Koriya ta Kudu za ta koma taimaka wa Koriya ta Arewa

An wallafa

A karon farko cikin shekara biyu, Koriya ta Kudu ta yanke shawarar koma wa domin ayyukan jin kai a makwabciyarta Koriya ta Arewa, wadda suke zaman doya da manja.

Ma'aikatar hadin kan kashashen biyu a Seoul ta ce, za ta samar da dala miliyan takwas domin bayar da gudunmuwa ga shirye-shiryen taimaka wa yara da mata masu juna biyu da kuma samar da magunguna na Majalisar Dinkin Duniya.

Babu bayanin lokacin da Koriya ta Kudun za ta bayar da tallafin.

Tun daga shekarar 2015, Koriya ta Kudu ba ta kara ba wa Koriya ta Arewa wani tallafi na ayyuykan jin kai ba, saboda gwajin makamin nukiliyar da makwabciyar tata take yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, mafi yawan al'ummar Koriya ta Arewa, sun dogara ne a kan tallafin abinci.