Rashin Messi ya jefa Inter Miami a tsaka mai wuya

Lionel messi
An wallafa

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke buga gasar MLS a Amurka ta samu koma baya a yunkurinta na taka rawar gani a kakar wasa ta bana, inda Chicago Fire ta doke ta da ci 4-1, wasan da Lionel Messi bai samu bugawa ba saboda rauni.

Tsohon dan wasan Liverpool, Xherdan Shaqiri ne ya zura kwallo biyu a ragar Miami sannan Maren Haile-Selassie shi ma ya jefa kwallaye biyu.

'Yan kallo 62,124 ne suka halarci wasan a filin wasan Soldier Field da ke Chicago inda suka yi fatan ganin kyaftin din Argentina Lionel Messi.

Amma dan wasan mai shekaru 36 ya buga wasa sau daya ne kacal a wasanni bakwai tun ranar 3 ga watan Satumba.

Messi, wanda ya kulla yarjejeniya da Miami a watan Yuli bayan kwantiraginsa da Paris St-Germain ta kare, ya kalli wasan karshe da Houston Dynamo ta doke sabuwar kungiyarsa da ci 2-1 a wasan karshe na gasar cin kofin US Open a makon da ya gabata.

Inter Miami ita ce ta 14 a gasar MLS da ta kunshi kungiyoyi 15 kuma tana bukatar lashe dukkan wasanninta guda uku na gaba kafin ta iya tsallakawa zuwa mataki na gaba.