Masar ta zargi Habasha da karya doka kan madatsar ruwan da suke takaddama a kanta

An wallafa

Masar ta zargi kasar Habasha da karya dokokin kasashen duniya bayan samun rahoto cewa kasar tana sake cika kogin Nilu da ruwa a shekara ta biyu a jere.

Batun cika madatsar ruwan ya dade yana janyo tashin hankali tsakanin kasashen biyu.

Ga Masar, ta dogara ne baki daya kan kogin na Nilu wajen samun ruwan da al'ummar kasar ke amfani da shi, don haka take kallon lamarin na makwabciyarta a matsayin babbar barazana.

An dauki gwamman shekaru ana tattaunawa kan madatsar ruwan amma ba a cimma matsaya ba.

Kokarin da kungiyar Tarayyar Afirka ta yi a baya-bayan nan na sulhunta rikicin bai yi tasiri ba, a yanzu kasashen Masar da Sudan - wadda ita ma take amfana da ruwan - sun bukaci kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya shiga lamarin.

Suna son daukar mataki kan lokacin cike madatsar ruwan, da yawan ruwan da Habasha za ta rika saki.

Masar ta ce an shaida mata cewa an fara aikin cike dam din na shekara ta biyu. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da damuna ta kankama a kusa da madatsar ruwan.

A martanin da Masar ta mayar ta bakin ministan noman rani, Mohammed Abdel Ati, ya ce ya aika wa takwaransa na Habasha wasika tare da jaddada cewa Masar ba ta amince da matakin da kasar ke dauka ba.

Ya kara da cewa matakin ya keta yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015, wadda ta tanadi cewa aikin cike madatsar ruwa zai faru ne idan dukkan kasashen da lamarin ya shafa sun fahimci juna.

Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya rawaito ita ma Sudan tana cewa Habasha ta sanar da ita kan wannan batu.

"Sun aiko da wata banzar wasika," kamar yadda aka ambato babban mai shiga tsakani, Mustafa Hussein, yana cewa.

Gabanin taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a ranar Alhamis, Ministocin harkokin wajen kasashen da ke birnin New York, sun kira matakin kasar Habasha da "mummunan lamari da ya nuna mummunar manufar kasar".

Sun kara da cewa "Cike madatsar ruwan a karo na biyu ya saba wa dokar da aka gindaya tun da fari." Sai dai Habasha ta kare kanta cewa ba wai da gangan take aikin ba.

"Cike madatsar ruwan na tafiya ne da aikin da ake yi, don haka ba da gangan muke yi ba," kamar yadda wani babban jami'i a ma'aikatar ruwan Habasha ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ana fatan da zarar an kammala aikin madatsar ruwan baki daya, al'ummar Habasha miliyan 65 za su samu ingantacciyar wutar lantarki.

Hukumomi sun ce hakan zai inganta rayuwar 'yan kasar Habasha da bunkasa kasar baki daya.

A wata wasika da ma'aikatar harkokin wajen Habasha ta aike wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata, ta bayyana aniyarta ta daukar wasu matakan difilomasiyya a kusa da madatsar ruwan.

Ta zargi kungiyar kasashen Larabawa, wadda ta bayyana karara tana goyon bayan kasashen Sudan da Masar, da rura wutar rikicin. Habasha ta kara da cewa lamarin na kungiyar Tarayyar Afirka ne ba na kungiyar Larabawa ba.