Napoli na son Rashford, Isak zai koma Barca, Walker na iya komawa AC Milan

Asalin hoton, Getty Images
Napoli na shirin siyan dan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford, PSG na dab da daukar dan wasan gefe na Napoli Khvicha Kvaratskhelia sai kuma Barcelona na zawarcin dan wasan Newcastle United Alexander Isak.
Ana sa ran Napoli za ta fara zawarcin dan wasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, yayin da ake sa ran dan wasanta na gaba ɗan Georgia Khvicha Kvaratskhelia zai bar kulob din na Italiya. (Mirror)
Sai dai tuni Paris St-Germain na gab da siyan Kvaratskhelia din, mai shekaru 23 da haihuwa tuni ya cimma yarjejeniya da kungiyar ta Faransa. (Foot Mercato)
PSG ta yi imanin cewa za ta iya shawo kan Aston Villa ta sayar mata da dan wasan gaban Colombia Jhon Duran, mai shekara 21, kuma kulob din Ligue 1 na son sanya dan wasan gaban Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26, a duk wata tattaunawa. (Mail)
Barcelona na zawarcin dan wasan gaban Newcastle United Alexander Isak kuma za su iya zawarcin dan wasan mai shekaru 25 a watan Janairu ko kuma a bazara, ya danganta da yanayin kudinsu. (Mundo Deportivo )
AC Milan na sha'awar sayen dan wasan bayan Ingila Kyle Walker, kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce dan wasan mai shekaru 34 ya nemi barin kulob din na Ingila, kuma an amince masa. (Guardian)
Fatan Chelsea na sayen dan wasan baya na Ingila Marc Guehi mai shekaru 24 daga Crystal Palace na iya zuwa karshe, saboda tsauraran tsarin albashin kulob din na Stamford Bridge. (Mirror)
Daraktan wasanni na Eintracht Frankfurt Markus Krosche ya tabbatar da cewa wata kungiya ta tuntube su game da daukar dan wasan gaban Masar Omar Marmoush, inda Manchester City ta amince da yarjejeniya da dan wasan mai shekaru 25. (Sky Sports Germany)
Barcelona ta ki amincewa da tayin da Juventus ta yi mata na sayen dan wasan bayan Uruguay Ronald Araujo, kuma tana son ci gaba da rike dan wasan mai shekara 25, wanda kwantiraginsa da kulob din na Spain zai kare a shekarar 2026. (Mundo Deportivo)
Borussia Dortmund na tunanin zawarcin dan wasan tsakiyar Ingila Carney Chukwuemeka, mai shekara 21, a matsayin aro daga Chelsea. (Sky Sports Germany)



























