Me ya sa Trump da Sadiq Khan ba sa ga maciji da juna?

Shugaba Donald Trump na Amurka na wata ziyarar aiki a Burtaniya inda Sarauniya Elithabeth ta gayyace.
Mista Trump ya kai irin wannan ziyara a watan Yulin 2018 ta farko a tun bayan da ya zama shugaban kasar Amurka.
Tuni dai shugaba Trump da mai dakinsa, Melania Trump suka gana da sarauniya a fadarta ta Buckingham Palace.
Bakin sarauniyar sun sanya furen ban girma a kaburran mazanjiya da ke Westminster Abbey.
A shekarar 2011, Sarauniya Elizabeth ta karbi bakuncin tsohon shugaban Amurkar, Barack Obama a Fadar Buckingham.
Mene ne tsakanin Trump da Sadiq Khan?

'Yan mintina kadan kafin saukarsa a Burtaniya, Donald Trump ya caccaki magajin garin London wanda suka saba yin cece-kuce da shi a baya.
A shafinsa na twitter, Mista Trump ya bayyana Sadiq Khan wanda tun fari ya ce "ka da a tarbi" mista Trump da 'wanda ya rasa makama'.
Ko a lokacin ziyarar shugaba Trump ta watan Yulin 2018 an samu irin wannan tankiya tsakanin mutanen biyu.
A lokacin ne mista Trump ya yi kakkausar suka ga kasancewar Sadiq Khan magajin garin birnin na London, inda ya ce an samu karin hare-haren ta'addanci da aikata manyan laifuka da kuma kwararar bakin haure.
To sai dai Magajin Garin Landan din Sadiq Khan ya ce ba shi da lokacin tankawa Shugaban Amurka Donald Trump game kalaman da ya danganta shi da su.
Ana dai ganin rashin jituwa tsakanin mutanen biyun ta samo asali ne kan zanga-zangar nuna kin jini da aka yi wa mista Trump a birnin London lokacin da ya yi wancan zuwa.
Sadiq Khan ya kwarara wa masu zanga-zangar gwiwa cewa suna da 'yancin yin zanga-zanga, al'amarin da ya fusata shugaba Trump.
Zanga-zangar kin Trump a Burtaniya

Masu zanga-zanga na shirin gudanar da zanga-zanga a ranar Talata a wasu manyan biranen Burtaniya da suka hada da London da Manchester da Belfast da Birmingham da manufar kin jinin shugaba Trump.
Masu zanga-zanagar dai na nuna wa Mista Trump yatsa kan rashin girmama mata da kananan yara da masu cirani da kuma irin kalamansa da suke ganin na rarraba kan jama'a ne musamman karfafa wa masu akidar wariyar launin fata.
Ko a ziyarar da mista Trump ya kai Burtaniya a 2018, dandazon masu zanga-zanga ya toshe manyan titunan London inda aka yi ta daga kwalayen da ke dauke da rubutun rashin amincewa da Donald Trump.
Cincinrindon masu zanga-zangar ne ma ya sa Shugaba Trump bai iya zuwa wasu wurare ba da tun farko aka tsara zai je.
Wani abun mamaki ma shi ne yadda masu zanga-zangar suka yi mutum-mutumin Donald Trump na leda inda suka sake shi a sama.
To sai dai a wannan karon, masu kaunar Shugaba Trump din sun ce su ma za su shirya zanga-zangar nuna goyon baya.


























