Olympiakos ta zama ƙungiyar Girka ta farko da ta lashe gasar zakarun Turai

Asalin hoton, Getty Images
Ayoub El Kaabi ne ya ci wa Olympiakos ƙwallo minti huɗu da take wasan ƙarshen da ta doke Fiorentina a gasar zakarun Turai ta Europa League.
Nasarar ta sa ƙungiyar ta zama kulob ɗin Girka na farko da ya jinjina kofin zakarun na Turai.
Ɗan wasan gaban na Moroko ya jefa ƙwallon a raga da ka bayan Santiago Hezze ya koro ƙwallo, abin da ya sa 'yan kallo suka ɓarke da sowa a filin wasa na AEK Arena da ke birnin Athens.
Sai dai an ɗauki tsawon lokaci na'urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa na duba ƙwallon ta El Kaabi, wadda ita ce ta 11 da ya ci a gasar.
Wannan ne karo na biyu da Fiorentina ke samun kanta cikin takaici bayan ƙungiyar ta Italiya ta yi rashin nasara a hannun West Ham a wasan ƙarshe na kakar da ta gabata, inda Bowen ya ci ƙwallo a mintunan ƙarshe.
Haka nan, wannan ne karo na biyu da wata ƙungiyar Girka ta je wasan ƙarshe a zakarun Turai, yayi da Fiorentina ta buga wasan ƙarshen a karo na shida.























