiyyar Rasha a matsayin ramuwar gayya na korar wani jami'i da Rasha ta yi a watan Nuwamban 2024.

Gwamnatin ƙasar Ajantina ta ayyana zaman makoki na kwana uku bayan da hukumomin ƙasar suka ce adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan da aka yi ranar Juma'a sun kai 16.
Cikin waɗanda suka mutu har da wasu ƙananan yara mata biyu, da mai shekara ɗaya da mai shekara biyar da haihuwa.
An yi ruwan sama da ake tunanin ya kai adadin wanda ake yi shekara guda cikin ƴan sa'o'i kaɗan, inda ya mamaye dukkan unguwanni da ke yankin Bahia Blanca, wani gari mai tashar jiragen ruwa a kudancin lardin Buenos Aires.
Ambaliyar ta kuma katse wutar lantarki a yawancin yankunan da ke gaɓar tekun.

Asalin hoton, Tinubu Facebook
Najeriya ta shigo da man fetur da ya kai na naira tiriliyan 12.48 a shekarar 2024, kamar yadda alƙaluman Hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS suka nuna.
Rahoton hukumar ya ƙara da cewa an shigo da fetur na naira tiriliyan 2.63 a rubu'in farko na shekara, sannan aka shigo da na naira tiriliyan 3.22 a rubu'i na biyu, sai kuma na tirilan 3.32 a rubu'i na uku, da kuma na tiriliyan 3.3 a rubu'i na huɗu na shekarar.
Rahoton ya kuma nuna cewa Najeriya ta yi cinikayya da ƙasashen duniya da ya kai na naira tiriliyan 138, inda aka kashe naira triliyan 60.5 domin shigo da kayayyaki da kuma naira tiriliyan 77.4 domin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Haka kuma tataccen man fetur ne kan gaba a cikin abubuwan da aka shigo da su ƙasar, sannan a ɗaya ɓangaren kuma, fitar da ɗanyen mai ne ke kan gaba a jerin abubuwan da aka fitar da su daga ƙasar.

Akwai yiwuwar cewa nan da ƙasa da shekara biyu, Birtaniya za ta amince domin a fara sayar da nama da sukari da wasu kayan madara da aka haɗa a ɗakin bincike, inda zai zama karon farko da hukuma ta amince mutane su ci irin abincin.
Hukumar kula da ingancin abinci ta fara yunƙuri domin ganin ta cika sharuɗɗan da ake buƙata cikin lokaci, domin mutane su fara amfani da kayayyakin abincin da ake haɗawa ta hanyar amfani da wasu sinadarai.
Tuni kamfanonin Birtaniya suka nuna sha'awarsu ta cin kasuwar naman, duk da cewa sun ce sharuɗɗan gwamnati na jawo musu tsaiko.
A watan jiya ne aka fara sayar da abincin karnuka wanda aka haɗa da naman ɗakin bincike a karon farko a Birtaniya.
Tun a shekarar 2020 ƙasar Singapore ta amince a fara sayar da naman da aka haɗa a ɗakin bincike, sannan Amurka ta bi sahunta bayan shekara uku, kafin Isra'ila ta shiga layi a bara.
Sai dai Italiya ta haramta cin naman, sannan jihohin Alabama da Florida na Amurka su ma sun haramta amfani da shi.

Asalin hoton, Nuhu Ribadu/Facebook
Iyalai da masoya suna nuna alhini tare da jimaminsu kan rasuwar fitaccen malamin shari'ar a Jami'ar ABU, Farfesa Kharisu Chukkol.
Rahotanni sun ce mamacin ya rasu ne yana da shekara 82 a duniya bayan fama da jinya da ya kwana biyu yana yi.
Daga cikin ƴaƴan marigayin akwai tsohon shugaban riƙo na Hukumar EFCC, Abdulkareem Chukkol.
Daga cikin waɗanda suka shige gaba wajen aka saƙon jajensu, akwai mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ya ce marigayin malaminsa ne.
"ƙwararren masanin ɓangaren shari'a ne kuma abin koyi a wajenmu. Muna addu'ar Allah ya jiƙan shi."

Asalin hoton, Rivers state Government House Media
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Rivers, Tony Okocha ya yi kira ga Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulkin jihar, ko kuma a tsige shi.
Okocha ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ƴanmajalisar jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi.
"Hukuncin kotun ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi," in ji Okocha kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tun da farko, bayan hukuncin kotun ƙolin, majalisar jihar ta ba gwamnan jihar wa'adin kwana biyu ya sake gabatar da kasafin kuɗi, gayyatar da ya ƙi amsawa.
Daga baya shi kuma ya gayyace su gidan gwamnati domin su tattauna, inda su ma suka ce ba za su je ba, domin a kafofin sadarwa suka ga gayyatar.

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Jamus ta gargaɗi Isra'ila cewa matakin da ta ɗauka na yanke lantarkin Gaza da hana shigar da kayan agaji zai sake jefa yankin cikin mawuyacin hali.
Kakakin gwamnatin ƙasar ta ce matakan da Isra'ila ta ɗauka ba za ta saɓu ba, domin sun karya dokokin duniya.
Isra'ila dai ta ce ta ɗauki matakin ne domin tursasa Hamas ta sako sauran waɗanda ta yi garkuwa da su.
Wakilan Isra'ila za su isa Qatar domin tattaunawa kan tsawaita wa'adin zagaye na farko na yarjejeniyar tsagaita wutar.
Sannan wakilin Trump a yankin Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, zai shiga tattaunawar domin tabbatar da samun matsaya.
A yau Litinin ne harajin da China ta ƙaƙaba kan wasu kayayyakin amfanin gona na Amurka ya fara aiki, lamarin da ke nuni da ƙaruwar takun-saƙar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu masu ƙarfin tattalin arziki a duniya.
Wakiliyar BBC ta ce ma'aikatar kuɗin China ta fitar da sanawar cewa ta ƙara kashi 15 cikin ɗari kan kaji da alkama da audugar da aka shigowa da su daga Amurka.
Tun komawarsa mulki a watan Janairu dai Mista Trump ya ƙara haraji kan kayayyakin manyan abokan hulɗar kasuwancin ƙasarsa da suka haɗa da China da Canada da Mexico.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK
Hukumar EFCC ta ce a shekarar 2024 ta samu nasarar da ba ta taɓa samu ba tun da lokacin da aka ƙirƙire ta.
Ta ce a shekarar ta ƙwato kuɗaɗe da suka haɗa da naira biliyan 364.6 da da dala miliyan 214.5 da fan 54,318.64 da yuro 31,265 da kuɗin ƙasar Canda, dala 2,990 sai kuma kuɗin ƙasar Australia, dala 740, kamar yadda ta bayyana.
Wasu kuɗaɗen da hukumar ta ƙwato sun haɗa da CFA7,821,375 da dirham ɗin UAE 170 da riyal 5,115 da W73,000, yen 105, da GH¢ 225 da rand 50.
Hukumar ta ƙara da cewa a shekarar ce ta ƙwato rukunin gidaje 750, wanda shi ne mafi girma a tarihin hukumar.
Haka kuma ta ƙwato kuɗaɗen kirifto irin su Bitcoin guda 13.37 wanda darajarsu ta kai dala 572,992.86 da Ethereum 5.97886094 masu ƙimar dala 13,353.06 da USDT 1,002.547631 da sauransu.
Hukumar ta kuma ƙwato kamfani da otel da zinare da fulotai.
Hukumar ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe guda 15,725, ta gurfanar da mutane aƙalla 5,083 a kotu, ta samu nasara a shari'a guda 4,011.
Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa ta samu wannan nasarar ce ta hanyar aiki da jajircewar jami'anta wajen yaƙi da almundahana da sauran laifuka a ƙasar baki ɗaya.

Asalin hoton, Getty Images
A Najeriya fasinjojin motocin sufuri ne suke bayyana damuwarsu kan abun da suka kira rijiya ta ba da ruwa guga ta hana, da masu motocin haya ke musu, ta hanyar ƙin rage farashin sufuri.
Sun ce ya kamata a an rage kuɗin sufuri saboda raguwar da aka samu a farashin litar man fetur a ƙasar.
Fasinjojin sun koka kan yadda suka ce hakan na shafar ɓangarorin rayuwarsu da dama, musamman tafiye-tafiye zuwa wuraren sana’a ko kasuwanci.
Sai dai direbobin sun ce har yanzu farashin bai daidaita ba ne, inda suka yi alƙawarin da zarar farashin ya daidaita za su yi wani abu.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai matatar man fetur ta Dangote ta sake rage farashi man daga naira 890 zuwa naira 825, sannan kamfanin NNPCL shi me ya bi sahu, abin da ake ganin wani matakin samun sauƙi ne ga ƴan ƙasa.

Asalin hoton, EPA
An dakatar da tashi da saukan ɗaruruwan jiragen sama a faɗin ƙasar Jamus bayan ma'aikatan ɓangaren sun fara yajin aiki.
An fara yajin aikin ne a ranar Lahadi, ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar kwadagon ƙasar, Verdi, a filin jirgin Hamburg, kafin ya zama na ƙasa baki ɗaya.
Sun shawaraci fasinjoji a biranen Frankfurt da Munich da Berlin da manyan biranen ƙasar da su da su haƙuri da tafiya ta jirgi.
Ƙungiyar kwadagon ta Verdi, wadda ta ƙunshi ma'aikatan gwamnati da na sufuri, tana yajin aikin ne domin albashi da yanayin aiki.
Rahotanni daga Jamus na nuna cewa yajin aikin zai iya shafar aƙalla fasinjoji 500,000.
Katja Bromm, kakakin filin jirgin Hamburg, inda aka dakatar da tashin jirage 143 da ya kamata su tashi a safiyar yau Litinin, ya ce ƙungiyar Verdi "ba ta kyauta" ba da ta shiga yajin aiki ba tare da sanarwa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴanbindiga sun kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha'u Ma'aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa a ƙauyen Zakirai da ka ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴanbindigar sun yi garkuwa da wani matashi mai shekara 20 mai suna Mohammed Bello, sannan wani ɗan gidan shi mai suna Abubakar ya samu rauni a hannunsa.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce tuni ƴansanda suka fara farautar ɓatagarin domin ceto wanda suka yi garkuwa da shi.
A wani labarin daban, rundunar ƴansandan jihar Kano ta sanar da kama mutum huɗu da take zargin ƴanbindiga ne, sannan ta ƙwace makamai da alburusai da kuɗi kimanin naira 1,028,800.

Asalin hoton, AFP
Amurka da Rasha sun buƙaci a gudanar da wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a yau Litinin domin tattauna tashin hankalin da ke ƙara ƙamari a Syria.
Hakan dai ya biyo bayan kisan da aka yi a ƴan kwanakin nan na ne ɗaruruwan fararen hula a lardunan Latakia da Tartus da ke gaɓar tekun Siriya.
Shugaban riƙon ƙwarya na Syria, Ahmed Al Sharaa, ya ce zai kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki kashe-kashen.
Ya ce babu wanda ya fi ƙarfin doka kuma duk wanda aka samu da jinin ƴan Syria a hannunsa zai fuskanci hukunci cikin gaggawa.

Asalin hoton, Nigerian Senate/X
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta buƙaci shugaban majalisar dattawan ƙasar, Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa sanata Natasha Akpoti-Uduaghan saboda an yi hakan ne ba bisa ƙa'ida ba.
Haka kuma ƙungiyar ta SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Natashan ba komai ba ne illa tauye mata ƴancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda tsarin mulkin Najeriya ya bata.
A makon da ya gabata ne dai majalsair dattawan Najeriya ta sanar da dakatar da Sanata Natasha Uduagahn bayan kwamitin ladabtarwar majalsar ya zarge ta da karya wasu daga cikin dokokinta.

Asalin hoton, AFP
A jamhuriyar Nijar yayin da aka shafe kwanaki da dama ana fama da matsalar ƙarancin man fetur, kamfanin man fetur na Nijar (SONIDEP) ya alaƙanta yanayin da wasu manyan abubuwa guda biyu.
Daraktan kula da kasuwancin man fetur na ƙasar a wata hira da yi da talabijin na ƙasar ya alakanta lamarin da ƙoƙarin da fasakwurin man da kuma ƙarancinsa, inda ya ce kamfanin tace man samar da tankokin mai tsakanin 23 zuwa 25 ne a kullum alhali Yamai kaɗai na buƙatar tankoki aƙalla 25 a kullum.
Ya ƙara da cewa an ƙiyasta ƙasar na buƙatar tsakanin tankoki 45 zuwa 50 a kullum.
Sai dai ƴan ƙasar na nuna damuwa kan yadda suke ganin ana samar da mai tare da tace shi a cikin ƙasar amma duk da haka ya gaza biyan buƙatunsu.