Europa League: Yadda zata kaya tsakanin Barcelona da Napoli a Camp Nou

Osimhen
An wallafa

Barcelona za ta karbi bakunci Napoli a filin wasa na Camp Nou idan anjima kadan.

Shine daya daga cikin wasanni gasar zakarun turai ta Europa da yafi jan hankalin masoya kwallon kafa, lura da kalubalen da kungiyar ke fuskanta a baya-bayan nan.

A bagaren masu masaukin bakin akwai manyan yan wasa da ke jinya, da suka hada da yan wasan gabanta Ansu Fati da Memphis Depay da kuma Sergio Roberto.

A baya kuma Samuel Umtiti da Clement Lenglet suma ba za su samu buga wasan ba.

Sai dai dama a watan Janairu Barcelona ta yi cinikin dan wasan gaban Gabon daga Arsenal wato Aubameyang, da kuma Traore daga Wolverhampton.

Sai dai suma bakin na da yan wasa hudu da ke jinya, to amma sun samu karin karfi da dawowar dan wasan gaban Najeriya Victor Osimhen.

A karawa 10 da suka yi a baya Napoli ce tafi cin Barcelona, inda ta lashe wasa uku, yayin da Barca ta ci biyu aka yi canjaras biyar.

Barcelona ta fara farfadowa tun bayan kawo tsohon dan wasanta Xavi a matsayin koci.

Xavi

A karon farko FC Barcelona na neman lashe kofin da bata taba lashewa ba tun da aka kafa kungiyar.

Kuma ta tsinci kanta a gasar ta Europa ne bayan da Bayern Munich ta lallasa ta da ci 3-0 a wasan ƙarshe na rukuni a Champions League a watan Disamba da ya gabata.

To amma tana fuskantar bashi da ya yi mata katutu, duk da hakan bai hana ta shiga kasuwa don kawo sabbin yan wasa ba a bana.

A sauran wasanni Borussia Dortmund na Glasgow don karawa da Rangers, sai kuma FC Porto da zata karbi bakuncin Lazio.

Akwai kuma wasan RB Leipzig da Real Sociedad, Atalanta da Olympiacos Piraeus, Sevilla da Dinamo Zagreb, da kuma wanda za a kece reni tsakanin Zenit Saint Petersburg da Real Betis.