Bayanan hoto, Farfajiyar filin wasa na kasa da ke Abuja wato National Stadiuum yana karbar bakuncin wasannin gogaggun 'yan wasa da 'yan koyo
An wallafa
Bayanan hoto, Masu makarantun koyar da kwallon kafa na zuwa atisaye a filin wasan kwallon kafar na kasa da ke Abuja
Bayanan hoto, BBC ta kai ziyara filin domin ta ga wasu dag cikin 'yan makarantan da ke koyon tamola a filin wasan
Bayanan hoto, Kwalejin horar da kwallon kafa ta Abuja na daya daga cikin makarantun horar da 'yan wasa da ake da su a Najeriya, inda ake koya wa yaran dabarun kwallo kafa da kuma horar da su, burin 'yan wasan dai shi ne su zama manyan 'yan kwallo da zasu taka leda a kasar da kuma kasashen Turai.
Bayanan hoto, Atisayen wasu matasan 'yan wasa ke nan na makarantar koyon dabarun kwallon kafa ta Football College Abuja a filin wasa na kasa, wato "National stadium".
Bayanan hoto, Wannan makaranta dai na alfahari da cewa wasu daga cikin dalibanta suna buga wasa a wasu kungiyoyin kwallon kafa na Turai, kamar yadda mataimakin mai horar da 'yan wasa, kuma daya daga cikin masu horar da 'yan wasa na makarantar, Coach Ibrahim
Bayanan hoto, Ma'aikatan BBC ma sun dauki lokaci suna kalon yadda yaran suke taka leda kamar sauran masu sha'awar kwallon kafa
Bayanan hoto, Matasan 'yan kwallon na baje kolin basirar da Allah ya ba su
Bayanan hoto, Burinsu dai shi ne su zama manyan 'yan kwallo domin su taka wa kasarsu leda da kuma tafiya kasashen Turai domin su taka leda a can.
Bayanan hoto, Matasan na baje kolin basirar da Allah ya ba su da kuma jajircewa da dagewa a kan cika burinsu na kwallon kafa.
Bayanan hoto, Kullum da safe suna zuwa domin yin atisaye, da farko suna shiga aji ne su fara daukar darasi daga karfe bakwai zuwa tara na safe, daga bisani kuma su shiga fili su yi abin da aka koya musu a aikace