Mourinho ya tsawaita zamansa a United

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya tsawaita zamansa a kungiyar har zuwa 2020.
Kwantiragin da kocin ya saka wa hannu ta baya za ta kare ne a 2019.
Mourinho ya ce,"Ina jin dadin yadda United ta gamsu cewa ni ne kocin da ya dace da horar da wannan babban kulob wajen samar masa da kyakkyawar makoma".
A watan Mayun 2016 ne dan kasar Portugal din ya karbi aikin horarwar kungiyar daga hannun Louis Van Gaal, inda ya lashe kofin EFL da na Europa a kakarsa ta farko.
Yanzu dai United ce ta biyu a teburin Firimiya, inda take bin bayan ta farko a teburin Manchester City, kuma kungiyar na cikin gasar zakarun Turai da na FA.
"Muna kirkiro hanyoyin da za su kai kungiyar ga gaci, da kuma samar mata da kyakkyawar makoma. Ina son 'yan wasana, kuma zan so mu kasance da su a kalla shekara uku masu zuwa, in ji kocin.





















