'Yan gwagwarmaya da 'yan hamayya a Zimbabwe sun fara buya

Shugaba Emmerson Mnangagwa
Bayanan hoto, Shugaba Emmerson Mnangagwa
An wallafa

Kungiyoyin kare hakkin dan adam a Zimbabwe sun ce 'yan sanda da soji, na ci gaba da kama gwamman magoya bayan 'yan adawa da masu gwagwarmaya a wani yunkuri na dakile sukar gwamnati.

Wata kungiyar lauyoyi masu rajin kare hakkin adam ta kasar ta ce kusan mutum sittin aka daure zuwa yanzu, yayin da jami'iyyar hamayya ta MDC ke cewa yawanci mutanenta ne.

An bayar da rahoton cewa 'yan gwagwarmaya da dama sun buya, saboda fargabar gwamnati za ta iya kama su.

Su ma kasashen duniya na ci gaba da nuna damuwa a kan rahotannin take hakkin dan adam da ke karuwa a kasar.

Fiye da fitattun marubuta dari na nahiyar Afrika ne suka rattaba hannu kan wani korafi da ke neman a dakatar da kasar daga kungiyar hadin kan Afrika saboda abubuwan da ke faruwa.

Yadda zanga-zanga ta barke a kasar

Fiye da mutane dubu dari da biyar aka kama daga watan Maris zuwa yanzu
Bayanan hoto, Fiye da mutane dubu dari da biyar aka kama daga watan Maris zuwa yanzu

Fiye da mutane dubu dari da biyar aka kama daga watan Maris zuwa yanzu, saboda saba dokokin da aka kafa na hana yaduwar cutar korona wajen shirya zanga-zanga.

Daga kwana biyu da suka wuce zuwa yanzu kuwa an kama akalla mutum 1000, ko dai saboda dalilin shirya tarukan ba bu gaira ba bu sabab, ko kuma saboda rashin sanya takunkumi.

Masu suka na zargin gwamnati da fakewa da dokokin kullen korona wajen huce takaicinta a kan yan hamayyar da suka zame mata kadangaren bakin tulu, da kuma yan gwagwarmayar da ke sukar yadda ake tafiyar da harkokin mulki.

Ranar 31 ga watan jiya, an shirya wata gagarumar zanga-zanga don neman shugaba Mnangagwa ya yi murabus, bukatar da ba ta kai ga gaci ba.

Harkokin tattalin arziki sun kara tabarbarewa bayan hawan shugaba Mnangagwa mulki
Bayanan hoto, Harkokin tattalin arziki sun kara tabarbarewa bayan hawan shugaba Mnangagwa mulki

Tun bayan hawan shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa ake samun karuwar take hakkin dan adam a Zimbabwe, daya daga cikin matsalolin da aka yi fatan zuwansa zai kawar.

Mista Mnangagwa ya zama shugaban kasa ne bayan da aka hambarar da gwamnatin Robert Mugabe wanda ya mulki kasar har na tsawon shekara 37.

Sai dai al'amura sun kara tabarbarewa tun bayan zuwansa, kama daga batun rashin aiki a tsakanin 'yan kasa, durkushewar tattalin arziki da karuwar talauci

Wasu bayanai sun nuna cewa da yawa daga cikin matasan kasar kan fice don zuwa cirani wasu kasashen duniya saboda rashin kyakkyawan yanayin neman na kai a kasar.