Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
To jama'a nan muka kawo karshen wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma yanzu, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
WHR na son a gudanar da bincike kan kisan jagoran adawar Chadi
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kare hakkin Bil-adama ta Human Rights Watch ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan jagoran adawar Chadi.
Yaya Dillo ya rasu a makon da ya gabata lokacin da jami'an tsaro suka kai farmaki shalkwatar jam'iyyarsa.
Kisan nsa na zuwa ne watanni gabanin zaben shugaban kasa da za a yi ciki watan Mayu kamar da shugabannin sojojin Chadi suka sanar. Inda ake sa ran Mista Dillo zai tsaya takara.
Kungiyar kare hakkin bil-adamar ta kara da cewa ta ga hoton jagoran adawar da raunin harbin bindiga a kansa. Jam'iyyarsa dai ta ce kashe shi aka yi.
Mista Dillo ya yi fice a sukar shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar, Mahamar Deby wanda ya sanar da cewar zai tsaya takara.
Atiku ya bukaci 'yan PDP a jihar Edo su kai zuciya nesa
Asalin hoton, Facebook/Atiku Abubakar
Bayanan hoto, Atiku Abubakar ne dan takarar PDP a zaben shugaban kasa da ya gabata
Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga fusatattun 'ya'yan jam'iyyarsa ta PDP a jihar Edo su kwantar da hankali tare da kai zuciya nesa.
Cikin wata sanarwa da Atikun ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya yi kira ga sauran 'yan takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyarsa da ba su samu nasara a zaben fitar da gwanin da aka yi a jihar, su mara wa Asue Ighodalo baya a zaben gwamnan jihar da ke tafe cikin watan Satumba.
Mista Ighodalo ne ya lashe zaben fitar da gwanin gwamnan jihar da Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar na kasa ya shirya cikin watan Fabrairu.
Yayin da mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da wani tsagin jam'iyyar ya gudanar.
Atiku Abubakar ya ce ya kamata sauran 'yan takara da mambobin jam'iyyar su sasanta kansu don yi wa jam'iyyar aiki.
“Dole ne mu taya - shugabancin jam'iyyar PDP da 'ya'yan jam'iyyar a jihar Edo - murna kan zaben fitar da gwanin da ya samar da ingantaccen mutum da zai yi takara karkashin tutar jam'iyyarmu a zaben gwamnan jihar da ke tafe,'' in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.
Ya kara da cewa “jam'iyya ta yi zabinta , kuma babu musu kan cewa zabin da ta yi ingantacce ne''.
''Kan haha ne nake kira ga duka sauran 'yan takara da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka fusata su kai zuciya nesa a sasanta da juna, don tabbatar da Edo ta ci gaba da zama jihar PDP''.
Jihar Edo na daga cikin jihohin kasar da jam'iyyar PDP ke mulkinsu, don haka a matsayinsa na madugun adawar kasar, dole ne Atiku ya yi duk mai yiwuwa don ganin jam'iyyar ta sasanta kanta, don kauce wa rasa jihar cikin jerin jihohin da jam'iyyar PDP ke iko da su.
AU ta yi Allah-wadai da hari kan Falasdinawan da ke layin karbar abinci
Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai ya yi kakkausar Allah-wadai kan abin da ya bayyana da kisan Falasdinawa masu yawa da ke kan layin karbar tallafi.
Mousa Faki Mahamat ya yi tir da harin da sojojin Isra'ila suka kai inda suka kashe tare da jikkata Falasdinawa fiye da 100 da ke jiran abincin da za su tsira da ransu a arewacin Zirin Gaza da aka mamaye.
A ranar Alhamis 29 ga watan Fabrairu ne aka kai harin a arewacin Gaza.
Cikin wata sanarwar da kungiyar AU ta fitar, ta yi kiran gaggauta gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda suka kashe fararen hula.
Zelensky ya nemi taimakon kasashen Yamma bayan harin Rasha a Odesa
Asalin hoton, Reuters
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi kira ga kasashen Yamma su kai wa kasarsa tallafin makaman kariya daga hare-hare ta sama bayan wani harin jirgi maras matuki ya kashe akalla mutum bakwai a birnin Odesa.
Mista Zelensky ya ce ''Rasha na ci gaba da kaddamar da yaki a kan fararen hula''.
Dakarun Ukraine na ci gaba da kare kasarsu, bayan da sojojin Rasha suka kwace iko da garin Avdiivka da ke gabashin kasar cikin watan da ya gabata.
A baya-bayan nan sojojin Rasha na samun nasara a Ukraine - wadda ke fama da matsalar karancin makamai.
Cikin wani sako da ministan cikin gida na kasar ya wallafa a shafinsa na Telegram, ya ce harin ya lalata wani gini mai hawatara a birnin Odesa.
Amurka ta kai tallafin abinci na farko ga mutanen Gaza
Asalin hoton, US CENTCOM
Amurka ta kai tallafin abinci na farko ga al'ummar Gaza ta jiragen sama.
Fiye da kulli 30,000 na abinci jiragen saman Amurka uku suka jefa wa al'ummar Gaza.
An gudanar da aikin rabon abincin tare da hadin gwiwar sojojin saman Jordan, kamar yadda rundunar sojin Amurka suka bayyana.
Jami'an Amurka sun ce abincin da aka rabar shi ne na farko daga cikin da yawa da shugaba Biden ya bayyana ranar Juma'a.
Shugaba Biden ya alkawarta kai agajin abinci zuwa Gaza, bayan da aka kashe sama da mutum 100 da ke dakon jiran agajin abincin tallfi ranar Alhamis
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar ta ce jiragen saman sun jega kullin abinci 38,000 a wani wuri a Zirin Gaza
A baya wasu kasashe irin su Birtaniya da Faransa da Masar da Jordan sun taba jefa wa al'ummar Gaza tallafin abinci ta sama, to sai dai wannan shi ne karon farko da Amurka ta yi hakan.
Kun taba sanin wani goro da ake kira goron Tula?
Goron Tula wani nau’in dan itace ne mai kama da kanya a ido sannan yana da kwallaye da kuma zaki kamar sukari.
Ana dai noma wannan nau’in goro a garin Tula da ke jihar Gombe.
Ana sayar da mudun goron Tula naira fiye da dubu 50, abin daya sa itacen ya zama abin alfahari ga al’ummar yankin.
A wannan bidiyo, manoman goron sun yi cikakken bayani dangane da muhimmancinsa da suka hada da gyaran gida ga ‘ya’ya maza.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Mahamat Deby ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban gwamnatin sojin Chadi, Mahamat Idris Deby ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da aka dade ana jira.
Cikin makon da ya gabata ne shugaban ya sanar da ranar 6 ga watan Mayu mai zuwa a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasar.
Yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa ranar Asabar, Mista Deby ya shaida musu cewa zai tsaya takara, inda ya ce ya ''karbi takardar tsayawa takarar''.
Hakan na zuwa ne kwana uku bayan mutuwar jagoran adawar kasar, Yaya Dillo, a lokacin wata arangama da jami'an tsaro a ofishin jam'iyyarsa da ke N'Djamena babban birnin kasar.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil-adama suka yi kira a gudanar da bincike game da kisan Dillo, wanda dan'uwa ne ga Mahamat Deby.
Janar Mahamat Deby ya hau karagar mulkin Chadi a shekarar 2021, bayan mutuwar mahaifinsa - wanda ya jagoranci kasar na tsawo shekara 30 - a wani gumurzu da 'yan tawaye.
An rantsar da Mahamat Deby - mai shekara 39 - a matsayin shugaban rikon kwarya a shekarar 2022. Inda ya alkawarta mayar da mulki hannun farar hula cikin wata 18, sai dai daga baya ya tsawaita wa'adin zuwa shekara biyu.
Ra'ayi Riga: Aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye
A farkon wannan makon ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye na shekarar 2012 da ya bayar da shawarar haɗe wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati waɗanda ayyukan su ke da alaƙa, a wani mataki na rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.
Gwamnatin ta rungumi wannan rahoton ne a ƙoƙarin sauya fasalin wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya duk da cewa hakan zai kunshi rusa wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati da kuma narke masu aiki iri ɗaya da juna a waje guda.
Shin mene ne cikakken bayani kan wannan rahoto?
Kuma ya hakan zai shafi ma'aikata da ma'aikatun da ake magana?
Sannan ya hakan zai taimakawa tattalin arzikin ƙasar?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirin ya tattauna a kai.
Bayanan sautiRa'ayi Riga
Lafiya Zinariya: Matsalar damuwa yayin ciki ko kuma bayan haihuwa
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Wasu iyaye a Mogadishu na neman adalci bayan kashe ɗansu
Asalin hoton, Facebook
Kafafen yaɗa labaru a Mogadishu, sun ce iyayen wani yaro na neman diyyar ɗansu wanda ake zargin sojoji sun kashe a mashigar Sinai da ke kusa da Masar.
Wasu shaidu da aka tattauna da su, sun ce wata mata ta kuma jikkata, inda suka ce sojoji sun buɗe wuta kan mutane da ke fita waje.
Mutanen sun ce suna son a cire ko kuma sauya wani jami'i a lardin Banadir wanda suke zargi da hannunsa a lamarin.
Iyayen yaron sun ce suna neman hakkinsu daga gwamnatin Somaliya.
Gane Mani Hanya tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Batun da yanzu haka yake ci gaba da yamutsa hazo a
kafafen sada zumunta shi ne na murabus daga shugabancin hukumar Hizba ta Kano
da Sheikh Aminu Daurawa ya yi a jiya Juma’a.
Da safiyar Juma’ar ne dai Sheikh Daurawa, a wani sakon
bidiyo a shafinsa na Facebook, ya sanar da ajiye mukamin nasa wanda hakan ba ya
rasa nasaba da wani jawabi da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi
dangane da ayyukan rundunar ta Hizba.
To kafin dai wannan murabus, BBC ta tattauna da malam
Aminu Daurawa dangane da ayyukan Hizbar da ma abubuwan da ake zargin dakarun
hukumar da aikatawa.
A hirarsa da Madina Maishanu, Sheikh Daurawa ya fara da
bayani kan ayyukan rundunar ta Hizba.
Bayanan sautiLatsa sama don sauraron tattaunawar
Hukumomin lafiya sun farfaɗo da jami'an sa-ido kan masu zazzaɓin lassa a Kano
Hukumomin lafiya a jihar Kano sun farfaɗo da ayarin jami'an bin diddigi da sa-ido kan masu
larurar zazzaɓin lassa a jihar, a wani mataki na riga-kafi.
Wannan na zuwa ne yayin da a jihar Kaduna mai
makwaftaka aka samu rahoton mutuwar mutum shida sanadiyyar zazzaɓin lassa.
Dr
Abubakar Labaran Yusuf shi ne kwamishinan lafiya na jihar, ga kuma ƙarin bayani da ya yi wa
Zahraddeen Lawan.
Bayanan sautiLatsa sama don sauraron tattaunawar
Ƴan tawayen Colombia sun saki mutum 26 da suka yi garkuwa da su
Ƙungiyar 'yan tawaye ɗaya
tilo da ta rage a Colombia, wato ELN ta saki mutuane 26 da tai garkuwa da su a
wani ɓangare na sasantawar da suke yi da gwamnati.
Cikin waɗanda suka shaki
iskar 'yanci har da wasu ɗalibai da aka sace a wurin binciken ababen hawa tare
da buƙatar kuɗin fansa.
A wata
sanarwa da ELN ta fitar, ta ce matakin wani ɓangare ne na shirin da suke yi na tsagaita ayyukansu,
bayan zama sulhu da gwamnati a ƙasar Cuba a bara.
Ƙungiyar 'yan tawayen ta
shafe sama da shekaru 10 ta na ta da kayar-baya a Colombia, kafin daga bisani
shugaba Gustavo Pedro wanda tsohon ɗan wata ƙungiyar 'yan tawayen ƙasar ne ya
amince da hawa teburin sulhu da su.
Sojojin Ukraine sun ce sun sake kakkaɓo jirgin saman Rasha
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin saman Ukraine ta ce ta sake harbo wani jirgin saman Rasha Su-34, lokacin da jirgin ke ƙoƙarin harba bama-bamai a wasu yankunan ƙasar.
A cewar sojojin ƙasar ta Ukraine, sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, 1 ga watan Maris.
An ruwaito cewa wannan shi ne jirgin saman Rasha mai suna Su-34 na shida da sojojin Ukaraine suka kakkaɓo a makon nan.
Sojojin Ukraine ɗin sun yi iƙirarin cewa sun harbo jiragen yaƙin Rasha 13 a cikin makonni biyu a kacal a cikin watan Febrairu, sama da wanda suka yi a watannin baya na yaƙin.
Muna fatan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza kafin fara azumi - Biden
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana fatan ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a daidai lokacin da ake shirin shiga watan Ramadan.
Ana sa ran cewa watan na Ramadana mai alfarma, zai fara ne a ranar 10 ko 11 ga Maris.
Da aka tambaye shi ko yana sa ran cimma yarjejeniya a lokacin, Mista Biden ya ce: "Ina fatan haka. Har yanzu muna aiki tukuru a kan hakan."
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawa kan tsagaita wuta da kuma ƙara matsin lamba ga Mista Biden da ya taimaka wajen kawo karshen rikicin.
Yarjejeniyar da aka tsara, za ta dakatar da ayyukan soji na tsawon kwanaki 40 tun daga farkon watan Ramadan sannan kuma za a ƙara kai kayan agaji zuwa Gaza, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
An kuma bayar da rahoton cewa yarjejeniyar ta kunshi sakin fursunoni Falasɗinawa da kuma sakin Isra'ilawan da ake garkuwa da su.
An kama ƴar bautar ƙasa ta bogi a sansanin horaswa a Nasarawa
Asalin hoton, NYSC
Rundunar ‘yan
sandan jihar Nasarawa ta kama wata ƴar bautar ƙasa ta bogi mai suna Ogeh Bethel
Chibuife bisa laifin shiga sansanin horaswa na Magaji Dan Yumusa da ke
Keffi, babban birnin jihar ba bisa ka’ida ba.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan Ramhan Nansel ya fitar, inda ya ce wadda ake zargin ta zo ne daga jami'ar jihar Ebonyi.
Nansel ya ce
wadda ake zargin, wanda daliɓar ƙarin shekara ne daga
Jami’ar Jihar Ebonyi, ta sulale ta shiga sansanin horaswa na NYSC wanda ake ɗaukar kwanaki 21 ana yi, da nufin samun horo a rukunin A, kashi na farko na 2024, inda daga bisani aka gano ta.
Ya ce wani
jami’in NYSC ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a ranar Lahadi, kuma
jami’an rundunar ne suka kama ta.
"Ta faɗa cewa a shekarar 2022 ya kamata ta kammala karatunta, ammasai ta faɗi wasu kwasa-kwasa, kuma a ƙoƙarinta na ɓoye karyar da ta
yi wa iyayenta, ta je kasuwa ta siyo rigar kayan bautar ƙasa. Bayan ta sulale ta shiga cikin sansanin don ɗaukar hotuna ta aika wa
iyayenta kafin aka kama ta," in ji shi.
Kamfanonin harhaɗa magunguna a Amurka za su fara sayar da maganin zubar da ciki
Asalin hoton, Getty Images
Biyu daga cikin manyan
kamfanonin harhaɗa magunguna a Amurka sun sanar da fara sayar da maganin zub da
ciki nau'in mife-pristone ga waɗanda suka kawo shaidar likita.
CVS da Walgreens, sun ce za
su fara hakan a mako mai zuwa a jihohin Amurka da aka halastawa mata zubar da jiki.
Tun a
shekara ta 2000 aka amince da sayar da magungunan zub da ciki a Amurka, kuma har
yanzu ana irin magungunan a manya da ƙananan asibitoci.
Shugaba Joe Biden ya yi
maraba da hakan, inda ya ce gagarumin ci gaba ne ga masu gangamin tabbatar da
hakan.
Mutane da dama sun jikkata yayin karɓar kayan agaji a Gaza - MDD
Asalin hoton, Reuters
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tawagar da ta
aike Gaza, ta gano mutane da dama da suka jikkata a Gaza, yayin da Isra’ila ta
amsa cewa dakarunta sun bude wuta ga dandazon Falasɗinawa da suka dabaibaye
ayarin kayan agaji saboda dalilai na tsaro.
Mai magana da yawun sakataren MDD ya bayyana, cewa likitocin da suka kai
ziyara asibitin Al-Shifa, sun ga Falasɗinawan da suka jikkata a lokacin da suka
je karɓar kayan agajin, inda aka kai mutum sama da 700 da suka ji rauni da kuma gawawwaki 70 asibitin Al-Shifa.
Shugabannin ƙasashen duniya sun
buƙaci a gudanar da bincike tare da kiran tsagaita wuta ta wata
biyar a yakin Gaza.
Buɗewa
Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da safiyar Asabar.
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.
Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.