Man City za ta dauki Sergio Gomez daga Anderlecht

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Manchester City na tattaunawa da Anderlecht ko za a sayar mata da mai tsaron bayan tawagar Sifaniya ta matasa 'yan kasa da shekara 21, Sergio Gomez.
City na neman mai tsaron baya daga gefen hagu, bayan da Brighton ba ta sayar mata da Marc Cucurella, wanda Chelsea ta dauka a makon jiya kan fam miliyan 62.5.
Watakila City ta fara amfani da Gomez, mai shekara 21 nan take, ko kuma Pep Guardiola ya bayar da aronsa ga Girona ta Sifaniya.
Ya koyi tamaula a makarantar matasa ta Barcelona daga nan ya koma taka leda a Borussia Dortmund.
Gomez ya yi wasannin aro kaka biyu a Huesca a 2019, daga Anderlecht ta dauke shi karkashin koci Vincent Kompany, tsohon kyaftin din Manchester City.






















