Man Utd da Arsenal na son Guehi, Liverpool na samun tayi kan Salah daga Saudiyya

Guehi
An wallafa

Crystal Palace na fargabar ɗan wasanta na Ingila mai shekara 23, Marc Guehi na iya barin ƙungiyar a kan fam miliyan 55. Tuni dai ƙungiyoyi irinsu Manchester United da Arsenal suka shiga zawarci. (Times - subscription required)

Ɗan wasan Najeriya mai shekara 25, Victor Osimhen na iya barin Napoli a wannan kaka, inda ake tunanin ya je Chelsea ko PSG. (Gazzetta - in Italian)

Borussia Dortmund za ta yi kokarin mayar da zaman aron Jadon Sancho daga Manchester United zuwa yarjejeniyar dindindin a wannan kaka. (Fabrizio Romano)

Liverpool ta shirya karban tayin kusan fam miliyan 150 da take samu daga ƙungiyoyin Saudiyya akan Mo Salah na Masar mai shekara 31. (Football Insider)

Ɗan wasan baya a Netherlands Lutsharel Geertruida, mai shekara 23, na iya barin Feyenoord tare da manajansa Arne Slot zuwa Liverpool. (Express)

Mai buga gaba a Poland Robert Lewandowski ɗan shekara 35 na son ya cigaba da zaman Barcelona a wannan kaka, duk da tayin da yake samu daga ƙungiyoyin Saudiyya. (Sport - in Spanish)

Arsenal da Liverpool da Manchester United na zawarcin ɗan wasan Brighton mai shekara 20 asalin Kamaru Carlos Baleba. (Caught Offside)

Leeds na son saye ɗan wasan Liverpool mai shekara 27 Nat Phillips, da ke zaman aro a Cardiff. (Mirror, via Yorkshire Post)

Thiago Silva na Brazil na son barin Chelsea a karshen kaka zuwa Fluminense. (TEAMtalk)

Wataƙil Everton ta sayar da ɗan wasanta mai shekara 21 Jarrad Branthwaite a kokarin kaucewa saɓa dokokin wasannin. Haka na iya bai wa ɗan wasan daman tafiya Manchester United. (Sun)

Arsenal ta shiga tattaunawa kan sabon kwantiragi da ɗan wasan Brazil mai shekara 26 Gabriel. (Fichajes - in Spanish)

Arsenal da Borussia Dortmund na farautar ɗan wasan Barcelona mai shekara 18 Brian Farinas. (Caught Offside)

Blackburn na son a biyata fam miliyan 20 kan ɗan wasanta na Ireland Sammie Szmodics, tana samun zawarci daga Brentford da Luton da Sheffield United. (Sun)