Premier League: West Ham ta rike wuta a na hudu bayan ta tashi 2-2 a gidan Leicester

West Ham
An wallafa

West Ham ta cigaba da zama a na hudu da maki 41 a teburin Premier, bayan da ta tashi 2-2 a gidan Leicester City.

Bakin ne suka fara saka kwallo raga ta hannun Jared Bowen, kafin mai masaukin bakin ta farke ta hannun Youri Teilemans dab da aje hutun rabin lokaci.

To amma Leicester ta shiga gaba ta hannun mai tsaron bayanta Ricardo Pereira, kafin West Ham ta farke a minti na 90 ta hannun mai tsaron bayanta Craig Dawson.

Hakan na nufin West Ham na ci gaba da dagewa wurin ganin ta samu gurbi a gasar zakarun turai, don yanzu ta hada maki 41 a wasanni 25.

Manchester United ce ke binta a na biyar da maki 40 a cikin wasanni 24 da kwanton wasa daya.

Ita kuwa Leicester na zaune ne na 11 da maki 27 cikin wasanni 22.

West Ham

West Ham ta buga wasan ba tare da mai tsaron bayanta ba wato Kurt Zouma, wanda ake cece-kuce kan sa saboda fama da rashin lafiya yayin atisaye.

A makon da ya wuce ne wani hoton bidiyo ya nuna dan kasar Faransar yana dukan magensa, wanda hakan ya yi sanadin cin shi tarar fam 250,000, kuma wasu kamfanoni suka yanke hulda da shi.

Shine wasan karshe a gasar Premier da aka buga ranar Lahadi da yamma, to amma kafin shi Liverpool da Newcastle ma sun ci wasannin su, yayin da Tottenham tasha kashi har gida a hannun Wolves.

A mako mai zuwa West Ham za ta karbi bakuncin Newcastle, yayin da Leicester za ta nika gari zuwa Wolverhampton.