An kara dakatar da Tonali wata biyu kan karya dokar yin caca

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da dan wasan Newcastle United, Sandro Tonali wata biyu, sakamakon karya dokar yin caca.
Dan kasar Italiya, mai shekara 23, ba zai yi hukuncin ba, idan bai kara aikata laifin karya dokar yin caca ba.
A yanzu haka yana hukuncin dakatarwar wata 10 da aka yanke masa cikin Oktoban 2023, bayan da ya aikata laifin a Italiya, lokacin yana taka leda a AC Milan.
Cikin watan Maris hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi dan wasan da cewar ya yi caca 40 zuwa 50 bayan da ya koma Newcastle daga AC Milan a watan Yuli, ciki har da yi a kan sakamakon wasannin kungiyar St James Park.
FA ta ce kudin da dan wasan tawagar Italiya ya zuba a cacar ya kai £85,600, wanda aka dakatar aka kuma ci tarar £20,000.
Cacar da Tonali ya yi a kan Newcastle ya zabi da kungiyarsa ce za ta ci wasan.
FA ta ce ya kuma buga karawa uku daga cikin hudun da ya yi cacar.























