Bayern Munich ta kammala ɗaukar Olise daga Crystal Palace

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta kammala ɗaukar Michael Olise daga Crystal Palace kan yarjejeniyar kaka biyar, bayan da ta biya kunshin kwantiraginsa £60m.
Mai shekara 22, wanda aka haifa a Ingila, amma ya buga wa tawagar matasan Faransa ƴan kasa da shekara 21, ya yi wa Palace karawa 90 a dukkan fafatawa.
Ya koma Palace da taka leda daga Reading kan £8m a Yulin 2021.
Chelsea da Newcastle United sun yi kokarin taya ɗan wasan a kakar nan, wanda ya zaɓi ya koma taka leda a Bayern karkashin Vincent Kompany.
Olise ya ci ƙwallo 10 a karawa 19 a Premier League da ta wuce, inda Palace ta kare a mataki na 10 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
Ɗan wasan yana cikin wadanda za su wakilci Faransa a tamaula da za a yi a Olympics a birnin Paris a bana.
Haka kuma Bayern na daf da sayen ɗan wasan Fulham, Joao Palhinha kan £42m har da ƙudin tsarabe-tsarabe.
Kaɗan ya rage mai shekara 28 ɗan kasar Portugal ya koma Bayern Munich a bara, daga baya cinikin ya wargaje.
Haka kuma ƙungiyar da ke buga Bundesliga ta ɗauki Eric Dier na Tottenham, wanda ya buga mata wasannin aro tun daga Janairu.
A kakar da ta wuce Bayern Leverkusen ta kawo karshen kaka 11 da Bayern ta yi tana lashe Bundesliga.
.



























