'Shan garin kwaki yana kawo cutar zazzabin Lassa'

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Anambra da ke kudancin Najeriya ta haramta shan danyen garin kwaki, wanda a cewar ta yana jawo zazzabin Lassa.
Hukjumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce cutar Lassa na yaduwa ne ga 'yan adam ta hanyar abinci da wasu abubuwan da fitsari ko najasa suka taba.
Garin kwaki wani nau'in abinci ne da ake yin sa daga rogo a Najeriya, wanda ake ci ta hanyar tuka shi ko kwadonsa ko a sha shi da ruwa.
Idan aka dafa shi da kyau kwayoyin cutar Lassa din na mutuwa.
Amma da yawan 'yan Najeriya na shan sa danye.
Kwamishinan Lafiya na jihar Anambra Dr Joe Akabuike, ya ce: "Irin garin da ake shanyawa a kan titi yana da matukar illa kuma shan sa na da hadari.
Ya ce yawanci irin wannan garin kwakin gurbatacce ne.
Ana ta samun karuwar yaduwar zazzabin cutar Lassa a fadin Najeriya.
A ranar Lahadi ma wani likita ya mutu a jihar Edo bayan da ya kamu da cutar daga wani yaro mai dauke da ita.




























