An kori direban Bus a Indiya saboda Biri

An kori wani direban motar Bus a Indiya, saboda barin wani Biri ya tuka motarsa.
Sama da fasinjoji 30 da ke cikin motar ne suka yi korafi kan abin da direban ya yi.
Kungiyar direbobin mota ta kudancin jihar Karnataka sun dauki mataki, jim kadan bayan bayyanar wani bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta da ya nuna Birin na tuka motar cikin kwanciyar hankali.
Mai magana da yawun hukumar ya ce an dauki matakin dakatar da direban ne saboda ba za a amince da sanya rayuwar fasinjoji cikin hadari ba.
Sai dai abin mamaki shi ne bidiyon birin da ke tuka motar, ya bai wa ma'abota shafukan sada zumunta sha'awa.
Wani mai suna Parag Heda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "wannan abin sha'awa ne, me ya sa aka kori direban daga aiki? Kamata a yi ma sa gargadi don kada ya sake aikata hakan."
Ganau kan lamarin sun ce Birin ya shiga motar ne lokaci daya da wani fasinja, inda ya ki zama a ko ina sai kujerar gaba ya kuma yi zuruf ya dare kan cinyar direban shi kuma ya bar shi ya rike sitiyari da hannu daya kamar yadda hoto da bidiyon suka nuna.
Rahotanni sun bayyana cewa ana cikin tafiya Birin ya sauka watakila ya zo inda ya bar direban ya ci gaba da tukin shi.

























