Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Wainar da ake shirin toyawa tsakanin Inter da Liverpool a San siro
`
Idan anjima ne za a kece reni a filin San siro tsakanin Inter Milan da Liverpool a zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun turai, a wani wasa da masu sharhi ke kallon cewa da wahala a iya cewa ga wanda zai ci nan take.
Da farko dai Inter na wasa ne a gida, kuma wani abin dubawa shine hukumar shirya wasanni ta UEFA ta soke damar da a baya ake amfani da ita ta fito wa zagayen gaba da kwallon waje wato 'away goal' kenan.
Hakan na nufin duro ba zai fidda kowa ba, sai wanda ya fi cin kwallaye ne zai fito.
Duka kungiyoyin biyu suna kokari a kofunan cikin gida, kuma suna da zakakuran yan wasa da za su iya fidda su kunya a wasan na yau.
Yayin da Liverpool ke shirin bai wa Inter Milan matsala ta hannun Mohamed Salah da Sadio Mane, masu masaukin bakin na da Eden Dzeko a gaba da kuma Arturo Vidal a tsakiyarsu.
A kan haka masu sharhi ke ganin akwai yaki tsakanin Dzeko da Virgil van Dijk, lura da kyawon da Dzeko yake dashi a sama.
Amma kuma sai Inter sun yi kamar suna yi kafin su iya rike Salah da Mane, sannan su hana kwallo tashi daga tsakiya.
Hakama a gaban masu masaukin bakin akwai Lautaro Martinez, wanda hadin shi da Dzeko ga kuma Sanchez zasu iya bai wa masu tsaron bayan Liverpool Van Djik da Matip matsala.
Kazalika masu horar da kungiyoyin wato Simone Inzaghi da Jurgen Klopp sun fahimci yan wasansu sosai, wanda yasa ake ganin sun shirya amfani da dabarun samun galaba kan juna a wasan na yau.
Inzaghi ya karbi Inter hannun Antonio Conte wanda yanzu ke Tottenham, kuma ta lashe kofin Scudetto bara sannan ita ke saman tebur a bana.
A daya bangaren kuwa Liverpool na bin bayan Manchester City ne a teburin Firimiyar Ingila.
Saboda haka za a iya cewa wasa ne tsakanin kungiyoyi biyu tsarar juna, kuma abu ne mai wahala a iya hasashen wanda zai cinye wasan kai tsaye.
A daya wasan na yau Red Bull Salzburg ce za ta karbi bakuncin Bayern Munich a Austria.
Sai dai an fi tunanin Bayern Munich ce za ta zama zakara a wasan, la'akari da babakeren da ta yi a gasar Bundesliga ta Jamus da kuma karfin tawagarta.