Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kane, Vlahovic, Sanches, Asensio, Haaland, Trippier, Coutinho

Asalin hoton, Reuters
Manchester City a shirye take ta fitar da fam miliyan 150 domin sayen dan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 28, inda majiyoyi ke cewa, hakan ka iya sa Tottenham da shugabanta Daniel Levy su yarda a fara tattaunadwa kan cinkin kyaftin din na ingila. (Jaridar Independent)
Idan Manchester City ta kasa samun Kane a bazaran nan, an ce zakarun na Premier za su duba yuwuwar sayen dan wasan Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 21, a madadinsa. An ce Cityn ta shiga cikin masu zawarcin dan gaban na Fiorentina a kan euro miliyan 80. (Jaridar Firenze Viola)

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta gamu da cikas a yunkurinta na neman sayen dan wasan tsakiya na Lille Renato Sanches, inda dan Portugal din mai shekara 24 ya ji raunin da zai yi jinyar sati shida. (Jaridar Mirror)
Kila Arsenal ta fito da fam miliyan 34 daga lalitarta domin sayen gwanin dan wasan Real Madrid Marco Asensio, mai shekara 25. (Jaridar Fichajes )
Tottenham ta kara bayyana aniyarta ta sayen dan bayan Serbia Nikola Milenkovic bayan da West Ham ta yanke shawarar fasa sayen dan wasan na Fiorentina mai shekara 23. (Jaridar The Times)
Mai yuwuwa dan gaban Masar Mohamed Salah, mai shekara 29, ya samu kansa cikin dambarwar kwantiragi mai tsawo da kungiyarsa ta Liverpool. (Jaridar Times)

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle ta sanya farashin fam miliyan 10 a kan dan wasan tsakiya na Ingila Sean Longstaff. Kwantiragin dan wasan mai shekara 23 a St James' Park zai kare a bazara mai zuwa, kuma an ce kociyan Everton Rafa Benitez na saha'awar daukarsa zuwa Goodison Park. (Jaridar Mail)
An sheda wa Arsenal da Manchester United su manta da maganar neman sayen dan bayan Atletico Madrid, Kieran Trippier, dan Ingila mai shekara 30. (AS)

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Everton ta samu sayen dan gaban Schalke Matthew Hoppe a kan kasa da fam miliyan bakwai da kungiyar Ba'amurken ta sa a kansa, saboda matsalar kudi da kungiyar ta Jamus ke ciki. Everton na daya daga cikin kungiyoyin da ke sha'awar dan wasan mai shekara 20, kuma ana ganin idan ta taya shi fam miliyan hudu za ta iya samunsa. (Jaridar Bild)
Liverpool ta zama ta gaba-gaba a fafutukar da kungiyoyi ke yi ta janye dan wasan gaban Borussia Dortmund na Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21. (Sport1)
Watford ta yi watsi da tayin fam miliyan biyar da Crystal Palace ta yi wad an wasanta na tsakiya Will Hughes, dan Ingila mai shekara 26. (Jaridar Sun)
Dan gaban Wales Gareth Bale, mai shekara 32, ya sake samun kwanciyar hankali a Real Madrid bayan sake haduwarsa da Carlo Ancelotti, bayan da kociyan kungiyar na baya Zinedine Zidane ya yi watsi da shi. (Marca )

Asalin hoton, FAW
Leeds United ta yi yunkuri da dama na ganin ta sayi dan bayan Celtic Matthew Anderson, a bazaran nan, amma kuma kungiyar matsashin na Scotland mai shekara 17 ta yi ta watsi da bukatar. Amma kuma har yanzu Leeds din na kokarin dauko abokin wasansa a kungiya, shi ma dan baya, Leo Hjelde dan Norway mai shekara 17. (Yorkshire Evening Post)
Juventus ta yi nasasar doke Liverpool da Tottenham a sayen matashin dan wasan Brazil Kaio Jorge, mai shekara 19, daga Santos. (Goal)

Asalin hoton, Reuters
Har yanzu Manchester United na duba yuwuwar sayen wani dan wasan tsakiya. Amma kuma duk wani da za ta saya, sai ta sayar da wani ko wasu 'yan wasan sannan ta samu kudin saboda, sayo Raphael Varane, mai shekara 28, da kuma dan Ingila, Jadon Sancho, mai shekara 21 da ta yi. (Manchester Evening News)
Tsohon tauraron dan wasan Newcastle da Chelsea Demba Ba, mai shekara 36, ya bar kungiyar Lugano, ta Switzerland, inda dan Senegal din ya yi mata wasan minti 48 kawai. (talkSPORT)
Barcelona na fatan samun karin euro miliyan 200 ta rage bashin da yake kanta ta hanyar sayar da
Dan Faransa Samuel Umtiti da Philippe Coutinho, na Brazil mai shekara 29 da kuma dan Bosnia Miralem Pjanic, mai shekara 31. (Goal)
Dan wasan tsakiya Joe Willock, dan Ingila mai shekara 21, na fatan kawar da tarihin da Alan Shearer ya kafa na cin kwallo a jere, a karo na biyu na fara yi wa Newcastle wasa a karawa da Aston Villa a karshen makon nan. (Mirror)



























