Tasirin yajin aikin masu safarar abinci zuwa kudu kan farashin kayayyaki
An wallafa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Yajin aikin haɗaɗɗiyar Kungiyar masu kayan gwari da cimaka ta ƙasa ya haifar da tsadar farashin kayayyakin musamman kayan abinci da dabbobi a kudancin Najeriya.
An nuna wa BBC wani Rago da farashinsa ya kai naira miliyan ɗaya, wani kuma ya kai naira dubu 800.
Tun a makon jiya ne ƴan kasuwar da ke kai kayan abinci kudancin Najeriya daga yankin arewaci suka fara yajin aikin.
Sun shiga yajin aikin ne domin nuna goyon baya ga ƴan uwansu mutanen arewa da rikicin kasuwar Sasa ya shafa a garin Ibadan na jihar Oyo.
Yanzu yajin aikin ya yi tasiri bayan haifar da tsadar farashin kayayyakin abinci a yankin kudu maso yammacin Najeriya.