Ƙarshen rahotonni
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Laraba, kafin mu kawo muku wasu rahotonnin gobe da safe.
Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran muhimman abubuwa da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Usman Minjibir, Badriyya Kalarawi, Isiyaku Muhammed, da Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Laraba, kafin mu kawo muku wasu rahotonnin gobe da safe.
Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.

Asalin hoton, Getty Images
Japan ta bayyana fargaba bayan Chaina ta yi gwajin harba makami mai linzami da ya ratsa nahiyoyi zuwa tekun Pacific, karon farko bayan fiye da shekara 40.
Beijing ta ce makamin ya sauka cikin ruwan ƙasa da ƙasa, amma ba ta bayyana sunan wurin ba, tana mai cewa ta sanar da kasashen da abin ya shafa.
Australia ta bukaci sanin dalilin gwajin makamin, wanda New Zealand ta bayyana a matsayin abin damuwa.
A watan Yuli China ta dakatar da tattaunawa da Amurka kan batun mallakar makaman nukiliyar bayan Amurkar ta yi cinikin makamai da Taiwan.
Isra'ila ta ce ta kai hare-hare kan wuraren Hezbollah 2,000 a Lebanon tun bayan ƙaddamar da yaƙi a can.
"Cikin kwana uku da suka wuce, mun kai hari wurare sama da 2,000 a Lebanon, ciki har da ɗaruruwa a yau," a cewar kakakin rundunar sojin Daniel Hagari.
Ƙungiyar agaji ta likitoci MSF ta yi gargaɗin matsalolin lafiya a yankin Darfur da ke Sudan.
Wani sabon rahoto da ƙungiyar ta fitar ya ce mata masu ciki 110 ne suka rasa rayukansu tsakanin watan Janairu zuwa Agustan bana, yayin da dubban yara ƙanana ke fuskantar yunwa.
Ƙungiyar ta ce sakamakon rushewar harkokin lafiya a yankin, mata masu ciki da jarirai na mutuwa daga cutukan da za a iya magancewa.
Kungiyar ta yi kira ga bangarorin su sasanta rikicin da ke tsakaninsu don kayan agaji da za su ceto rayuka su samu isa ga mutanen da suka rasa muhallansu.
Wakilin BBC ya ce MSF ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar an kawo ƙarshen wannan yaƙi, sannan bangarorin da suke yaƙi da juna su yi watsi da banbancin da ke tsakaninsu.

Asalin hoton, Reuters
Hare-hare ta sama da Isra'ila ke kaiawa share fage ne na yiwuwar kai samame ta ƙasa, in ji shugaban rundunar sojin ƙasar.
Da yake yi wa dakarunsa jawabi a yau Laraba, Herzi Halevi ya ce: "Kun ga jirage na yawo a saman kawunanku muna kai musu hari a kullum. Wannan shiri ne na yiwuwar kai hari ta ƙasa don karya lagon Hezbollah.
"A yau, Hezbolah ta ƙara nisan harinta, nan gaba a yau kuma za su fuskanci martani mai zafi. Ku shirya kawai.
"ZA mu ci gaba babu ƙaƙƙautawa, za mu ci gaba da ragargazarsu sosai a ko'ina. Manufarmu a fayyace take - ita ce mayar da mutane gidajensu a arewaci."
Ya ƙara da cewa "domin cim ma hakan", sojoji "na duba wani shiri da ke buƙatarku ku shiga ƙasar maƙiya, ku shiga ƙauyukan da Hezbollah ta gina manyan ofisoshin soji".

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa zai yi wa majalisar ministocinsa kwaskwarima nan gaba kaɗan, a cewar mai magana da yawunsa Bayo Onanuga.
"Shugaban ƙasa ya ce zai yi wa majalisarsa kwaskwarima. Ban sani ba ko zai yi hakan kafin 1 ga watan Oktoba amma dai tabbas zai yi [...] bai faɗa mana lokaci ba dai" in ji shi lokacin da yake magana da manema labarai a yau Laraba.
Mista Onanuga ya ce shugaban ya kuma umarci ministcin "da su daina jin kunyar yin magana da kafofin yaɗa labarai" domin tallata ayyukan gwamnatin.
A cewarsa: "Wasu daga cikinsu na gudun magana a talabijin, ko rediyo. Ya nemi su daina yin hakan, su fita su bayyana ayyukan da suke yi."
Babu tabbas game da dalilin da ya sa Tinubun zai yi sauyin a daidai wannan lokaci. Akasarin ministocin gwamnatin Muhammadu Buhari - wanda Tinubu ya gada - sun shafe kusan shekara takwas a kan mulki.

Asalin hoton, Ruth Ogunleye/Tiktok
Sojar da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta yi wa ritaya saboda rashin lafiya bayan ta zargi wasu manyan hafsoshi da cin zarafinta ta sake magantuwa.
A watan Janairu ne Ruth Ogunleye ta fito a shafinta na TikTok tana cewa ta sha wahala sanadiyar wasu manyan hafsoshin sojin rundunar.
Zargin nata ya haifar da cecekuce a lokacin, inda ministar mata ta shiga maganar, har ta zanta da babban hafsan soji a lokacin.
Bayan sanar da yi mata ritayar ce Ms Ogunleye ta sake fitowa a wani bidiyon a TikTok, inda ta ce tana so a wallafa sakamakon binciken a duka kafofin sada zumunta domin kowa ya gani.
"A ranar 9 ga Janairun 2024, na fito a kafofin sadarwa na yi ƙorafin cin zarafi da fyaɗen da aka yi mani. Da yadda aka nuna ni da bindiga, aka saka mani ankwa, aka ajiye ni a wani ofis na kwanaki. Ina roƙon rundunar sojin Najeriya ta bayyana sakamakon binciken da ta yi kowa ya gani," in ji ta.
A ranar Talata ne Janar Onyema Nwachukwu ya bayyana sakamakon binciken, inda ya ce sun gano wanda take zargi Kanal I.B. Abdulkareem bai aikata laifin ba, sannan ya ƙara da cewa an yanke shawarar yi mata ritaya ne domin rashin lafiya bayan ta ƙi amincewa a duba lafiyarta.
Amurka da Faransa na aiki kan daftarin tsagaita wuta a rikici tsakanin Hezbollah da Isra'ila a Lebanon, kamar yadda majiyoyi a Isra'ilar suka bayyana wa Reuters.
Daftarin ya ƙunshi yarjejeniya a arewaci domin mayar da mazauna Isra'ila gidajensu ta hanyar difilomasiyya, a cewar ɗaya daga cikin jami'an.
Sai dai kuma har yanzu babu cigaba da aka samu mai yawa game da hakan.

Asalin hoton, Reuters
Yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a faɗin Lebanon, rundunar tsaronta ta ce ta ƙaddamar da hare-hare 100 kan ƙungiyar Hezbollah.
Harin ya kai wani gari mai nisan kilomita 140 daga arewacin iyakar Lebanon da Isra'ila.
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce a yau Laraba mutum 23 sun mutu sannan 90 sun ji raunuka.
A farkon wannan rana Isra'ila ta daile wani makami mai linzami da Hezbollah ta harba zuwa birnin Tel Aviv a karon farko.
Kungiyar Hezbollah ta ce ta yi nufin kai wa hukumar leken asiri ta Mossad harin.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ɗage tafiyarsa zuwa New York sai ranar Alhamis, inda zai yi jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya.
Dabarar Isra'ila ita ce raunata Hezbollah ta yadda za ta daina harba rokoki arewacin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
An zargi ƴansandan Kenya da amfani da ƙarfi ya yin zanga-zangar da aka yi a harabar majalisar dokokin kasar ranar 25 ga watan yulin bana.
ƙungiyar kare hakkin ƴan Adam ta Amnesty International ta fidda rahoton da ya ce an kashe mutane biyar daga cikin masu zanga-zangar sannan ɗaruruwa sun jikkata a lokacin da ƴansanda suka harba harsashi.
Binciken wanda ya tattara shaidu daga wadanda al'amarin ya faru a gabansu da kuma bidiyo ya kuma yi zargin kame ba bisa ka'ida ba da cin zarafin ma'aikatan lafiya. To amma har yanzu mahukunta Kenya ba su ce komai game da zarge-zargen ba.
Wakilin BBC ya ce: Wakilin BBC ya ce rahoton ya yi zargin wasu jami'ai sanye da takunkumi cikin motoci marassa lamba sun budewa masu-zanga-zanga wuta.
Kungiyar Kare Hakkin Yan Adam din ta nemi a gudanar da sabon bincike game da kisan kan da ya faru lokacin zanga-zangar rashin amincewa da dokar karin kudaden haraji.

Asalin hoton, HQ NIGERIAN ARMY
Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewar hukumomin tsaro a jihar sun hallaka ɗaya daga cikin riƙaƙƙun ƴan bindigar da ke addabar jihar mai suna Kachalla Makore tare da yaransa.
Gwamnatin ta ce an hallaka ɗanbindigar ne dai a lokacin da ya ke hanyarsa ta ɗauko gawar wani riƙaƙƙen dan bindiga da aka halaka a baya-bayan nan Kachal sani black a yankin Dan Sadau.
HHakan dai ya biyo bayan matakin da rundunar sojin Najeriya ta ɗauka na samar da wata rundunar Fansar Yamma, a tsakanin jihohin Sokoto, da Kebbi da Zamfara da Katsina don kakkaɓe 'yanta'dda daga yankin.
Ko a kwanakin baya ma rundunar ta halaka gawurtacen ɗan bindigar nan da ya addabi jihohin Zamfara, Sokoto, Kastina da jihar Kaduna, Halilu Sububu, da karin wasu ’yan bindiga fiye da guda shida da suka addabi yankunan.

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima wanda ya wakilci shugaba Tinubu, a yayin jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nemi da a yafewa Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa basukan da ake bin su.
"...dole ne mu tabbatar cewa duk wani gyara da za a yi wa tsarin kuɗaɗe na duniya da suka haɗa da cikakken tsarin yafe bashi...domin ƙasashe ƙanana da masu tasowa ba za su iya samun cikakken cigaban tattalin arziƙi ba ba tare da yin duba da sake nazari kan irin nauyin bashin da ke kansu." In ji Kashim Shettima.
Sauran batutuwan da mataimakin shugaban ya taɓo a jawabin nasa sun haɗa da neman haɗin kan Majalisar Ɗinkin Duniya wajen ganin an mayar da kuɗaɗen sata da waɗanda aka fitar da su zuwa manyan ƙasashe ba bisa ƙa'ida ga ƙasashen da aka sato su.
Sanata Kashim Shettima ya kuma nemi zauren Majalisar da ya bai wa nahiyar Afirka da Najeriya gurbi a kwamitin tsaro na Majalisar ta Ɗinkin Duniya. >>>>>Cikakken labarin

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Real Madrid Kylian Mbappe zai yi jinya kamar yadda Real Madrid ta samar.
Ɗan kasar Faransa, wanda ya koma Real kan fara kakar bana daga Paris St Germain ya ci ƙwallo a La Liga da suka doke Deportivo Alaves 3-2 ranar Talata.
An sauya Mbappe daga karawar sauran minti 10 a tashi daga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Bayan da aka tashi daga wasan ne, Carlo Ancelotti ya sanar cewar yana cikin koshin lafiya, Mbappe ne ya bukaci a canje shi, saboda kada a samu matsala. >>>>> Cikakken labari.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Malaman Jami'a ta Najeriya, ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin mako biyu cewa za su tafi yajin aiki idan har ba a biya musu buƙatunsu ba.
Wannan dai na zuwa ne bayan ƙarewar wa'adin kwana 21 da ƙungiyar ta bayar a baya.
ASUU dai na son ganin an kammala zartar da batutuwan da ke cikin yarjejeniyar da ta cimma da gwamnatin tarayya ta 2009 da kuma biyan ƴaƴan ƙungiyar albashinsu na watanni takwas da aka riƙe musu saboda yajin aikin da ƙungiyar ta yi na kusan shekara guda.
Harwayau ƙungiyar ta ASUU na son ganin gwamnati ta inganta jami'o'in ƙasar da kuma biyan su alawus-alawus da aka sanya wani ɓangarensa a kasafin kuɗin shekarar 2023.
Sauran batutuwan sun haɗa damuwa da irin yadda ake samun ƙaruwar jami'o'i da batun tsarin biyan su albashi.

Asalin hoton, EPA
Fiye da mutum 430 ne suka mutu sakamakon annobar kolera a ƴan watannin da suka gabata, a daidai lokacin da yaƙin basasar ƙasar ke ci gaba a ƙasar, in ji ma'aikatar lafiyar ƙasar.
Alƙaluman waɗanda suka kamu da cutar sun ƙaru zuwa kusan 14,000 kamar yadda ma'aikatar lafiyar ƙasar ta sanar.
Sanarwar ta ce gwamnati na yin duk abin d aya kamata wajen "daƙile annobar a jihohin da annobar ta ɓarke."
Rikicin da ke wakana a Sudan ɗin na matuƙar shafar samar da magunguna ga waɗanda abin ya shafa. Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 150,000 tun bayan fara yaƙin a bara kamar yadda wakilin Amurka na musamman a Sudan, Tom Perriello ya sanar.
Likitocin ƙasa da ƙasa sun ce "suna samun matsala daga dukkannin ɓangarorin biyu masu yaƙi da juna, abin da ya sa ayyukan jinƙai suka gaza samun masu buƙata."
Ministan Lafiyar ƙasar, Haitham Mohammed Ibrahim ya ayyana ɓarekewar kolerar ne a tsakiyar watan Agusta.
Baya ga yaƙin da ake yi, ruwan sama da ambaliya da suka janyo cunkoso a sansanoni sun taimaka wajen ɓarkewar cutar ta kolera,
Esperanza Santos, jagoran ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa a Sudan ya ce "waɗannan abubuwa su ne suka haɗu suka haifar da annobar.
A wasu yankunan ma an umarci makarantu da kasuwanni da shaguna da su rufe domin daƙile yaɗuwar annobar.

Asalin hoton, Reuters
Yawaitar sacewa da kame da kuma uwa-uba kashe wani abokin hamayya a Tanzania ya ƙara dakushe tagomashin da aka fara samu a siyasar ƙasar bayan ɗarewa karagar mulki da Shugabar Kasa Samia Suluhu Hassan ta yi a shekarar 2021.
An yi farin ciki a lokacin da Samia - shugabar ƙasa mace ta farko a Tanzania - ta fara mulki, inda jam'iyyun adawa suka fara shirya tarukan siyasa suna kushe gwamnati ba tare da fargabar fuskantar wata matsala ba.
Amma yanzu alamu na nuna cewa an fara komawa gidan jiya tun bayan da wanda ya maye gurbinta, John Magafuli ya hau karagar mulki.
A cikin ƴan makonni, an kama wasu manyan ƴan hamayya guda biyu, sannan an sace wani ɗan hamayya, Ali Kibao, sannan aka kashe shi, inda aka tsinci gawarsa a gurɓace da alamun an watsa masa gubar acid.
"Yanayin da siyasar Tanzania ke ciki a yanzu akwai ɗaga hankali," in ji mataimakin shugaban babbar jam'iyyar Chadema, Tundu Lissu.
Ya bayyana wa BBC hakan ne mako ɗaya kafin a kama shi a ranar Litinin, lokacin da jam'iyyarsa ta yi yunƙurin shirya zanga-zanga a kan kashe Kibao da kuma zargin da suke yi na ɓacewar wasu masu adawa da gwamnatin.
Daga bisani an bayar da belin Lissu tare da wani jagora ajam'iyyarsu, Freeman Mbowe.
Jam'iyyar Chadema ta ce an kama tare da tsare sama da ƴan jam'iyyarta guda 100 saboda hana su shirya gangamin siyasa.

Asalin hoton, Reuters
An samu mutumin da ake tuhuma da yunƙurin kashe Donald Trump a inda yake buga ƙwallon golf a gidansa da ke Florida da laifin kisa.
Masu gabatar da ƙara a Amurka sun ce an samu Ryan Routh da laifin kai harin bindiga ta katangar gidan shaƙatawar ɗan takarar na jam'iyyar Republican a lokacin da yake wasa.
Sannan sun ce ya bar ƴar takarda ɗauke da bayanan manufarsa.
Ryan Routh kawo yanzu dai bai amsa laifin ba. Sai dai dama yana fuskantar tuhuma kan laifuka biyu da suka shafi amfani da bindiga.
Babban alƙali, Merrick Garland, ya ce Ma'aikatar Shari'a ba za ta raga wa duk wani mutumin da ya yi ƙoƙarin jefa dimokuraɗiyyar Amurka cikin haɗari ba.

Asalin hoton, AFP
Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce 'Hezbollah ce ke da nasara' kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a safiyar yau Laraba, wanda shi ne karo na farko da jagoran na addini ya fito ya yi magana a game da hare-haren Isra'ila a Lebanon.
Jawabin na Ayatollah Ali Khamenei na zuwa ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-cen Iran na goyo wa Hezbollah baya da tallafin kuɗaɗe da kayan yaƙi.
A jawabinsa a New York a ranar Litinin, shi ma Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce ba sa fatan ta'azzarar yaƙi a Gabas ta Tsakiya, inda ya ƙara da cewa ko yaƙin ya ƙazanta, babu ƙasar da za ta ci riba.
Shi ma shugaban kwamitin makamashin nukiiya na MDD, Rafael Grossi a zantawarsa da Reuters ya bayyana cewa ya ga alamar Iran ta shirya tattaunawa a game da shirinta na nukiliya, sannan ya ce zai ziyarci ƙasar a watan Oktoba.

Asalin hoton, Getty Images
China ta ce ta yi nasarar gwajin wani shu'umin makami mai linzami da ke tashi daga wata nahiya zuwa wata a yankin tekun Pacific.
Da safiyar yau Laraba ne aka yi wannan gwajin, lamarin da babu shaka zai haifar da damuwa tsakanin ƙasashen duniya musamman Amurka da ƙawayenta, kan habbakar harkokin nukiliyar ƙasar.
A wani saƙo da ba kasafai aka saba ganin irinsa ba, Ma'aikatar tsaron China ta ce makamin da a yanzu ba shi da wata illa, an yi gwajinsa ne kafin daga bisani ya faɗa cikin yankinsu na teku kuma ba wai an harba da niyyar fada wa wata ƙasa ba ne.
Sai dai babu cikakken bayanai kan takamaimai inda makamin ya fada har zuwa lokacin haɗa wannan labarin, ko idan ya haifar da wata barazana.

Asalin hoton, Getty Images
Masu jefa ƙuri'a a yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi sun fita rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu cikin uku na zaɓen da ake gudanarwa a yankin.
Ana gudanar da wannan zaɓe ne a tsakiyar Kashmir da kewaye ciki har da babban birnin ƙasar, Srinagar. Wakilin BBC ya bayyana cewa ya ga mutane sun tsaya kan layi, kuma an tsaurara matakan tsaro a rumfunan zaɓe, yayinda ake cikin yanayi na fargaba, sai dai mutane da dama a karon farko na son nunawa duniya inda suka karkata a zaɓensu na farko cikin kusan shekara 10.
Wannan kuma shi ne karo na farko da ake gudanar da wannan zaɓe tun bayan da gwamnatin Firaminista Nerandra Modi ta soke ƴanci da yankin ke da shi a 2019.