Liverpool na iya zama Manchester a shekarun baya - Jermaine Jenas

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Liverpool za ta iya mamaye kwallon kafar Turai kamar yadda Manchester United ta yi a shekarun 1990 da kuma shekarun 2000, in ji tsohon dan wasan Ingila Jermaine Jenas.
Liverpool din dai a yanzu ita ce a gaba a Gasar Firimiya kuma za ta kara a ranar Lahadi da Manchester United da misalin 16:30 agogon GMT.
Liverpool wadda Jurgen Klopp ke jagoranta na gaba da Manchester United da maki 27.
Manchester United da Ole Gunnar Solskjaer ke jagoranta ita ce ta biyar a gasar.
A wata hira da gidan rediyon BBC Radio 5 Live, Jenas ya shaida cewa akwai tazara matuka tsakanin kungiyoyin biyu ta fannin maki.
Ya ce ''Klopp na da wani abu daya dangane da horar da 'yan wasa da Ole ke koya''.
United ta lashe Gasar Firimiya sau 13 a kakar wasanni 21 karkashin jagorancin Sir Alex Ferguson - wanda ya yi ritaya a 2013.
Kungiyar ta lashe gasar a jere tsakanin 1999 zuwa 2001 sai kuma tsakanin 2007 zuwa 2009.
Tsohon dan wasan gaba na kungiyar Solskjaer ya gaji Jose Mourinho, wanda tun a farko ya jagoranci kungiyar ne na wucin gadi.


























