Harry Kane ya ji rauni a idon sawu

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Kyaftin din Ingila, Harry Kane ba zai buga wasan sada zumunci tsakanin kasarsa da Belgium ba saboda rauni a idon sawunsa.
Dan kwallon ya koma kungiyarsa ta Bayern Munich da ke Jamus.
Kane mai shekaru 30, shi ne yafi kowanne dan kwallon Ingila zura kwallo a tarihin tawagar kasar kuma bai buga wasan sada zumunci tsakaninsu da Brazil ba.
An buga wasan a ranar Asabar inda Brazil ta doke Ingila da ci daya me ban haushi a filin Wembley.
"Harry Kane ba zai buga wasanmu na ranar Talata," in ji kocinsa Gareth Southgate.
Shi ma dan wasan baya Kyle Walker ya ji rauni.






















