Manchester City ta lashe Community Shield

An wallafa

Manchester City za ta fara kakar tamaula ta bana da kafar dama bayan da ta lashe Community Shield ranar Lahadi a Wembley.

City ta yi nasarar doke Liverpool a bugun fenarity da ci 5-4, bayan da suka tashi wasan kunnen doki 1-1.

Man City ce ta fara cin kwallo ta hannun Raheem Sterling minti 12 da fara tamaula, daga baya Liverpool ta farke saura minti 12 a tashi daga karawar ta hannun Joel Matip.

Bayan kammala Community Shield na nufin karshen makon nan za a fara gasar cin kofin Premier na bana, wanda Manchester City ta lashe na bara.

Haka kuma City din ita ce ta yi nasarar daukar kofin FA da na League Cup a kakar da aka kammala.

Jadawalin wasan farko a gasar Premier

Juma'a 9 ga watan Agusta

  • Liverpool da Norwich City

Asabar 10 ga watan Agusta

  • West Ham United da Manchester City
  • Watford da Brighton & Hove Albion
  • Burnley da Southampton
  • Crystal Palace da Everton
  • Bournemouth da Sheffield United
  • Tottenham da Aston Villa

Lahadi 11 ga watan Agusta

  • Newcastle United da Arsenal
  • Leicester City da Wolverhampton Wanderers
  • Manchester United da Chelsea

Karin wasu bayanai

  • Manchester City ta lashe Community Shield na shida a tarihi kuma ta farko da ta dauka biyu a jere, tun bayan bajintar da Arsenal ta yi a Agustan 2015.
  • Haka kuma City ita c e ta farko da ta lashe Community Shield, bayan cin kofin Premier dana FA, tun bayan Arsenal da ta yi hakan a Agustan 2002, inda ta ci Liverpool 1-0.
  • Idan ka hada da bugun fenarity, Manchester United da Chelsea ne aka fi doke wa a karawar karshe kowacce sau tara-tara a Community Shield, sai Liverpool mai bakwai iri daya da Arsenal.
  • Kwallon da Raheem Sterling ya ci Liverpool ranar Lahadi, ita ce ta farko da ya zura wa tsohuwar kungiyarsa a karawa 11 da ya yi da ita a kowacce fafatawa.