Rufewa
A nan za mu rufe wannnan shafin na labaran kai-tsaye na yau Takata.
Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 30/09/2025
Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida
A nan za mu rufe wannnan shafin na labaran kai-tsaye na yau Takata.
Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Qatar ya ce ƙasarsa za ta koma kan teburin sulhu domin ci gaba da shiga tsakani domin samar da zaman lafiya a Zirin Gaza.
Wannan na zuwa ne bayan Netanyahu ya nemi afuwar Qatar game da hare-haren da ya kai a Doha kan jagororin Hamas.
A wayar da Trump da Netanyahu suka yi da Firaministan na Qatar, Netanyahu ya bayyana nadamarsa kan mutuwar wani ɗan Qatar a harin na ranar 9 ga watan Satumba, wanda ya ce ya karya ƴancin ƙasar na Qatar, sannan ya ce Isra'ila ba za ta sake irin haka ba.
Ministan harkokin wajen Qatar ya ce afuwar da Netanyahu ya nema ce ta sa Qatar ta amince ta ci gaba da shiga tsakani, "domin tabbatar da zaman lafiya a Zirin Gaza ta hanyar amfani da tsare-tsaren da Amurka ta tsara," in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Trump ya shaida wa daruruwan manyan hafsoshin soji da aka tara a wani taro na musamman, cewa ya kamata su yi amfani da biranen Amurka a matsayin filin atisaye, kan abin da ya kira abokan gaba na cikin gida.
Wakilin BBC ya ce shugaba Trump yayi jawabin nasa ne akan yaƙin cikin gida, da ta'azzarar matsalar tsaro a birane kamar su Sanfransisko da Chicago da Los Angeles.
Mista Trump ya kuma kare matakin tura rundunar tsaro ta cikin gida da ya yi, yana mai cewa zai gyara biranen da yake ganin cike suke da laifi ɗaya bayan ɗaya.
Haka kuma ya caccaki abin da ya kira wasa da aiki, yana mai cewa a ƙarƙashin mulkinsa an farfado da ruhin jarumtar soji.
Sojojin Ecuador sun ce an saki ragowar dakarun su huɗu daga cikin goma sha bakwai da aka yi garkuwa da su a ranar Lahadin da ta gabata, yayin zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali akan cire tallafin man fetur.
Sojojin sun kasance tare da wata tawagar agaji ƙarƙashin jagorancin Shugaba Daniel Nabowa, wanda mutane kusan dari uku suka tare, suna jefa masu wani nau'in bam haɗin gida.
Tawagar na raba tallafi ne ga al’ummomin da yajin aikin gama garin ya shafa, wanda ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama a ƙasar ta kira.
Mutanen na zanga-zanga ne kan matakin shugaban na cire tallafin man fetur.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya ce Hamas na da kwanaki uku zuwa hudu ta mayar da martani kan daftarin samar da zaman lafiyar da ya gabatar domin kawo karshen yakin Gaza.
Ya shaida wa ‘yan jarida cewa idan har kungiyar ba ta amince da shi ba, to hakan zai zama mummunan karshe a gare ta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Majed al-Ansari, ya ce ya yi wuri a ce an yi martani, amma daftarin na buƙatar a duba shi sosai cikin tsanaki.
Wakilin BBC ya ce akwai abubuwa da dama da ya kamata a cimma matsaya akansu game da daftarin, kamar taswira da tsarin ƙasar Falasɗinun da za a samar.

Asalin hoton, EPA
Majalisar Dinkin Duniya ta ce matakin da hukumomin Taliban suka dauka na katse intanet a Afghanistan, barazana ce da ka iya cutar da al’ummar kasar baki ɗaya.
Shirin tallafawa al'umma na majalisar dinkin duniya dake Afghanistan ya buƙaci hukumomin Taliban da su dawo da intanet, da hanyoyin sadarwa ba tare da bata lokaci ba.
Wakilyar BBC ta ce katsewar hanyoyin sadarwa a ciki da wajen ƙasar ya shafi hada-hadar bankuna, da kasuwanci ta Internet, da soke tashin jiragen sama da dama.
Har yanzu dai Hukumomin Taliban ɗin ba su bayar da cikakken bayani kan dalilin ɗaukar matakin ba.

Asalin hoton, Reuters
Kotun soji ta musamman a Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo wato DR Congo ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Joseph Kabila hukuncin kisa.
Kotun ta yanke masa hukuncin ne bisa samunsa da aikata laifukan yaƙi da cin amanar ƙasa duk da cewa bai bayyana a kotun ba.
Sai dai ya yi watsi da hukuncin, wanda ya bayyana da rashin adalci, sannan ya yi zargin cewa ana amfani da shari'a wajen "murƙushe ƴan hamayya."
Kabila ya yi mulkin ƙasar na tsawon shekara 18 bayan ya gaji mahaifinsa Laurent, wanda ake harbe a shekarar 2001.
Tsohon shugaban ya miƙa mulki ne ga shugaban ƙasa Félix Tshisekedi a shekarar 2019, sai suka fara takun-saƙa, lamarin da ya sa Kabila ya tsere daga ƙasar a 2023.
A watan Afrilun wannan shekarar ne Kabila ya ce zai iya taimakawa wajen kawo ƙarshen mummunan yaƙin da ake gwabzawa a ƙasar tsakanin gwamnati da ƙungiyar M23 da ta fi ƙarfi a Goma, sannan aka ruwaito ya shiga ƙasar, amma ya tafi ɓangaren da ke ƙarƙashin ƴantawayen.
Bayan wannan ne Tshisekedi ya zargi Kabila da kasancewa cikin waɗanda suke goyon bayan ƙungiyar, sannan sanatacin ƙasar suka cire masa rigar kariya domin ya fuskanci hukunci.

Asalin hoton, Gallo via Getty Images
An tsinci gawar Jakadan Afirka ta Kudu a brinin Paris na Faransa, kwana guda bayan an sanar da rahoton ɓacewar sa.
Nathi Mthethwa ya faɗo ne daga bene hawa na 22 a wani otal da ke yankin.
Rahotanni sun ce ya ɓata ne da yammacin jiya Litinin, lamarin da ya sa ƴansanda suka fara gudanar da bincike. Kawo yanzu ma'aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu ba ta fitar da wata sanarwa ba akai.
Margayin mai shekara 58 ya fara aiki ne a Paris a bara bayan ya taba rike mukamin ministan al’adu da kuma na ‘yansanda.

Asalin hoton, EPA
Shugabannin Turai da na Gabas ta tsakiya sun yi maraba da yarjejeniyar da Amurka ta tsara na tabbatar da zaman lafiya a Gaza.
Shugaba Trump ya ja kunnen Hamas kan kada ta sake ta ƙi amincewa da yarjejeniyar.
Shawarwarin da shugaban Amurka Donald Trump da Firaiminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu suka amince da su sun buƙaci kawo ƙarshen yakin nan take da sakin ƴan Isra'ila 20 da har yanzu ke raye cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Sannan a mayar daga warwakin sauran duka a cikin kwana uku, yayin da Isra'ila za ta saki ɗaruruwan Falasɗinawa da take riƙe da su a gidajen yarinta.

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta sanar da hana sayarwa da amfani da wasu magunguna guda 101 a faɗin ƙasar.
Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na X a ranar Talata, inda ta ce daga yanzu sana'anta magungunan da kasuwancinsu da ma amfani da su "laifi ne" a Najeriya.
NAFDAC ta ce daga cikin dalilan haramta magungunan akwai rashin ingancin lasisi da wasu laifukan da hukumar ta bayyana.
NAFDAC ta lissafin magungunan baki ɗaya a shafin nata da ke ƙasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images
Falasɗinawa na ci gaba da taruwa domin karɓar agaji a Gaza yayin da ɗaruruwan motocin ɗaukar kayan agaji suka shiga Gaza jiya.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da yaƙi ke ci gaba da ɓarkewa a Gaza
Shugaban Amurka Donald Trump dai ya sanar da tsare-tsaren tsagaita wuta yayin da ake sauraran martanin Hamas.
Sabbin hotuna daga Nuseirat a tsakiyar Gaza sun nuna ɗimbin jama’a suna taruwa domin karɓar tallafi daga cibiyar da asusun tallafin bil’adama na Gaza ke kula da ita.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, EPA/Fadar shugaban Najeriya
Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan na da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
To amma cikin wata sanarwa da fadar ta fitar ta ce ƴan Najeriya na sane da abin da ta kira ''rashin takaɓus'' a mulkin Jonathan ɗin na shekarun baya.
Goodluck ya mulki Najeriya a daidai lokacin da ƙungiyar Boko Haram ke kan ganiyarta wajen ƙaddamar hare-hare kan fararen hula.
A baya-bayan nan dai akwai ƙaruwar kiraye-kiraye tsakanin wasu ƴan jam'iyyar hamayya ta PDP kan tsohon shugaban ƙasar ya fito takara a zaɓen 2027.
Karanta cikakken labarin - https://www.bbc.com/hausa/articles/cdr6mp7zdg7o

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Kullen Allah ta ce samar da ma'aikatar kiwon dabbobi da gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu ta yi, ya sake farfaɗo da fatan da Fulanin ƙasar ke da shi na damawa da su a harkokin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Khalil Mohd Bello ne ya bayyana haka a babban taron lalubo hanyoyin magance rikicin manoma da makiyaya da aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar.
Khalil Mohd Bello ya ce Fulanin Najeriya sun jima suna bayar da gudunmowa ta fuskar tattalin ariki da ci gaban ƙasar.
Rikicin manoma da makiyaya wata matsala ce da ta jima tana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya, inda a wasu lokutan take haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Shugaban na Kullen Allah ya ce rikicin manoma da makiyaya matsala ce da ta jima tana haifar da matsaloli da daƙile ci gaban ƙasar.
Ya ce galibi abubuwan da haifar da matsalar su ne rashin bin doka da ƙa’ida, ta hanyar tare wa makiyaya hanyoyin kiwo tare da mayar da dazuka zuwa gonaki a wasu jihohin ƙasar.

Asalin hoton, Khalil Mohd Bello
Ya kuma zayyano wasu hanyoyin da yake ganin za su taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya da suka haɗa:

Asalin hoton, KNUST SHS
Hukumar Ilimi ta Ghana (GES) ta kori Charles Akwasi Aidoo, mataimakin shugaban makarantar sakadire ta Kwame Nkrumah da ke a Jami'ar Kimiyya da fasaha ta Kwame Nkrumah bayan wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta da ke nuna yana taɓa wa wata ɗaliba mace ƙirjinta a wani wuri da ake ganin ofishinsa ne.
A cikin wani bidiyon mai tsawon dakika 16 da ɗalibar ta ɗauka, an ga Aidoo yana sanya kansa a kafadar ɗalibar.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce: “Gwamnati, a cikin ƙudurinta na kare martabar aikin koyarwa da jin daɗi da kare lafiyar ɗalibai, ta cire mataimakin shugaban makarantar daga muƙaminsa.”
Haka kuma, hukumar ta ƙara da cewa: “Mun haramta wa Charles Akwasi Aidoo shiga makarantar yayin da bincike ke gudana bisa ka’idojin hukumar.”
Sanarwar ta bayyana cewa hukumar za ta bi dukkan matakai na doka don tabbatar da cewa an hukunta shi bisa ga ka’idojinta.
Hukumar ta ƙara da cewa suna ƙin duk wani aiki da zai kawo barazana ga lafiya da mutunci da kuma jin daɗin ɗalibai.
Ba wannan ne karo na farko da hukumar ke ɗaukar mataki kan malamai ko shugabannin makarantu da suka aikata “aikin rashin ɗa’a” da ɗalibansu ba.
A watan Nuwamba 2018, hukumar ta kori malamai tara da wasu manyan ma’aikata a wasu makarantu sakamakon aikata batsa da rashin ɗa’a.

Asalin hoton, ARISE TV
Ƴan Fashi sun kashe wata ƴar jaridar Arise TV me suna Somtochukwu Christelle Maduagwu a Abuja.
Somtochukwu ta rasu ne a safiyar Litinin, 29 ga Satumbar 2025 tana da shekera 29 bayan da ƴan fashin suka kutsa cikin gidanta.
Sanarwar da gidan talabin ɗin ya fitar ta ce ƴan sanda sun fara binkike kan lamari da burin kamo waɗande ke da hannu a kisan nata.
“Somtochukwu Christelle Maduagwu ta rasu ne kwatsam, ba zato ba tsammani a safiyar Litinin sakamakon harin ƴan fashi da aka kai gidanta a yankin Katampe, Abuja, wanda ‘yan sanda sun fara bincike.” in ji sanarwar.
Ƴar jaridar wadda kuma ita lauya ce tana da murya mai ƙarfi wadda ke jan hankalin masu kallo da yin hulɗa da su.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa ba a cimma wata yarjejeniya ta amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu ba yayin ganawarsa da Donald Trump.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin Telegram ɗinsa, an tambayi Netanyahu ko ya “yarda da kafa ƙasar Falasɗinu”, sai ya ce "a'a, hakan ba zai taɓa faruwa ba"
Ya ce babu wani tanadi na irin wannan a cikin tsare-tsaren Trump na tsagaita wuta a Gaza, sannan ya ƙara da cewa Isra’ila za ta yi amfani da ƙarfi wajen hana kafuwar Falaɗinu.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen Zambia da Tanzania sun ƙulla yarjejeniyar dala biliyan 1.4 da China domin sabunta tsohuwar layin dogo da ke haɗa ƙsashen biyu saboda ƙarfafa ciniki a yanki da sauƙaƙa jigilar tafiya, kamar yadda gidan jaridar Zambia Monitor ya ruwaito.
Yarjejeniyar ta haɗa gyara layin dogo daga Dar-es-Salaam zuwa New Kapiri Mposhi na Tashar jirgin ƙasa ta Tazara da gyaran manyan masana’antu da kula da layin da ake da shi da kuma sayen ƙarin injinan jirgin ƙasa da motoci.
Ministan sufuri da kayayyaki na Zambia, Frank Tayali, ya ce: "Wannan yarjejeniyar na nufin bai wa manoma da 'yan kasuwa da masana’antu damar samun hanyar zuwa kasuwanni a ƙasashen waje da kuma bayan iyaka.
Haka kuma, yarjejeniyar za ta samar da damar aikin yi ga matasa da ƙarfafa dangantakar zumunci tsakanin ƙasashe.
Ministan Sufuri na Tanzania, Makame Mbarawa, ya ce "aikin zai samar da ayyukan yi da ƙara bunƙasa tattalin arziki a ƙasashen biyu."
Shugaban Chine, Xi Jinping ya yi alƙawarin "tallafawa layin dogo mai shekaru da dama a taron Hadin Gwiwar China da Afirka a watan Satumban 2024, bayan ganawa da Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan.
An kammala tashar jirgin ƙasa ta Tazara ne a shekarar 1976 ta hannun China, amma yanzu tana cikin halin lalacewa, inda daga injinan jirgin ƙasa 50, guda 10 ne kawai ke aiki.

Hukumar tsaro ta DSS a Najeriya ta gurfanar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar Omoyele Sowore a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau, Talata, bisa zargin shi da aibata shugaba Bola Tinubu a shafinsa na X.
Hakazalika, DSS ta gurfanar da manyan kamfanonin sada zumunta na X da Meta a matsayin waɗanda ake ƙara.
Hukumar ta ce waɗannan kamfanoni sun ƙi goge abin da suka kira kalaman ƙarya da cin mutunci da aibata shugaba Tinubu da Sowore ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Tun a ranar 6 ga watan Satumban 2025 ne DSS ta sanar da cewa ta nemi a rufe ko a dakatar da shafin Sowore a dandalin X bisa zargin cewa yana yaɗa kalamai da za su iya haifar da rikici da barazana ga tsaron ƙasa.
Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin kare martabar shugabanci da kuma kare ƙasar daga mummunar tasirin yaɗa labaran ƙarya.
Hukumar ta bayyana cewa kalaman kai tsaye a kan Tinubu barazana ce ga tsaron ƙasar inda ta yi kira ga kamfanin X da ya goge tare da gaggauta rufe ko dakatar da shafin Sowore.
Amma kuma har yanzu X bai rufe shafin nasa ba inda DSS ta zargi kamfanin da rashin bin umarninta dalilin da ya sa ta gurfanar da kamfanin a gaban kotu.


Asalin hoton, Getty Images
Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnati Suna ya ruwaito.
Rahotanni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban dam ɗin Ethiopia da aka buɗe a wannan watan.
Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin ne a ranar 28 ga watan Agusta, inda ta ce ya shafi jihohin Khartoum da River Nile da White Nile da Sennar da kuma Blue Nile.
Ma'aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwa na iya mamaye gidaje da gonaki, tare da kira ga ɗaukar matakan gaggawa.
Farfesa Abbas Sharaky na jami’ar Cairo, masani a fannin ƙasa da albarkatun ruwa, ya bayyana cewa ƙaruwar matakin ruwa a Nilu sakamakon kuskuren ɗan adam ne da ya shafi babban dam na Ethiopia.
Sharaky ya ce injinan da ke kula da tafiyar da ruwan dam huɗu sun gaza aiki, wanda ya sa Ethiopia ta kasa shawo kan ruwan da kuma tura ruwan da ya wuce gona da iri zuwa Sudan.
Ethiopia a jiya ta ƙaryata zargin, inda ta ce dam ɗin ya taka muhimmiyar rawa wajen rage illar ambaliyar.
A kowacce shekara, matakin ruwa a Kogin Nilu yana ƙaruwa a watan Agusta saboda ruwan sama mai yawa a tsaunukan Ethiopia.