Yadda matan Afghanistan ke rayuwa bayan karbe iko da Taliban ta yi

"Alkalamin rubutuna, yana kamar fukafuken tsunsu ne; zai iya fada maka abubuwan da ba za a bari mu yi tunani a kai ba da kuma mafarkin da ba za a bar mu muyi ba.’’
A yawan lokuta, muryoyin matan Afghanistan na fitowa ne daga titunan Kabul da wasu birane idan suka fito zanga-zanga. So tari, suna ana jin muryoyin mata ne wadanda a yanzu suke wajen Afghanistan.
Sai dai, yawanci basa iya fitowa su bayyana bukatunsu, inda suke bari a zuciyoyinsu.
A wasu lokutan kuma, su kan yi amfani da alkalamin rubutu ko ma wayoyinsu wajen bayyana ra’ayinsu yayin da suke ci gaba kokarin sabawa da tsauraran dokokin ‘yan Taliban a ƙasar.
Sun takaita irin tufafin da mata za su saka da wajen da za su yi aiki da abin da za su yi da abin da ba za su yi ba da rayuwarsu.
'Yan Taliban na ta fitowa da doka bayan doka wadanda suke sanya wa mata.
Watanni kalilan kafin dawowar mulkin Taliban a watan Agustan 2021, matan Afghanistan guda 24, sun rubuta labarai kan abubuwan da suka faru a zahiri wadanda kuma aka wallafa a cikin wata takarda mai suna ''My Pen is the Wing of a Bird’' a farkon wannan shekara.
Yawancin matan Afghanistan sun bayyana cewa al’ummomin ƙasashen waje sun barsu su kadai, amma marubutan sun yi amfani da alkalaminsu wajen karfafawa sauran ‘yan uwansu mata da yin rubutu kan abubuwan da miliyoyin ‘ya’ya da mata ke fuskanta tun da dawowar mulkin Taliban.
A nan, wasu marubuta biyu a Kabul masu suna Paranda da Sadaf, sun bayyana ra’ayoyinsu.
Kwarin gwiwa

"A yau na tashi da zimma. Bayan da na zabi tufafina, na yanke shawarar sanya nikabi mai ruwan hoda domin yaƙi da bakin nikabi da nake sakawa a kullum...laifi ne saka nikabi mai ruwan hoda?’’
Paranda tafi so ta saka nikabi mai ruwan hoda, domin hakan na nuna mai fafutukar kare hakkin mata. Sai dai, abin da mata za su saka ya zama matsala a yanzu. Taliban ta sanya tsauraran dokoki kan tufafin da mata ke sakawa.
A wannan zamani na yau, ba matan Afghanistan na yaƙi da abin rufe kai bane – illa kawai suna so a basu damar zabar abin da za su sanya.
Za ka iya ganin matan da suka saka nikabi mai ruwan hoda a kan tituna da kuma wuraren taron jama’a.
Kiraye-kirayen sauyi
"Koma wa baya ba abu ne mai sauki ba. Sannan ci gaba ma na cike da babban ƙalubale, shin ya kamata na yi fata ko a’a? Ba za mu koma baya ba.’’ A cewar wata marubuciya Hafizullah Hamim.
Matan Afghanistan na jagorantan bukatar neman sauyi a cikin zanga-zangar da ba a saba gani ba. Wasu dandazo na mata, sun fita kan titunan Kabul da wasu birane rike da alluna da fostoci, inda suke kira kan ‘yanci da kuma aiki.’’ Sai dai, an tarwasa su da karfin tuwo da kuma tsare wasu, inda wasu kuma suka bace yayin tsare su da aka yi.
A kan iyaka, a ƙasar Iran ma, matan ne ke jagrorantar kiraye-kirayen neman sauyi, inda suke magana a kan ‘yancin mata da kyakkyawar rayuwa da kuma buƙatar kawo ƙarshen wajibcin sanya hijabi.
A Afghanistan, hakki ne na barin mata su yi aiki, ‘ya’ya mata kuma su samu ilimi.
Wahala a shingayen bincike

''Wani jami’in tsaron Afghanistan ya tare motar mu yayin zuwa aiki, yan una ni…zuciyata ta yi bugawa da sauri, jikina kuma na rawa. Ji na yi kamar iska na kaɗawa a gefena…lokacin da motar mu ta tashi, kamar iskar ta tafi zuwa wani wuri. Tsorona sai ya koma fushi.’’
Babbar matsalar ita ce baka san me zai faru ba. Wasu jami’an tsaron Taliban basa yi wa mutane da daɗi, yayin da wasu kuma basu da matsala. Tafiye-tafiye da mata ke yi na cike da wahalhalu.
Idan za su yi tafiya mai nisan kilomita 72, wajibi ne su nemi muharrami. Taliban na saka dokoki a duk lokacin da suke so – inda suke kora mata gida a duk lokacin da suke so.
Bukatar jindadi

''Jindadi da ke tattare da shan ice cream ga yara kwatankwacin yadda mata ke ji lokacin da suke yin tafiye-tafiye.’’
So tari, za ka ga dogayen layuka na mata da ƙananan yara a shagunan sayar da ice cream.
Wuraren sun zama waje da mata suke zuwa domin shakatawa. Sai dai, a yanzu, hatta wuraren shakatawa da ma wuraren motsa jiki na mata da yin wanka ba a barin su suje,’’ saboda matan basa saka hijabi’’,wanda yana cikin dokoki da Taliban ta kafa.
A karo na biyu

"An bayar da baikon ɗiyar mai gidan wanka...abin mamaki, tana da shekara 13. Mahaifiyarta ta ce Taliban ba za su sake buɗe makaranta ba, su bar ta ta tafi gidanta da sa’a, bayan fidda rai a karon farko da zuwan ‘yan Taliban.
Ni ma na amince da auren dole...har yanzu ina jin raɗaɗi. Amma na manta duk abin da ya faru, inda yanzu na fuskanci rayuwa.
Matan Afghanistan na tunawa da irin raɗaɗi da suka fuskanta lokacin da Taliban ta yi mulki a 1990 wanda ya kawo ƙarshen buƙatarsu na yin karatu.
Paranda kamar sauran mutane, sun yi amfani da damarmaki lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Taliban a shekara ta 2001 – kamar zuwa makaranta ko samun saki.
''Yan mata masu zuwa makaranta sun girma tare da mafarkai da dama. Sun ji takaici lokacin da aka kulle makarantu.
Iyakokin da maza suka saka

"Na yi amfani da kafofin sada zumunta, amma a aynzu na rufe bakina. Ina cike da raɗaɗi kan irin munanan kalamai da maza ke amfani da su kan mata.
Ina da yaƙinin cewa matsalolin matan Afghanistan ba wai gwamnati bane da ta canja tare da kawo sabbin dokoki...illa gani mara kyawu da maza ke yi wa mata.''
Gwamnatoci a Afghanistan na zuwa kuma suna tafiya, sai dai mamayar da maza suka yi tana nan.
Matan Afghanistan suna rayuwa da irin iyakoki da maza suka gindaya. Amma ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan – tare da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin ‘danniya mai ban mamaki.''
Kalaman mata

"Dole ne in rubuta game da abin da ke faruwa. Babu kafofin ƴada labarai da yawa a yanzu...Na yi imanin cewa, watarana, Afghanistan za ta zama ƙasa mai kyau ga mata da ‘yan mata. Hakan zai dauki lokaci. Amma zai faru.''
Paranda sunan alkalami ne – yana nufin tsuntsu. Mata kamar ta, musamman ma mata masu ilimi a garuruwa, sun ki aminta a takaita musu yin abubuwa.
Da yawa sun gudu. Mutane da yawa har yanzu suna da fata mai kyau.
Wasu mutane kalilan sun yi zanga-zanga daga lokaci zuwa lokaci. Ko da a wasu sassa na ƙasar, na gamu da mata wadanda basu yi karatu ba, na zaune cikin gidajensu da rayuwar kunci da Taliban ta saka musu.
Ƙarfin alkalaminta

"Rubuta! Me ya sa kuke jin tsoro? Tsoron wa kuke ji? …Watakila rubuntunku zai iya faranta rajn wani…Alkalamin ku ya zama goyon bayan hannayen wani da ya karye da kawo fata ga wasu mutane kalilan,’’ in ji Sadaf.
Rayuwar marubuci a ko’ina tana iya gamuwa da shakka da tsoro. Ga matan Afghanistan, yana da muhimmanci a samu mai aminci wajen rubutu don kirkirar ma’ana da manufa.
''Ɗaya daga cikin daliban ta gabatar da littafin a cikin kyawawan kalmomi, kuma mafi kyawun sashi shi ne lokacin da ta ambaci sunana. Dukkan dalibai sun yi min murna. Na rubuta wannan a matsayin mafi kyawun abin tunawa a rayuwata.’’
Mai daukar ɗawainiyar gida

"Ina fadawa kai na cewa kada na damu da batun kudi saboda Allah zai kawo mani wata hanya ta daban. Mu goma ne cikin iyalan mu, kuma ni ke daukar dawainiyar mu.''
Ban samu kudin kirki ba a lokutan baya, kuma har yanzu labarin bai sauya ba.
Fata mai kyau

"Zuciyata cike take da raɗaɗi...akwai wani abu da yake fada mani cewa in tashi in yi yaƙi. Ina fatan abubuwa za su sauya daga baki zuwa fari nan da ƙanƙanin lokaci.’’
''Yan Afghanistan suna yawan cewa fata shi ne abu na karshe da suke hankoro kafin mutuwa. A cikin ‘yan shekarun nan, kafin ‘yan Taliban su karbi ragamar mulkin ƙasar, lokacin da tashe-tashen hankali na yau da kullum suka tsananta, wasu sun ce fatan da suke da shi ya mutu.
Amma mutanen da suka rayu, har yanzu suna cike da begen samun sauki a rayuwa.



























