Ba zan hana Arteta komawa gida ba - Guardiola

Guardiola da Arteta
An wallafa

Pep Guardiola ya ce yana sa ran Mikel Arteta zai yanke hukunci cikin hanzari kan ko zai zama kocin Arsenal kuma ba zai yi gardama da tsohon dan wasan Gunners din ba kan batun karbar aikin.

Manchester City na tsammanin ganin Arteta a filin wasan da za ta buga da Oxford, a wasan kusa da daf da na karshe na kofin Carabao.

Mataimakin kocin City ya tattauna da wasu manyan shugabanin kungiyar ta Arsenal kan batun maye gurbin tsohon kocin da ta raba gari da shi Unai Emery.

"Ina ganin ya kamata ya yanke hukuncin cikin gaggawa," a cewar Guardiola.

"Me zai hana shi ta fiya? wannan abu ne mai kyau."

Arteta mai shekaru 37, ya je filin atisayen Manchester City ranar Talata, bayan tattauana da yayi da wakilan Gunners din har sau biyu.