Luguden wutar Isra'ila ya kashe mutum fiye da 900 a Gaza

Asalin hoton, Getty Images
Isra’ila ta ci gaba da luguden wuta kan Gaza cikin dare, inda dakarunta suka ce sun kai farmaki kan wurare fiye da 200.
Rahotanni sun ce ɗaya daga cikin hare-haren ya faɗa gidan mahaifin wani kwamandan mayakan Hamas, Mohammed Deif, kuma ya kashe ƴan uwanshi da dama.
Hukumomin Palasɗinu sun ce an kashe mutane fiye da 900 kawo yanzu.
Hamas ta ci gaba da ƙoƙarin harba makaman roka zuwa Isra’ila, inda take harin birnin Ashketon.
A ɓangare guda kuma, wata musayar wutar na gudana a kan iyakar Isra’ila da Lebanon, kuma dakarun Isra’ila sun ce an harba bama-bamai daga Syria zuwa yankin da Yahudawa suka mamaye.
Cikin wata wasiƙa da ya aikewa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, jakadan Palasɗinu a majalisar, Riyad Mansour ya zargi Isra’’ila da jefa jama’ar Palasɗinu cikin yunwa, duk a cikin dabarun ta na yaƙi.
Ya ce luguden bama-maban da Isra’ilan ke yi ƙololuwar laifin yaƙi ne.
A halin yanzu dai ƙasashen larabawa da dama sun ɗauki matakin ƙara yawan tallafin da suke bai wa Palasɗinu yayin da lamari ke ƙara rincaɓewa a Gaza.
Shugaba Mohammed bin Zayed na haɗaɗɗiyar daular larabawa ya bayar da umarnin bayar da tallafin Dala miliyan 20 cikin gaggawa ga Palasɗinun, yayin da Kuwait ma ta ƙara yawan tallafin da take bayar wa.
Sarki Abdullah na Jordan ma ya bayar da umarnin kai tallafin gaggawa da ya shafi kayan kiwin lafiya da sauran buƙatu.
Hozayfa al Yazji wani jami’i ne da ke aikin jin-ƙai a Gaza kuma ya shaida wa BBC cewa mutanen da ke Gazar sun riga sun cire tsammanin rayuwa.
"Abin da kawai zan iya cewa shi ne ana zartar da hukunci ne na bai-ɗaya. Bana goyon bayan kai hari kan fararen hula daga kowanne ɓangare. Wannan lugude kan Gaza fararen hula kawai yake kashewa da kuma tarwatsawa duk wani abu da ke wajen. Mutane na zaune cikin matsanancin tsoro kuma basu san abin yi ba" in ji shi.
Sai dai kuma mai ba wa firaiministan Isra’ila shawara, Mark Regev, ya ce dole ne Isra’ila ta ɗauki wannan mataki na martani don tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.



























